Forty three

1.7K 186 17
                                    

Tana zaune shiru a d'aki ta zuba uban tagumi, kana ganinta kasan akwai damuwa a tare da ita, tafi awa d'aya a haka tun bayan tashin ta sallar asuba, dukda jiya bata samu bacci ba, sai faman juye juyen da ta dunk'a yi akan gado tana tuninnika kala kala, sai dab da asuba bacci b'arawo yayi awon gaba da ita.

D'aga ido tayi ta maida kan agogon dake manne a bangon d'akin taga k'arfe bakwai ta d'an gota, wata ajiyar zuciyar ta k'ara tare ta k'ara fad'awa cikin duniyar tunanin ta.

Ba abunda take tunani tun zuwan ta gidan sai kamal, wana yanayin yake ciki, dan halin da ta barshi ya bala'in d'aga mata hankali, ya zaiyi ya ceci kanshi daga cikin wannan masifar dake bibiye dashi, dukda tasan yana da laifi abunda ya mata amma tana mutuk'ar tausaya mishi.

Ko mami da ta ga sun shigo da ita da abba jiya sai da fuskar ta ta zamana d'auke da alamar tambaya dukda dai bata furta ba a baki, sai dai, ta tambaye ina kamal da ta gansu su kad'ai amma sakeena sam sam ta kasa bata amsa, abba ne yayi saurin cecan ta yace zai mata bayani daga baya, ita dai bata san ya ta kaya ba tunda tun da aka sauke ta a guestroom bata k'ara fitowa ba daga d'akin, sai dai masu aiki su shigo yi mata hidima ko kausar tazo mata hira.

Tana haka taji anyi knocking tare da turo k'ofar, a hanakali ta maida hankalin ta kan wurin taga kausar na tsaye na mata murmushi, saurin kauda damuwar ta gefe tayi, ita ma murmushin ta saki sai a sannan ta mik'e daga kan sallayar ta fara ninkewa.

Kausar ma k'arasowa cikin d'akin tayi, d'ayan hannunta na jan wani d'an k'aramin akwati.

"Aah sai ina kuma da sassafen nan?"

Sakeena ta tambaye ta yarda ta ganta a shirye, cikin wani palazo, shirt da turban, da y'ar kwaliya a fuskar ta, yarinya tayi kyau.

"Wallahi makaranata, ina da lectures 8, nama makara"

"Nafa manta, ashe kanwar tamu an shiga jami'a"

Kausar murmushi tayi mata, tare da cewa,

"Har mun shiga 200 level ma, nan da shekaru kad'an zamu gama"

Sakeena dariya tayi nan dai ta d'an cigaba da jan kausar da hira tana tsokanar ta, sai da kausar taga zata makarar da ita da gaske tayi sauri mik'a mata akwatin da ta shigo dashi.

"Ga kaya nan mami tace in kawo miki, saboda zaki buk'ace su, ni dai bari nayi sauri na tafi kinga har 7:30 tayi"

Tana maganar tana duba Iwatch d'in dake sak'ale a hannunta.

"To shikenan a gaishe da mutun makaranta, ayi karatu da kyau dan Allah kada ayi wasa"

Dariya ta k'ara saki tace mata tom shikenan, samnan ta fita da sauri.

Tana jawo mata k'ofar sakeena ta k'ara wata ajiyar zuciya, a take damuwar ta ta k'ara bugan ta, daman duk yak'e ne hirar da tayi da kausar, komawa tayi ta zauna a jikin gado tayi shiru, tare da k'ara fad'awa cikin kogin tunanin ta.

Ba wanda ya kaita san araba auran ta da kamal duk duniya, ba abunda ta tsana a rayuwar ta irin zama dashi, amma kwana biyu ta lura ta nemi tsanar da tayi mishi ta rasa, yanzu kwata kwata ko kad'an bata jin hausin shi da k'inshi a ranta, wani abu a k'asan ranta na gaya mata kamal ya canza, ba wanda ta sani da bane, watak'ila shi ya saka duk ta daina jin abunda take ji game dashi.

Mik'ewa tayi ta jawo akwatin da taga in ta zauna ta biye wa tunanin ta sai ta kai azahar a haka, tana bud'e akwatin ta ganshi cike da kayan sawa, da underwears ta dai duka abunda zata buk'ata, murmushi tayi tare da yi ma mami godiya a k'asan ranta, sannan ta fara fitowa da abunda zata saka tana ganawa ta fad'a band'aki dan yin wanka.

Sai ta da shirya tsab cikin wata maroon abaya da mayafi ta feshi jikinta da turare sannan ta fiti daga d'akin, parlor ta fara yi tare da yin sallama, mami na tsaye a dining area, abinci take jerawa amma ta tsaya da abunda take yayin da ta k'ura ba window dake wurin ido, kana gani kasan tunani take me zurfi, ko shigowar sakeena bata ji ba balle sallamar ta.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now