Twenty

1.6K 132 5
                                    

Wani irin azababban fistari ne ya matse ta, ta rasa inda zata saka kanta, ga ba daman tsugunnawa tayi a compund d'in gidan, ba irin doorbell d'in da bata danna ba da buga k'ofa amma yak'i bud'ewa, wani irin zagi ta aikawa kamal a k'asan ranta, d'an rainin hankali da gangan zai iya ji yak'i bud'e mata, k'ara buga k'ofar tayi da duk k'arfinta dan sauran k'iris ta saki a wando, Allah ubangiji ya raba ta da abun kunya in tayi fitsari a jikinta ya zatayi, kunya sai ta kashe ta, haka ta ci gaba da rawa a tsaye har kusan minti talatin, itama da shegen taurin kanta, me ya hana ta shiga gidan tun jiya da daddare gashi yanzu har rana ta gama fitowa, ga ana ta kiran sallar azahar, Allah ya taimake ta akwai famfo a waje ta samu tayi sallar asuba, marar tace ta k'ara wani ruk'e wa, bata san lokacin ta tace

"Wayyo Allah na, kamal ka taimaka mun ka bud'e"

Tare da lumshe idanunta ta k'ara matse kafafunta, da danna doorbell, tana ji idanun mai gadin gidan akanta, amma duk bata shi take ba yanzu, har ta gama k'addarawa yau zatayi fitsari a wando kamar daga sama taji an bud'e k'ofar, ai sakeena bata tsaya bi takan shi ba tayi cikin gidan a guje sai d'akin ta, cillar da hijabin ta tayi a k'asan bedrrom d'inta tare da fad'awa band'aki, sai ta ta gama abunda zatayi tsab ta tabbata hankalin ta ya dawo jikinta sannan ta fito, tana fitowa ta tsince shi ya jingina a k'ofar d'akinta, hannun shi a cikin aljihun wandon shi, fuskar shi a had'e tamau yarda dai kullum take, wata muguwar harara ta jefa mishi, tare da yin sauri da k'arasawa wurin hijab d'inta dan a yanayin da dake, rigar jikinta kusan sharara ce ga kanta ba d'ankwali, tana sa hijab d'in tayi hanyar waje, shi kuwa kamal har lokacin bai bar kallon ta, manyan idanunshi kaf a kanta, gabanta fad'uwa ya fara yi, a haka ta samu ta dake,

"Ji yarda yake kallo na kamar wani maye"

Ta fad'i a zuciya, yayin da a zahiri bayan ta fito daga d'akin ta fad'i,

"zan bar maka gidan ka"

Ko kallanshi bata yi ba da tayi maganar, ga yarda tayi maganar a hankali kamar ba laka a jikinta, har tayi rabun tafiyar muryar shi ta tsai da ita,

"Fita zanyi in har kika koma waje to zan tafi da key d'in yarda in uzurin ya k'ara kama ki sai kiyi a jikin ki ko kiyi a waje ko kuma ki shiga band'akin mai gadi kiyi"

Wata kunya ce ta k'ara rufeta, duk laifin shine ai da ya kama ya kulle k'ofa da duk haka bata faru da ita ba, sai data samu ta had'e fuska yarda bazai raina mata wayo ba sannan a hankali ta juyo ta sauke idanunta akan shi, har lokacin yana jingine da k'ofar hannayen sa ma na cikin aljihun shi, fuskar shi kuwa d'auke da murmushin mugunta, wani irin haushin shi taji ya k'ara rufeta da tayi arba da fuskar shi, dan ba abunda ta tsana irin kamar da yake da kamil, wata harara ta k'ara sakar mishi, sannan ta fara takawa a hankali kamar ba kunya ce ta cika mata ciki ba ta wuce shi ta shiga d'akinta, tare da kullo k'ofar a hankali da saka mata key, ta jingina a jikin k'ofar, ba abunda kake ji sai k'arar bugawar da zuciyar ta take da kamshin turaren kamal da ya cika gidan gabaki d'aya,

Shiru tayi tana jiran k'arar k'ofar parlor alamun ya fita amma taji ko mosti bai yi ba, har kusan minti biyar,

"Ko dai ya tafi ne"

Ta tambayi kanta, dan tasan zata fi sakewa a gidan in har baya cikin shi, tayi duk abunda zatayi, a hankali ta murd'a key d'in ta bud'e k'ofar a hankali itama sannan ta lek'a dan taga yanan ko ya fitan amma idanunta sai cin karo sukayi da wannan manyan idanun nashi masu d'aukar hankalin y'an mata, har lokacin yana tsaye fuskarshi ta had'e ba alamun waso ko ko kad'an, da mugun sauri ta k'ara kulle k'ofar dayi mata key tare da fara maida numfashi,

"Ki cigaba da harara ta dan zan zubar da ruwan idanunki, kuma dama zaki daina wahalar da kanki na locking k'ofar dan ina da spare key zan shigo in ina son shigowa"

Jin murayar shi tayi a kunan ta taji gabanta ya fad'i, tsoron shine ya k'ara kamata barin ma yarda yayi maganar ba ta dauke da wasa, ba ayi minti d'aya ba taji k'arar k'ofar parlor alamun ya fita, wata irin ajiyar zuciya tayi tare da zubewa a k'asa, da ruk'e k'irjinta, wani mahaukacin tsoron shi ya gama rufe mata jiki, ta tsani zama dashi ta tsani ganinshi, yanzu haka zatayi ta fama har k'arshen rayuwar ta, anya bak'in ciki bazai kasheta ba, Allah ya raba kamal da shigo mata d'aki Allah kada ya tab'a sa wani abu ya had'a su, mik'ewa tayi da ta tuna bata yi sallar azahar ba, tare da shiga bathroom d'inta.

Bayan ta idar da salla tayi addu'ointa sosai, tana sanye cikin wata atamfa doguwar riga, d'inkin yayi mutukar kyau, kyan fuskarta ya k'ara fito, dirinta ma haka saboda ramewar da tayi duk da ta d'anyi duhu, taji cikinta yayi k'ara alamun yunwa take ji dan rabinta da abinci ta manta, taso ta share amma taga baza ta iya ba saboda yunwar taci k'arfin ta, wani katon hijab ta rarumo a cikin closet d'inta da take cike da kaya sannan ta saka, a hankali ta k'arasa jikin k'ofa ta saka kunnanta ko zataji mostin kamal, dan in har ya dawo sai dai yunwa ta kashe ta dan baza ta fita ba, da taji shiru ta bud'e tayi kitchen da sauri tana shiga shima tayi locking, store tayi direct tana bud'ewa taga abinci mak'il a ciki, harda kayan garar ta,

"Me yake ci"

Ta fad'a a hankali sai kace wani na kusa da ita sobada yarda taga ba abun da aka tab'a aciki, k'ara yin hanyar fridge tayi tana bud'ewa taga ba komi aciki sai ruwa,

"Haka yake zama da yunwa?, ko kuma a waje yake cin abinci"

Duk ta jera ma kanta tambayoyi, can kuwa tayi wa kanta wani rankwashi,

"Me ruwana ko yaci abinci ko bai ci ba, aiko mutuwa naga yana shirin yi sai dai na kalle shi na k'ara gaba dan ba ruwana da rayuwar shi"

Tana gama magana da kanta tayi store ta bud'e kwalin indomie ta d'auko guda uku, dan yarda take jin yunwa gani take kamar zata iya cinye kwalin, sai da ta dafa indomie d'inta lafiyyaya tasha sardine ta saka a plate ta zauna a k'asa ta narkin abinci ta, tana gamawa ta wanke plate d'in tare da gera kitchen d'in yarda bazai nuna alamar anyi girki ba ko an shigo, ta bud'e fridge ta d'auki ruwa sunkai bottle biyar sannanta fito, tana fitowa ta jawo k'ofar tare da maida numfashi, tanayin taku biyar wurin bedroom d'inta sai jin tayi karo da wani abu tana d'aga kai taga kamal a tsaye fuska a had'e, yana mata wani irin kallo, ai bata san lokacin da ta zaro manyan idanunta waje ba da sakin ruwan hannunta tare da ja baya da mugun sauri.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now