Twenty seven

1.4K 173 22
                                    

Ko da ya shigo parlor d'in baiga kowa ba, ba sakeena, ba kausar ba kamila, baisan me ya saka abun yayi mishi dad'i ba dan yau baya san had'uwa da matar shi, bedroom dinshi yayi, yana shiga ya fara cire kayan shi tare da fad'awa bathroom sai da yayi wankan shi sosai sannan ya fito, k'ugun shi d'aure da towel, yana fitowa yaji hayaniyar su a waje, gabanshi ne yayi wani irin fad'uwa, barin ma jin muryar sakeena da yayi, a hankali kamal yayi wurin closet d'inshi ya samu jallabiya ya zura bayan ya gama gera jikin shi da feshi shi da turare masu mugun k'amshi, sai da ya d'aure fuskar nan tashi tamau sannan ya fita daga d'akin.

Dukkan su na zaune tv a kunne, murmushin da ya gani a fuskar ta ne ya saka shi tsaywa cak, binta ya fara yi da kallo yana mamakin kamar ba ita bace jiya hawaye suka cika fuskar ta, yafi mintina yana kallanta, suma na parlor d'in basu san yana wurin ba, sai can kamar daga sama kamila ta juya ta ganshi,

"Lah ya kamal yaushe ka dawo?"

Maganar da tayi ce ta saka sakeena da kausar saurin kai idanunsu kanshi, suna had'a ido da ita tayi wani mugun had'e rai kamar bata tab'a dariya ba, sannan tayi saurin kwada idanunta, ya d'an yi sakwanni yana kallanta, sannan kuma ya maida hankalin shi kan kamila,

"Ban dad'e da shigowa ba"

Yana maganar yayi wurin su tare da d'an rankwashin kausar a kai yana jin ta fara mita, banza yayi da ita yayi wurin sakeena da take kan two seater idanunta nakan yatsun hannunta, tsugunnawa yayi a gaban ta a hankali, ya k'ura mata ido, sannan can ya kamo hannunta, yasan ta mishi kashaidin da ya daina tab'a ta ba da izinin ta ba, amma jikin shi ya gaya mishi baza ta tab'a tona mishi asiri ba duk abinda zaiyi mata, har lokacin bata d'ago ta kalle shi ba,

"Are you still angry?" A hankali yayi mata tambayar,

Yana gani ta lumshe idanunta alamun tana k'ok'arin kada ta saka duk k'arfinta ta ture shi daga kusa da ita, can ta bud'e su, mik'ewa tayi bayan ta fusge hannanuta daga kan nashi, sannan tayi kitchen ta barshi a wurin, shima lumshe idanunshi yayi, bai san me yake sashi kula ta ba bayan yasan dukkan su sun tsani junan su,

"Wani abun kayi mata ko?"

Jin muryar kausar d'in da yayi ne ya dawowar dashi daga duniyar da yake, mik'ewa yayi shima daga tsgunnawa da yayi, yayi wurin k'anwar tashi, tare da had'a lips d'inta da murd'awa,

"Wa aka cema ya rage shegen surutu?"

Kamila dariya ta saki da taga kausar sai faman so take da kwace daga hannun kamal, ta ruk'e hannayen shi tana fusga, shi kuwa sai k'ara ja mata baki yake, har idanun kausar ya fara cika da kwalla, ganin haka kamal ya sake ta,

"Haba ya kamal dan Allah"

murmushi yayi, sannan ya juya ya koma hanyar kitchen bai ce mata komi ba, yana shiga yaga sakeena na kaiwa da kawowa, tana zuba wasu abinci a cikin flask, jingina yayi a jikin bango ya cigaba da kallon ta da wannan mayun manyan idanun nashi, yasan tasan ya shigo amma ko da wasa bata kai idanunta kanshi ba,

"Ni kike had'a ma abinci?"

K'ara banza tayi dashi kamar bata jin hausa ta cigaba da abunda take, tana gama had'a abinda zata had'a ta d'auko su a k'aton tray, zata wuce shi kenan ta fita daga kitchen d'in yayi saurin tsayawa a gabanta tare da kwace tray d'in daga hannunta da ajiye wa akan cabinet, yana gani tayi wata harara dukda idanunta na k'asa sannan, ta juya ta zaga ta bayan shi zata wuce, ta sauri ya kamo hannunta, zata kwace kenan ya k'ara ruk'e ta,

"Nan da y'an awanun kausar da kamila zasu bar gidan na baza ki iya jurewa ba??"

Sai lokacin da kalle shi, fuskarta a had'e,

"Zan iya jurewa amma za'a sami matsala in har ka cigaba da tab'a ni"

Tana gama maganar ta fusge hannanta tare da daka mishi wata harara sannan ta koma ta d'auki tray d'in,

"In ka gama abinda kake zaka iya samun abincin ka akan dinning"

Tana fad'a ta fice daga kitchen d'in, lumshe idanunshi yayi tare da ajiyar zuciya, wai meke damun shi? me ya saka ya damu da ta nuna basa samun matsala a auran su?, me ya saka yake ta mata shishigi da shiga sha'anin ta?, ya lura tunda su kausar suka zo yake nuna halin da ba nashi ba, me yake damun shi?, ya dad'e yana tsaye a wurin da ta barshi yana ta tunani sai da ga baya ya fita daga kitchen d'in.

Bayan ya dawo daga masallaci, chewing gum a bakin shi dan cikin shi ya cika dam saboda tuwon da miyar ogbono da ya narka, ba gardama yasan sakeena ta iya girki, kullum yana cikin cinye duk abincin da ta saka mishi a gaban shi, kamila ya gani a zaune ta shirya tsab cikin atamfa ta d'ora k'aton mayafi akanta,

"Har kun shirya"

Yana maganar ya kalli agogon dake manne a jikin bango, yaga k'arfe 7:30,

"Ni da kausar mun shirya, muna tsoron in bamuyi sauri ba zamuyi missing flight"

D'aga kai yayi tare da cewa bari yaje ya shirya shima.

Sai da ya gama shirin shi tsab cikin wani farin yadi kanshi d'auke da wata bak'ar hula, k'amshi sai tashi yake daga jikinshi sannan ya fito, muk'ukkin motar shi a hannunshi, yana fitowa parlor yana duba agogan shi yaga k'arfe 7:50, d'auke idanun shi yayi daga kan agogon rolex d'inshi ya maida kansu,

Kausar da wani glass cup a hannunta tana shan ruwa, kamila da sakeena na zaune na hira, burki ya jaa ya tsaya, wai daman da ita zasu je, tana sanye cikin bak'ar abayar da tayi mata mugun kyau, fuskar ta ba wata kwaliya in ba hoda ba da kwalli, haka ya k'ura mata ido bai ma san yana yi ba,

"Yauwa tunda ya fito ku tashi mu tafi"

Kausar na maganar duka suka bar hirar, suka maida hankalin su kanshi, kamila ce ta mik'e tare da d'aukar handbag d'inta, sakeena kuwa sai da ta mishi wani mugun kallo sannan ta mik'e itama ta d'auki tata handbag d'in, ita ta fara ficewa daga gidan sannan sauran suka bi bayan ta, suka bar kamal a tsaye wanda ya kasa d'auke idanunshi daga kan matar shi.

(Jama'a na kasa gane inda kamal ya dosa, wai me yake tunani ne???

Anyways please vote, comment and share♥️)

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now