Three

2.5K 183 10
                                    

Jogging ya fito yi a harabar gidan, kunnan shi d'auke da AirPods yana jin karatun qur'ani, ya d'an jima yanayi saboda gidan akwai girma sosai, sai da ya gama tsab sannan ya wuce side d'inshi, yana shiga parlor d'inshi ya fara cire shirt d'inshi ya zarce bedroom d'inshi, direct bathroom d'inshi yayi, sai da ya gama wankan shi tsab sannan ya fito d'aure da towel a jikin shi, wurin dressing mirror d'inshi yayi ya fara yin abunda ya zaman mishi al'adarsa, sannan ya wuce closet d'inshi, shiga yayi cikin sweatpants bak'i da bak'ar shirt dan yau kawai zaman gida zaiyi ba wani wuri zaije ba, wurin mekeken standing mirror d'inshi yayi sannan ya fara taje kanshi, sai da ya gama shiryawa tsab tara da feshe jikin shi da turaruka masu dad'in k'amshi sannan ya d'auki wayar shi ya fito daga bedroom d'in, ko da ya iso parlor d'inshi, bai d'aga ido ya kalli k'aton hotan nan ba balle har ya kai idonshi wurin bedroom d'in da yake kallan nashi, dan yau baya da shirin yin tunanin shi, yana fitowa side d'in mami ya wuce.

-------

Yana shiga ya ganta a dining area tana ta faman shirya abinci, murmushi ya saki tare da k'arsawa wurinta, yayi kissing cheeks d'inta had'e da fad'in good morning, sai a lokacin ta lura ya shigo, tana kallanshi itama sakar mishi nata murmushin tayi,

"Kazo a dai dai yanzu nake shirin sawa a kiraka daman"

Kamal murmushin nashi me k'aramishi mugun kyau ya k'ara sakar mata tare da jawo kujera da zama, bai dad'e da zama sai ga wata y'ar farar yarinya kyakyyawa sosai wace bata wuce shekara sha tara ba ta sauko daga sama, tana ganin shi farin ciki ya kamata ta k'araso wurin shi a guje,

"Oyoyo Ya Kamal"

Shima d'ago yayi da manyan idanunshi ya ganta a gaban shi tana ta murna, shima farin cikin yake dan raban da ya ganta tun last year da suka zo ganin shi ita da Mami da Abba, zama a kujerar kusa dashi tayi, ta fara mishi hira da labarai,

"Mami ta turani gidan Ya Kamila wai celebration d'in dawowar ka na tsufaffi ne mu zamu ganka har mu gaji"

Kausar na maganar tana zumb'uro baki, Mami ko kallonta batayi ba tama shige kitchen, in mitar autar tata ne har ta gaji da ji, shi kuwa Kamal sai murmushi yake dan yayi kewar fitinar ta da rashin jinta,

"Tun asuba na fara shirin dawowa Ya Kamila na ta cewa na tsaya mu taho tare nace a'a tunda kowa na da mota kowa yayi hanyar sa kawai"

Kamal dariya ya saki,

"Kice kinyi missing d'ina da yawa shi ya saka har kika kusan yima yayar ki rashin kunya"

Kausar saurin kallon shi tayi ta zaro manyan idanunta waje tare da d'ora hannunta akan bakin shi,

"Shiru kada mami taji yanzu tayi sakwara dani a cikin gidan nan baka ga a hankali nayi maganar ba"

K'ara tuntsirewa da dariya yayi, in har kana tare da Kausar baka da wata damuwa dan kullum tana cikin saka ka dariya ne, hira suka ci gaba dayi har Mami ta dawo dinning d'in hannunta ruk'e da mug me d'auke da black coffee, ajiywa tayi a gabanshi sannan ta fara serving d'inshi breakfast, fried potatoes ne da egg da kuma shredded beef sauce, haka suka fara cin abinci suna hira jefi jefi, Mami na gaya mishi yaushe Abba zai dawo daga Paris, kausar ce ta d'ago kai ta kalle su, sannan ta fara magana,

"Dan Allah in kunga potatoes wa yake tuna muku?"

Duka suka juyo suna kallonta, ita kuwa bama ta bari sun bata amsa ba ta ci gaba da surutun ta,

"Ya KAMIL ko?, dankali shine favorite abincin shi, bani da wayo sosai a lokacin amma zan iya tunawa yana san duk abincin da akwai dankali"

Tsit wurin yayi, baka jin mosti komi sai k'arar ac, a lokacin da kausar ta gama magana a lokacin tayi danasanin abunda ta fad'a, hannunta na kan bakinta ta toshe, bayan wata mugun harara da kallo da mami keyi mata, shi kuwa Kamal tana gama magana ya sunkuyar da kanshi k'asa, ya k'urawa abincin kallo, ya damk'e hannunshi da yake kan cinyar shi, gaba d'aya fara'ar da fuskar shi ke d'auke dashi yanzu babu, ya had'e fuskar shi tamau kamar bai tab'a dariya ba, lumshe manyan idanunshi yayi, shi ya saka baya san dawowa gida saboda ko da yaushe ana cikin tuna mishi abunda yafi komi san ya manta a duniya, wani irin haushin kanshi yaji da har ya yarda ya dawo k'asar nan, zumbur yayi ya mik'e daga kan kujerar shi, dan yanzu abincin ya fita daga ranshi, Mami da kausar dake faman kallo shi duk fuskokin su d'auke da damuwa, a hankali ya furta ya k'o shi zai koma side d'inshi, yana gama maganar ya d'auki wayar shi yai hanyar fita, yana ji Mami nama kausar fad'an ta cika shegen surutu kan ya bar parlor d'in.

-------

Yana shiga parlor d'inshi ya k'ara cin karo da wannan makeken hotan nan, wani haushi ya k'ara kamashi, da alamun yau dai ba zai samu nustuwar da yake so ba, intercom ya d'auka ya kira securities dake waje ya umarce su da d'aya yazo, yana kashewa ya koma waje ya tsaya jiran sa, bai dad'e a tsaye ba sai ga wani ya k'araso, ce mishi yayi ya shiga ciki ya d'auki wannan hotan ya saka a d'akin kusa da nashi, danshi ko hanyar d'akin baya san yi balle har ya shiga ciki, ba'ayi minti biyar ba sai gashi ya fito, Kamal na ganin haka ya koma ciki, yana shiga parlor d'in yaga bangon wayam, bai ji dad'in abun ba amma ya tabbata in har ya bar hotan ba zai tab'a yin rayuwar shi yadda yake so ba.

Yana shiga bedroom d'inshi ya fad'a kan gado, had'e da lumshe idanun shi, yanzu jin mood d'inshi yake yayi k'asa, danasanin zuwa breakfast wurin Mami yayi, daga gobe zai fara cin abincin shi shi k'adai saboda baya san tashin hankali, wayar shi ya d'auko ya latsa kan instagram, baya san social media bama shi da ko wane social media account in har ba instagram ba, shima kawai dan ya dunk'a stalking d'inta ne, cin k'aro yayi ta latest post d'in da tayi minti biyu da suka wuce, post d'in abinci ne, kallan saman yayi yaga location d'in, cilantro Abuja, ba wani nisa da gidan su, abun ne yayi mishi dad'i, tunda ya dawo Nigeria me ya saka bazai yi having fun ba.

Sauri yayi ya mik'e ya k'ara fad'awa cikin closet d'inshi dan ya canza kayan jikin shi, black jeans ya d'auko tare da wata maroon shirt, bayan ya gama shirin shi tsab ya k'ara feshe kanshi da turare, ya d'auki muk'ullin motar shi me k'irar Mercedes AMG-GT yayi waje, in ka ganshi ya had'u iya had'uwa, ko yadda yake tuk'in a nitse.

Yana isa cilantro wurin a parking lot ya hangi motar ta, duk da shekarar shi takwas baya k'asar ba abunda bai sani ba akanta, in har ta taka k'afa ta bar gidan su ya sani, rayuwarta kamar film ce a wurin shi, sai da saisaici wurin motar ta sannan yayi parking a bayanta, ta yarda baza ta iya fita ba sai in har ya matsar da motar shi.

Fitowa yayi yai hanyar shiga wurin, tunda ya fito kowa sai ya kalle shi da matan da mazan, kwata kwata baiyi kama da d'an nigeria ba, bayan farar fatar shi ga laulausan gashin kanshi, ga wani kwarjini da yayi mishi yawa bayan kyawun fuskar shi, yana shiga ya samu wuri ya zauna, tunda ya shigo ya hange ta zaune da wasu mata su biyu, hira suke yi sosai harda dariya, Kamal jin zuciyar shi yayi tayi sama, kawai ganintan da yayi ya k'ara saka zuciyarta tafasa da zugi, bai tab'a zata mutum zai iya irin tsanar da yayi mata ba, wannan dariyar da take yi ta k'ara k'ullar dashi, ta tarwatsa mishi farin cikin shi amma ita tanan tana rayuwarta cikin nishad'i da jin dad'i, ji yayi tsanarta na k'ara bin duka jinin jikinshi, lumshe idanunshi yayi a dadai wannan lokacin waiter ya kowo mishi menu, already yaci abinci a gida amma a haka yayi ordering burger da kuma chapman.

K'ara kafa mata ido yayi, yadda take shigar ta dai haka tayi yau ma, kimono ce a jikinta bak'a bayan jan mayafin da yake kanta, fuskarta ba kwaliya in ba hoda da kwali ba, gani yayi sun mik'e gaba d'ayan su alamun sun gama me suke, suka fita daga wurin, suna fita ya d'auko wayar shi ya shiga danna wa, can sai ga abincin shi ya iso, ko kallon abincin baiyi ba ya cigaba da yin harkar gaban shi, sai da yayi minti talatin a haka sannan, ya duba Rolex d'in hannunshi ya ga 11:45, mik'ewa yayi yaje ya biya kud'inshi sannan ya fito, yana fitowa ya hange su a tsaye ko daga nesa yasan ransu a mugun b'ace yake, abun yayi mishi dad'i dan ya barsu a rana na tsawan mintoci, itama tana tsaye a wurin motarta tana ta duba agogon hannunta, yana isowa inda yayi parkin motar shi, yaga matan biyu da suke hira sunyi saurin kallon shi alamun suna shirin sauke mishi buhun masifa, yana had'a ido dasu dukan su suka kulle bakin su, had'e da sunkuyar da kansu, ba wanda ya iya furta ko, a, ya tabbata kwarjinin shi ne, ga fuskar shi da take a d'aure sosai ba alamun wasa ko k'adan a cikinta, yana gani suka koma inda take da sauri suna mata magana, sai a lokacin ta d'ago ta kalli inda yake, yi yayi kamar bata wurin ya ciro muk'ullin motar shi daga aljihun wandon shi ya bud'e zai shiga kenan yaji an fusgo hannunshi, abun ya bama Kamal mugun mamaki, cikin idanunshi take kalla idanunta na d'auke da kwalla, fuskar d'auke da tsan tsan abun mamki, yana jin hannunta da yake kan nashi na rawa, a hankali ta bud'e bakinta ta furta sunan da baya san ji.

"KAMIL"

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now