Eight

1.5K 153 6
                                    

Yau sati d'aya da neman shaheeda a waya bata same ta, har ta gaji da kiran layin ta, jiya ma sai da taje wurin mommy ta tambaye ta ko ta canza number bata sani ba tunda sunyi wata da wata ni basa kula junan su, mommy tace mata wayar tace ta sami matsala sai dai in har ta bata number d'in mijinta dan itama tanan suke gaisawa amma sam Sakeena tak'i kawai tace mata in sunyi waya dan Allah tace mata ta neme ta in har an gyara wayar tata, yanzu kullum tana cikin jiran call d'in shaheeda ta k'osa ta kira ta.

Bayan da dawo daga office tayi wanka ta ci abinci da dai duk abunda ya zame mata aladar ta, tana zaune gaban MacBook d'inta tana wani aiki da bata k'arasa ba a office d'azu, taji anyi knocking k'ofa an shigo, mommy ta gani a tsaye a wurin, itama binta tayi da kallo,

"Kije kawun ki na neman ki"

Haka kawai tace mata ta k'ara gaba tare da kullo mata k'ofar, Sakeena kuwa bin k'ofar tayi da kallo sai can ta mik'e ta zura k'atan hijab sannan ta fito tayi side d'in daddy, tana shiga ta tarar shi kad'ai ne a parlor d'in da tv kunne yana kallon news d'in karfe tara, samun wuri tayi a k'asa a gefan shi ta zauna, sannan ta fara gaishe shi, sai da suka gama gaisawa sannan daddy ya d'auki remote ya kashe tv d'in ya juyo da nutsuwar shi wurin ta,

"Muhimmiyar magana nake so muyi dake, dan haka ina so ki bani hankalin ki kuma ki saurare ni"

Gaban Sakeena ne ya fad'i, wata muhimmiyar magana kuma, dake wa tayi ta amsa mishi da toh da taga zata barshi da jira, tana ji ya fara ce mata,

"Kinsan yanzu ke ba yarinya bace, shekarun ki sunja, ban san dalilin da ya sa kike zaune har wannan lokacin ba aure ba"

Zuciyar ta k'ara harbawa tayi, me ya kawo maganar aure, me daddy yake nufi tukun da shekarun ta sun ja duka duka shekarar ta 25 kacal a duniya akwai mata da yawa da sunfi shekarun ta amma sunan ba suyi aure ba, k'ara jin muryar kawun nata tayi,

"Tun shekara uku da suka wuce bayan kin gama degree d'inki na zuba miki ido naga ko zaki kawo mun wani, na tsaya naga gudun ruwan ki amma na lura ko ajikin ki ke rayuwar ki kawai kike yi,"

Yana kai ayar zancen shi ya d'an tsaya na y'an skwanni sannan ya k'ara da cewa,

"maganar gaskiya na gaji da ganin ki zaune a gidan nan ba aure dan haka na samo miki miji"

Da mugun sauri ta d'ago idanunta dake kallon carpet da sauke su akan kawun ta, ta ji shi dadai kuwa, ita ya samo wa miji?? a dalilin me?, ji tayi gumi ya keto mata da taga idanun shi basa d'auke da wasa, bayan mahaukacin bugawar da zuciyar ta take, kwalla ce ta fara cika idanunta da kyar ta iya bud'e baki ta fara magana,

"Daddy dan Allah kayi hakuri kada ka mun aure, dan darajar Allah, wallahi nafi son rayuwata a ha...."

Saurin dakatar da ita yayi da hannun shi,

"Bance kiyi mun magiya ba dan duk abunda zaki fad'a bazai saka ni na canza shawarar da nayi ba,"

D'aukar remote yayi ya kunna tv tare da maida hankalin shi wurin labaran da ake yi,

"Ki tashi kije ki fara shiri dan bikin nan da sati biyu ne"

Sakeena da tayi mutuwar zaune ta kasa ko motsi, ga hawaye dake ambaliya a fuskar ta, me ta tab'a mishi a rayuwar ta da yake san yi mata auran dole, wasu sababin hawayen ne suka sake kwarara, da kyar ta iya samu ta mik'e dan jikin ta wani irin rawa yake, haka har ta bar parlor d'in, tana turo mishi k'ofar ta zube a k'asa a wurin kuka mai k'arfi ya kub'oce mata, tunanin iyayen ta da suka rasu ta shiga yi, ta tabbata da suna da rai baza su tab'a yi mata abinda bata so ba, wani irin zafi zuciyar ta take nata, a lokacin taji san iyayen ta da kewar su ya dake ta, kuka take yi a wurin sosai ga babu mai rarrashin ta, sai da ta gama kukan ta sosai sannan ta tashi daga wurin jiki ba kwari tayi d'akin ta.

Tana shiga ta zarce ban d'aki ta yo alwala daman isha tayi, tana fito wa ta samu abun salla ta fara, ko da ta idar ta dad'e akan abun salla sosai tana adu'a tare da kaima Allah kukan ta, tana gama addu'a bayan ta gama shafa'i wutirin ta d'auko qur'anin, shima ta dad'e tana karatu sai wurin goma da rabi ta mik'e daga kan sallayar.

Tana kwance akan gadon ta, kana gani kasan abun duniya yayi mata yawa, ga ba dama ta kira hamida yanzu dan dare yayi sosai kuma tasan in har ta kirata zata tada mata da hankali ne, shiru tayi a kwancen da take sai hawayen dake zuba a idanunta, ba abunda yake tada mata da hankali sai in ta tuna bama tasan wa zata aura ba, bata san halin shi ba, bata san fuskar shi ba, hawaye ne masu zafi suka sake zubowa daga idanunta, me ya saka daddy zaiyi mata haka, a matsayinta na marainiya bai kamata ya zalince ta haka ba dan tasan in har ita y'ar cikin shi ce bazai tab'a yi mata abun da yake shirin yi mata ba yanzu, dan shaheeda wanda take so aka barta ta aura kuma bai tab'a takura mata da maganar aure ba, gaskiya rashin iyaye babbar masifa ne a wurin ta, tashi tayi daga kwanciyar da take ta had'e cinyoyinta da jikinta tare da d'ora kanta akai ta shiga rera kuka me mugun abun tausayi, haka ta k'wana tana wannan kukan sai dab da asuba ta mik'e danyin salla.

Ko da ta fito wurin 7 zata ma daddy breakfast ta tsince mommy a kitchen d'in, da mommy ta ganta sai da tayi mugun firgita, saboda yadda ta koma, idanunta sunyi jaa wur bayan kumburan da suke, a rud'e tashi ga tambayar ta lafiya, Sakeena shiru tayi dan tasan ko ta gaya mata ba abunda zata iya yi, haka mommy ta hak'ura ta kyaleta, ita kuwa da taga mommy na kitchen d'in alamun ita zata yi ma daddy breakfast ta juya ta koma inda ta fito, tana shiga d'akin ta tayi ajiyar zuciya sannan ta rarumo wayar ta ta shiga yima oganta waya na wurin da take aiki tace mishi baza ta sami damar shigowa ba dan bata jin dad'i.

--------

Hamida da ta fito da sauri dan ta bud'e k'ofa saboda k'arar doorbell d'in ta ishe ta ga ba mai aikin ta a kusa, ta na wangale k'ofa taga Sakeena a tsaye tana kallon k'asa, gaban ta ne ya fad'i, ko daga shigar da tayi tasan ba lafiya ba, kafafunta na d'auke da bathroom slippers, bayan wani hijabi da ta maka a jikinta, Sakeena ta d'aga idanunta ta sauke akan k'awartata, hamida bata san lokacin da tayi kanta ba, ruke kafad'un aminyar tata tayi ta fara tambayar me ya faru, kana gani kasan a rud'e take saboda yarda taga kaman ninta ya canza, Sakeena najin muryar ta ta fashe da kuka hamida da mugun sauri ta jawo ta jikinta, haka suka tsaya a bakin k'ofa jiki yayi sanyi, sun dad'e a haka kafin hamida ta ja ta su shiga cikin gidan.

Sun zauna jigum bayan Sakeena ta gama bata labari, itama d'in yanzu kwalla ta cika mata ido ga sakeena da bata bar kuka ba har lokacin, haka ta dage da dunk'a rarrashinta, sai da ta gama kukan ta me isar ta sannan hamida ta kalle ta,

"Yanzu ba abunda zamu iya yi?"

D'aga kanta tayi, "ba abunda zamu iya yi dan duk dangin mu ba wanda yake jaa da maganar daddy, in yayi magana ta zauna ke nan ba mai iya canza ta sai dai in har shine ya canza kuma ma wannan abun ne me wuya"

Kwalla ce ta sake cika idanun hamida, kamo hannun sakeena tayi, ta saka cikin nata,

"Ki saurare ni da kyau kiji abunda zan gaya miki"

Sakeena d'aga idanuta tayi ta kalli babbar k'awartata tare da maida nustuwar ta wurin ta,

"Ki d'auki wannan kamar jarabawa ce daga wurin Allah, ki sani Allah baya taba d'ora wa bawan shi abunda yafi k'arfin sa, in har kika daure kika yi musu biyyaya to na tabbata zaki ga ribar ta, Allah ya gani da zuciya d'aya kike zaune dasu in har sunyi ne dan su cutar dake to suje dan kansu"

Tana gama zancen ta ta saka hannu ta fara share ma sakeena hawayen ta tana kiyi shiru k'awata kinji, bayan komi ya lafa hankalin Sakeena ya kwanta har ta samu tayi wanka ta shirya daman mijin hamida baya gari, hamida ta shiga kitchen ta d'ora musu shinkafa da wake za suci ta da mai da yaji, Sakeena bata koma gida ba sai da hamida ta tabbata ta kwantar da hankalin ta sannan ta k'ale ta tafi.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now