Twenty three

1.6K 192 16
                                    

Yana jingine makeken gadon shi, hannun shi d'auke da wani book yana karantawa, so yake yayi sauri ya gama ya kwanta dan gobe zai fara zuwa office, wayar shi ce ta d'auki yin ruri da take kan bedside drawer d'inshi, kamal a hankali ya juya ya d'auko tare da sakin murmushi me mugun k'ara mishi kyau, bayan yaga sunan da ya fito akan screen d'in, a niste ya latsa wayar ya saka a kunnan shi"

"Ya kamal guess what?"

Abunda ya fara ji kenan, ba sallama ba gaisuwa, matsalar shi da kausar kenan, ba ta da tunani wani sa'in,

"Yaushe guess what ya koma gaisuwa da sallama kausar"

Yana ji tayi shiru, allamun tana so ta bashi hakuri, shima shiru yayi yana jiran ta,

"Sorry, wallahi excitement ne ya saka ban gaishe ka ba"

Kamal girgiza kanshi yayi, yana ji ta fara gaishe shi, shima d'in amsawa yayi, sai da suka gama gaisuwar su tsab sannan kausar ta k'ara cewa,

"Kasan baban su saudat da ya sajida ya rasu d'azu da safe, a kano za ai zaman makokin"

Kamal d'aga kanshi yayi kamar k'anwar tashi na kusa da shi, su saudat ba wasu bane illa family friends d'insu, a daa sun zauna a unguwar su a kusa dasu shine dalilin da ya saka, kausar da kamila yin k'awance dasu da har suka saka mami ma ta zama k'awar mamansu, abba ya zama abokin babansu, sunyi zaman abuja amma yanzu gaba d'aya sun tattara sun dawo kano,

"Eh, mami ta kira d'azu ta gaya mun, daman nace gobe bayan na dawo daga office zanje gaisuwa"

"Muma gobe zamu zo, flight d'inmu da safe ne, dan haka kai da ya sakeena kuyi shirin k'arbar bak'i"

Da mugun sauri, ya d'ago daga jinginan da yake, zuciyar shi tace wani dum, bai tab'a zatan zasu sauka a gidan shi ba saboda sanin halin mami baza ta barsu ba gwanda su kwana a hotel dan kawai kada su takurawa sakeena, kausar ce ta k'ara magana kamar tasan mai yake tunani,

"Mami tace mu zauna a hotel, ya kamila ma, amma nayi ta rokonta da ta bari muzo gidan ka, a karshe dai sai da na had'a ta da abba sannan ta bari"

Da murnar ta tayi maganar, kamal lumshe idanunshi yayi dan yana ruwa, ta ina zai fara, bashi da ko kwayar shinkafa a gidan duk ya kwashe yakai gidan marayu, ga sakeena, yana tunawa da sakeena na can a kulle yayi zumbur ya mik'e hankali a tashe, in har k'annanshi suka zo suka ga mai yake mata baza suji dad'i ba kuma dole zance ya koma wurin mami da abba, in kuma suka ji shikenan tashi ta k'are, sauri yayi yai ma kausar sallama tare da cewa sai sun k'araso, sannan ya fita daga cikin gidan da sauri.

-----------

Bayan ya kaita band'aki ya sami wuri akan bedside drawer d'inta ya zauna, dole ne yayi mata kirki har su kausar su zo su tafi dan kada ta tona mishi asiri, dauko wayar shi yayi ya fara dannawa da zaman jiranta, ta dad'e a band'akin sosai har saida ta fara bama kamal haushi, dan yama gaji da duba agogo, shifa shi ya saka baya shiga sabgar mata saboda akwai su da shegen iyayi, taya mutun zai zauna a band'aki har na kusan awa d'aya, tashi yayi da zaman da yake dan yanzu ya harzuk'a, sannan yayi hanyar bathroom d'inta, ya sa hannun zaiyi knocking k'ofar yace mata tayi sauri a dai dai lokacin ta bud'e k'ofar, ko wace gab'a ta jikin kamal tsayawa tayi cak saboda abunda yake gani a gabanshi, tana cikin wani d'an k'aramin towel, gashin kanta da yake a jik'e duk ya sauka a bayan ta, hannunta d'aya ruke da wani towel ga ruwan da yake d'iga a jikinta, bak'ar fatar jikinta tayi wani kyau da ita ko daga ido, zuciyar shi ta fara mahaukacin bugawa, bugawar da bai tab'a ji tayi ba, bayan wani sabon abu da yake ji ya mamaye jikin shi, wani abu ne ya taho tunda ga kafarshi har tsakiyar kanshi, ya kasa d'auke idanunshi daga kanta dukda yasan kallan nata ne ke saka shi jin abubuwan da yake ji, a lokacin sakeena ita kuma ta kulle k'ofar da k'arfi a daidai fuskar shi har da y'ar k'aramar k'arar ta, yana ji tayi maganar ta cikin bathroom d'in,

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now