Twenty nine

1.6K 188 34
                                    

Tun bayan had'uwar ta da jabir a airport rayuwar gidan ta canza, ma'ana kamal ya fita harkar ta gaba d'aya, bata ganin shi, bata jinshi, ita abun mugun dad'i yake mata, in har ya fita toh har ta kwanta bacci baya dawowa in kuma ta tashi baza ta tab'a samun shi a gidan ba, yanzu sati biyu kenan bata saka shi a idanunta ba, ko abinci da tana mishi ta ajiye mishin akan dinning amma da taga wahalar da kanta take ko tayi mishi baya ci, yarda ta ajiye haka take zuwa ta d'auka ta daina.

Rashin ganin kamal ne da yarda baya takura mata ya saka ta cikin tsan tsan farin ciki kwanikin nan, bata da damuwar sa yanzu, rayuwar ta kawai take yi, tayi salla, ta karanta qur'ani in san kallonta ya motsa tayi, amma kuma wani sashe na zuciyar ta bai hana ta tunanin anya kamal ba wani mugun abu yake shirya mata ba, barin ma yarda taga ranshi yayi bala'in b'acci randa suka kai su kausar airport.

Bata tab'a ganin irin b'accin ranshi ba kamar na ranar, yayi mugun bata tsoro, duk bakinta ta kasa gaya mishi wata maganar dan ganinta tana gaya mishi mara dad'i zai buga kanta da bango, yayi mata jina jinan da sai tayi satit tika a asibiti, kuma sannan halin kamal wannan ba k'aramin aikin shi bane dan a azalimai ma ya fita daban, shi ya saka ta kama bakinta tayi shiru dukda a lokacin tana san gaya mishi shine yayi sanadiyar had'uwar ta da jabir tun farkon auran su.

Tana zaune a kan sallaya, qur'ani a hannuta tana ta raira k'ira a mai dad'in sauraro, karatun ta take cikin nustuwa da jin dad'i, k'arar doorbell d'in taji ne ya d'an tsai da ita daga karatun ta, shiru tayi dan tana so ta k'ara ji dan tunda tazo gidan ba wanda ya tab'a danna mata doorbell in ba lokacin dasu kausar suka zo, kamal in zai shigo key d'inshi yake amfani dashi, bata da wani da zaizo ganinta, k'ara jin k'arar tayi, sakeena ajiye qur'anin tayin akan sallayar bayan ta rufe tare da mik'ewa da fita, tana isa parlor tayi wurin k'ofa, a hankali ta murd'a muk'ullin ta bud'e.

Kamal ta gani a tsaye a jingine da k'ofa, kanshi a k'asa, bayan suit jacket d'inshi dake hannunshi, tie d'inshi a kunce, tsayawa tayi tana kallon shi dan bata san dalilin danna mata doorbell ba da yayi, a hankali ya d'ago da kanshi tare da sauke idanunshi da suka yi ja suka k'ank'anci a kanta, sakeena gabanta ne ya fad'i dan yarda taga gaba d'ayn shi ya canza, ya koma pale instead of fari, lips d'inshi sun koma purple, ga wata irin rama da yayi, bata san lokacin da ta tambayi kanta ba anya lafiya.

Ya d'anyi mintuna yana kallanata amma kina gani kinsan baya cikin hayyacin sa, da kyar ya iya matsawa daga jinginan da yayi, a haka ya fara dafawa zai shiga cikin gidan, sakeena kuwa ta bishi da kallo ta kasa koda mosti, yana fara taku d'aya yayi kamar zai fad'i, sakeena bata san lokacin da tayi kanshi ba tare da ruk'o shi, gaba d'ayan shi ya fad'a kanta, saboda baza ta iya da nauyin shi ba dukan su suka zube a k'asa a wurin.

Wani irin zafi taji ya kama jikinta dukda hijab d'in da ta sanya, ruk'e hannun kamal d'in da tayi dan ta gera shi daga kanta ya bata tabbacin zafin daga wurin shi ne, juya shi tayi ya zaman kanshi nakan hannunta, idanunshi a lumshe, hannunta ta saka akan gojin shi taji shi kamar garwashin wuta alamun zazzabi ke damun shi.

Sakeena tsayawa tayi ta bishi da kallo, sati biyun da bata ganshi ba shine ya koma haka, hannun ta ta saka ta fara d'an taba fuskar shi wai koda zai farka, dan ita baza ta iya dashi ba,

"Kamal, kamal, kamal"

A hankali ta fad'i sunan shi amma shiru, sai ma ganin da tayi ya d'ora hannushi akan cikin shi da d'amk'e cikin da duk k'arfin shi, tare da k'ara lumshe idanunshi da suke a kulle, alamun he is in pain, a hankali ya d'an far murgususu a jikinta, ganin yarda numfashin shi ya fara yin sama ya saka sakeena rud'ewa,

"Kamal, Kamal, me ya same ka?"

Da k'arfi take mishi tambayar, bayan tab'a shin da dake a fuska wai dan ya bud'e idanunshi, da taga hawaye har sun fara zuba a fuskar shi bayan ya damke hannunshi akan cikin shi, ga wani irin numfashi da yake fitarwa ya bama sakeena tabbacin wannan ba wasa bane da gaske bashi da lafiya, mallam isyaku ta kwada ma kira, sai gashi ya fito a guje, da yake da kamal ya fad'o mata a jiki, suna hanyar k'ofa ko cikin parlor d'in basu shiga ba, malam isyaku na isowa, ta fara ce mishi

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now