Thirty four

1.7K 156 28
                                    

Bayan sun dawo daga asibiti, an k'ara dressing ciwon k'afarta, sakeena na kwance akan makekiyar 3 seater d'in parlor d'inta, da kamal ya saka ta a dole sai ta zauna, shi kuma sai kaiwa da kawowa yake, ya kasa zaune tun ciwon da taji, bakinta a hangame tana binshi da kallo duk inda yayi, dan mugun mamaki yake bata, da kasa gane me ya saka shi rikicewa irin haka, tana yin mosti zai yi wurin ta da sauri ya fara tambayar me ya faru, kafar ta ce ke mata ciwo, ita tsabar mamaki kasa amsa shi tayi.

Yana tsaya a gaban dinning ya baje abinci kala kala a gabanshi da suka tsaya sukayi take away a bristol, tunani take yarda za suyi da uban abincin dan tasan baza su tab'a cinyewa ba, yarda kamal abinci kwata kwata bai dame shi ba, ita kuwa duk cin ta tasan itama kad'an zata ci.

Haka ta cigaba da zuba mishi ido har ya gama zuba komi a kan plate d'in, plate d'in har tsuro yayi tsabar ya cika taf, sannan yayi wurin ta, akan center table ya ajiye, sannan ya juya ya k'ara koma ya d'auko ledar magungunan da aka bata da bottle water, center table d'in ya jawo kusa da ita, sannan ya sami wuri ya zauna tare da d'auko abinci da yi dashi wurin fuskarta alamun yana bata ta karb'a taci.

Mamakin shi ne ya k'ara kamata, dan ta kasa ganewa, ita dashi wa zaiyi jinyar wani, mutumin da har yanzu bai gama samun isarsar lafiya ba har shine zai wani zo ya saka ta a gaba har sai taci abinci, maganar shi ce ta dawo da ita daga duniyar da take.

"In baza ki karb'a ba ki gaya mun sai in baki a baki dan kin bar hanuna na sagewa"

Harda d'aga mata gira yayi bayan ya gama maganar fuskar shi d'auke da wannan murmushin wanda ya saka duka dimples dinshi fitowa, Wani irin kallo tayi mishi, dan duk duniya ba abunda ta tsana irin wannan murmushin nashi dan tasan ba na tsakani da Allah bane, ta tsani taga yayi mata shi dan mugun k'ular da ita yake, sauke mishi harara ta cigaba da yi,

"Ce maka akai ina jin yunwa?"

Tana fad'a kuma ta gyara zama tare da k'ara daka mishi wata harara,

"Tsaya ma, ce maka akai ci na kawo duniya da zaka lodo mun wannan uban abincin,
mema ka mai dani tukun?"

Ji tayi ya tunsire da dariya, haba sakeena ta k'ara k'uluwa, ba abinda take sai aiki mishi da harara, kan ta ankara taji ya kamo lips d'inta gaba d'aya ya had'e tare da jan su,

"Wannan bakin naki"

Hannun ta ta saka ta fara doke hannushi da ya tamki leb'anta, yarda yaja l'eban yarda bazai mata zafi ba, amma duk da haka bai saka sakeena k'ara jin haushin shi ba, an gaya mishi ita kausar ce ta zai dunk'a yi mata haka, ci gaba tayi da kai mishi duka tana fad'in,

"Ka..ammal tkka..sakeni waalllhi, kayh khyale ni"

Tsabar ya rufe bakinta maganar ta bata fitowa sosai, dariya ya saki,

"Me?, me kika ce?, in sake ki?, me ya saka zan saki bakin da baya gajiya da yi mun rashin kunya"

Da taga zai cigaba da raina mata hankali ne, ga bashi da niyar sakin ta, ta saka farantan ta wanda sukayi zara zara saboda tsawo ta dage ta sakar mishi wani mintsini a hannun, ai kuwa ba shiri ya sake ta, tana gani ya ajiye abinci da ke d'aya hannunshi a kusa dashi, sannan ya ruk'e wurin da ta minstine shi, wurin yayi jajawur, abunka da farar fata, har ciwo ya bayyana a wurin.

Dadi abun yayi mata barin ma yarda taga yana yi da fuska alamun mintsinin yayi mugun yi mishi zafi, d'ago manyan idanushi yayi ya suake akan ta, tare da d'aga hannun da ta mintsine shi dai dai fuskar ta,

ZAFIN RABO ✔️حيث تعيش القصص. اكتشف الآن