One

7.7K 304 17
                                    

Da sunan Allah mai rahama mai jin k'ai.

Kaiwa da kawowa ake a cikin makeken gidan minister d'innan da yake a unguwar maitama a garin Abuja, gidan cike yake da y'an uwa da abokan arziki, fuskar kowa ka gani a cikin gidan tana d'auke da farin ciki da anushuwa, dan yau ne za'ayi babban bak'o,

A makeken parlor din gidan duka bakin suka zazzauna da yake dukkan su mata ne, ga kowa yayi kyau yayi shigarsa ta alfarma, barin ma matar gidan Hajia Rahima, wacce yau zuciyar ta k'al take d'auke da tsan tsan nishad'i kamar amma ta alkwari da gidan Aljanna.

"Yau ne dawowar babban d'an mu, wanda shekara da shekaru bai tako k'asar Nigeria ba, ni kaina da nake uwar d'akinsa bansa shi a cikin idanuna ba har na tsawan shekaru takwas, dan haka dole ne yau mu ci, mu sha kuma mu rawsaya, mu ragaje, muyi shoki dan kawai mu nuna farin cikin mu, ko ya kuka ce y'an uwa?"

Hajia laraba wacce take babbar aminyar matar gidan tayi jawabin tare da k'arashe maganarta da tambaya, ai kuwa gaba d'aya matan wurin suma shewa suka saka dan ba abunda zai hana su nuna farin cikin su yau,

Hajia rahima mik'ewa tayi ta zaman da take lokacin da wayar ta ta d'auki yin ruri alamun kira, fita tayi daga wurin hayaniyar, yayin da ta latsa wayar ta saka ta a kunne tare dayin sallama,

"Mami gani na iso airport ance nan da minti talatin jirgin su zai sauka, dan haka ku shirya ganin mu nan da awa d'aya da rabi"

Aka sanar da ita daga d'aya b'angaran, wani farin ciki taji ya k'ara kamata, hak'ika sanda take ma tilon d'an nata namiji ba k'aramin so bane, yau rabun ranta zai dawo kusa da ita, zatayi bacci harda munshari, godiya ta shiga yima na d'ayan b'angaren had'e da kashe wayar bayan sunyi sallama, koma wa parlor din tayi da sauri dan sanarwa abokan ta d'an nasu ya kusa shigowa.

-----

Sanya yake cikin dark blue jeans, da white shirt ya d'ora dark blue jeans jacket a samanta, bayan shades d'in daya d'ora a fuskar sa, yayi mutuk'ar yin kyau, kayan sun k'ara fitowa da farar fatar shi, duk inda ya taka sai an bishi da kallo saboda ya had'u, had'uwa ta k'arshe, tafiyar shi yake a niste kuma tafiyar kasaita, hannun shi d'aya rik'e da waya da take manne a kunnan shi, d'ayan hannunshi najan akwatin shi.

Waige waige yake yana jiran ganin inda babban abokin nashi zai b'ullo, bai kai k'arshen tunanin shi ba yaji an tab'a shi ta baya sauri yayi ya juya ya ganshi tsaye yana washe mishi hak'ora, shima d'in murmushin ya saki, murmushin da yake k'ara mishi mugun kyau, abokin nashi ne ya jawo shi jikin shi yana fad'in,

"Welcome back bro"

Murmushi ya k'ara saki, dukda ya tsani nigeria, ya tsani zama a cikin ta, yayi bala'in kewar y'an uwan shi da abokan shi, Imran ne ya sake shi daga rik'e shin da yayi, nan suka fara wasa da dariya har suka isa inda yayi parking motar shi, suna shiga ya kunna ya fara tuk'i, ci gaba sukayi da rahar da suke a cikin motar imran na bashi labarai kala kala, shi kuma ba abunda yake sai dariya, sun d'an dad'e suna hira, sai can kuma abokin nashi ya fara cewa,

"hope you're prepared dan na gaya maka mami ta tara mutane a gida suna can suna celebrating dawowar ka"

KAMAL girgiza kanshi yayi, baiyi mamaki ba, daman tafi kowa san ya dawo, kullum sukayi waya tana cikin yin mita, ya guje ta ya guji y'an uwanshi, ba irin threatening d'inshi da bata yi ba dan ya dawo har daga baya ta gaji ta hak'ura,

Imran ne ya k'ara cewa,

"Wai kasan ta yaya nayi convincing d'inta ta zauna a gida kuwa, da kana fitowa zaka ga jerin motoci a gabanka, bayan marok'an da ta d'auko suna wak'e ka, sai dai kawai ta tara maka jama'a"

Dariya suka saki duka su biyun, KAMAL baya amsa shi sai jefi jefi, daman shi magana bata dame shi ba, haka Imran ya dunk'a jan shi da hira har suka iso k'ofar makeken gate d'in gidan,

Suna shiga harabar gidan ya nemi farin cikin shi ya rasa, gaban shi yayi wani irin mummunar fad'uwa, zuciyar shi ta fara mahaukacin bugawa a cikin k'irjin shi, hannuwan shi guda biyu suka jik'e sharkaf da gumi, gaskiya yana ji yana da matsala, iyayen da suka tsugunna suka haife shi na cikin gidan amma duk duniya shi ne abu na biyu daya tsana, ba abunda yake san nisanta sama dashi, ji yake dama zai iya juyawa ya gudu ya koma inda ya fito, ya tsani garin nan, ya tsani zama a cikin shi, ya ma tsani zama a k'asar gaba ki d'aya.

Imran da yaga har yayi parking ya fito amma shi bashi da shirin fitowa ne yayi sauri ya maida kanshi cikin motar tare da sa hannunshi ya tab'a shi, KAMAL firgit yayi ya dawo daga duniyar da yake, ya juya inda abokin nashi yake tare da zuba mishi wannan manyan idanun nashi,

"Ya dai?, ko jira kaki iyayen naka su fito har waje tarba'r ka ne"

Sauri yayi ya cire seatbelt d'inshi, kan Mami da gayyarta su fito dan shi yasan kad'an daga cikin aikin ta ne, abokin shi ba abunda yake in banda dariya, haka suka fara takawa har suka isa side d'inta, tun kan suyi sallama aka banko k'ofa aka fara yin gwud'a, wata irin azababbiyar kunya ce ta kama KAMAL, shi fa duk abunda zai sashi ya zama center of attention ba san shi yake ba, baya san hayaniya dan bashi da wuyar yin ciwon kai,

Maman shi ce ta kamo hannushi tayi cikin parlor d'in dashi, kan kice me gaba d'aya y'an tsufafun nan sun rufe shi suna mishi ya gajiyar hanya, shi dai sai dai ya sunkuyar dakai ya amsa haka dai har ya samu suka mar matsa daga kanshi, nan aka k'ara zama aka saka shi a gaba da tambayoyi, bai samu ya samu kanshi ba sai da aka kusan azahar, shima ce musu yayi zaije ya d'an watsa ruwa sannan yayi sallah, yasan da ba haka yayi musu ba da baza su k'alle shi ba.

Yana zuwa k'ofar side d'inshi ya tsaya cak tare da zuba wa k'ofar kallo, ba abunda yake jin tsoro illa shiga cikin wurin dan yasan mai zai tarar, shekara takwas yanzu, wani zaiyi zatan ya manta, ya hak'ura saboda harta uwar da ta haife shi rayuwar ta take yi kamar bai tab'a zuwa duniya ba, amma banda shi, har yanzu yana jin zafin abun a zuciyar shi, har yanzu yana ganin abun kamar jiya ya faru, lumshe idanun shi yayi dan ya samu ya tattro nustuwar shi, can ya bud'e tare ta tura k'ofar ya shiga ciki,

K'ara tsayawa yayi da ya shiga makeken parlor d'inshi, parlor d'in ya canza gaba ki d'aya an saka sabun furnitures an kashe mishi kud'i, ya tabbata ya shiga cikin bedroom d'inshi abu d'aya zai gani, d'aga kanshi da yayi yaga k'aton hoto manne a jikin bangon parlor d'in, zuciyar shi ce ta k'ara wani mahaukacin bugawa, bai san lokacin da kwalla ta zuba daga cikin manyan idanun nashi ba,

Kamar za'a kiraka ka fito

Yayi maganar a zuci, ya dad'e a tsaye yana kallon hotan da kyar ya samu ya iya tattaro nustuwar shi, sannan yayi mishi addu'a a ranshi, ya goge hawayen da suka zuba a fuskar shi, tare da yin hanyar bedroom d'inshi dan ya samu yayi wanka da sallah ko zuciyar shi zata d'an sami nustuwa.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now