SADAUKARWA

884 124 69
                                    

Ina mika godiyata ga dukkan masoyana, da masoya wanan littafin, ina mika godiyata ga followers Dina, da masu labe da masu comment Allah barmu tare, ina neman afuwan duk wanda ransa ya baci, sanan ina neman yafiyar wanda yaji wani abu daya yi kama da halayyarsa, rokona daya ya gyara kawai, ina neman afuwarku akan tsarkin da na samu na rubutun, ina fatan duk wanda ya karanta wanan littafi zai tausayawa duk wanda ya musulunta, ya bashi kulawa ta musamman, daga aljihunsa, da kuma karfinsa, da kuma shawarwari sa,  mun bude wani platform na converts zamu rika taimaka musu da shawarwari da sadaka domin Allah, wanda duk yaji zai iya taimakawa domin Allah ya tuntubeni dn Allah, ko tufafi ko abinci ko kudi ga wanda yakeso, babu cuta acikin abin taimakone na fisabilillahi, daga nera goma, zuwa karshen kudi zaka iya badawa baya kadan baya yawa, duk wanda ya tuntubemu zamu fada masa tsarin jadawalin da kuma yadda za'a bayar da sadakar daya bayar, ko a sati, ko wata, ko a shekara kasaka nera goma d least, taimakone da muke sa ran daukarsa a aljanna. Ubangiji ya bamu iko watsapp dis line or call 08134642745, kuma idan kasan wata ko wani daya musulunta yake shan wahala ka bamu lambarsa ko ta ta private.

KARSHE

Tana cikin jikinsa, tayi lamo, rabonta datayi haka ta mance,

" Wai har yanzu bakon bai tafi ba?

Ta dan dago " wane bako?

Yayi yar dariya kafin yace " wanan me jar motar mana"

Tayi shiru sotake ta fahimci sakon nasa amma kuma ta kasa

" Wanan jan mutumin mai jar mota, dayake so  ya hanani kasar garar amarcin shekaru da yawa"

Kunya da dariya suka zo mata lokaci guda tagane abinda yake nufi,

" Kai abbansu!

Ya dan yi rau da ido yana dubanta " kinsan wanan daren zai zamo mai muhimmanci ne ko? Daren danayi ta wassafashi kafin da kuma bayan kin dawo gareni, ai dole na kagu ya zo shi"

Tana wasa da kirjinsa tace " ya kusa zuwa ka kara hakuri jibi ne ai"

" Hmmmmm"

Ya dan ja numfashi
" Jibi ta Allah ne, ga kuma tayi nisa na kagu na angwance"

Cewarsa kenan, kuma gaskiya jibin ta Allah ce sai abinda ya zartas cikinta kila abin ya zamo babu rabonsa ciki.

" Aff na manta fa, gobe zanyi tafiya can rigar ardo dn dauko su baffan insha Allahu, kuma za'a kamo ardo da dansa saboda mulkin kama karya, da zalunci da kashemin mata da sukayi"

Wani abu ya dan taba kirjinta " mata"

Ta manta ashe fa ya auri beeba ko, se yanzu ta fado mata.

Da sauri ta ture duk wani guntun kishi tace " Allah ya kiyaye hanya ya tsare ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, amma zaka biya gun azara ko?

Ya gyada kai ehh anjima zanje, idan na dawo ma zamu koma gaba daya har da ita"

" Allah ya nuna mana"

Shine zance na karshe da sukayi wanda ya zamo labarin kanzon kurege ya kuma juye zuwa wani abu daban, tafiyar tasa ta dawo da wasu lokuta mafiya muni a rayuwarta.

**********************†***************************************

Baba a daura auren nan dn Allah ni Zan zamewa Rahma alwali kuma yaya kuma ɗan uwa,

Wazeeri ya dubeshi sosai, yana jinjina SADAUKARWA irin tasa, tausayi dannasa ya kamashi lokaci guda, shi kuma tashi jarabawar kenan, kansa ya dafa yana masa aduoin alkhairi, " Zaid dan HARITHA Allah maka albarka Allah ya baka ikon jurewa da hakuri, ya yalwanta kirjinka da haske na hakuri, ya dayyaba zuriyarka"

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now