SADAUKARWA

773 146 17
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na ishirin da daya*

Rayuwar tayi Mata wani kulli da bazata iya warwarewa ba, Komi ta fice Mata akanta, zugar da shaidan yakeyi Mata kan imaninta ya Sanya ta sake rudewa, ganin haka yasa waziri yace maza a canza Mata gurin zama.

KASAR KANO

Gidane na dan kasuwa kasuwa Mai tarin dukiya da arziki Wanda bazai taba misaltuwa ba, Komi na gidan a wadace yake, mallakin gidan yanada matan aure har biyu da diyansa goma cif cif Amma ya wadatasu da Komi na rayuwa duk da yadda ake yiwa Yan kasuwa kallo da wata fuskar dn kankamon su da matsolancinsu, wanan kam ba hakan yake ba , Amma inajin hakan Bai rasa nasaba da kasancewarsa jinin sarauta dn baa San Yan sarauta da tsiya ba, alummar gidan wasu masu hadin Kai ne da juriya bazancen kishin banza da wofi mafi yawancin lokuta hajja mama da hajja karama matan gidan ana dauka ma Yan uwa ne dn yanda suke hade kawunansu suka nemawa mijinsu zaman lafiya da kwanciyar hankali, hakakna yaransu sunada wata tarbiya ta musamman wanan shine gidan baba Shareef wa ga maimartaba Wanda ya zabi kasuwanci fiye da mulki.

Wana guri shi su waziri da haj sukayi shawarar dawo da ita dn ta koma makaranta, tare da diyan gidan da suke sakkoninta.

Hakan kuwa yayi tasiri sosai dn ta Dan samu kwanciyar hankali ta kuma Soma hakuri da duk rayuwar data tsinci kanta acikinta mutum daya ta kasa mancewa a rayuwarta shine uncle dinta!

RUSSIA

Yqu aiki. Yayi Masa zafi jikinsa duk a mace yake, jiya nasihar da maimartaba yayi Masa ya taba shi ainun har ya fara raba dayan biyu, ko dai ya dawo ne mahaifarsa yayi taimako domin Allah ?

Wayarsa ce ta katseshi

Dada ce, da sauri ya dauka ko sallama baiyi ba Tace " inaga lokaci yayi daya kamata ka dawo ka agazawa annah, dn Tana cikin wani  Hali kuma nasan Kai kadaine zaka iya fitar da ita daga wanan halin"

Bata jira me zaice ba ta katse wayar , kuma ya Kira Taki dagawa.

Hankalinsa yayi mugun tashi annah ba lafiya? Ko rasuwa tayi? Ina mijinta?

Yayi ta dorawa kansa laifin barinta dayayi Wanda yayi alkawarin bazai taba barinta tayi kuka meyasa yayi haka? Wane Hali take ciki, ya subhanallah ya ambata Yana Mai tamke idanuwansa.

Cikin kwana da Basu wuce 30 ba ya Gama Komi , ya zabi  kasar legas a matsayin inda zai zauna, Zaid ne ya Gama Masa Komi , da asuba jirgin uTair aviation ya taso dashi zuwa Nija.

LAGOS
NIGERIAN ARMY BARRACK IKORODU

Barikice data tanadi manyan sojoji jiga jigai, da gidajensu, shima an bashi gida cikin jerin gidaje masu girma dn matssayinsa babbane, bayan reporting da sauransu ya nufi gida.

Murnar da Dada tayi baa cewa Komi ta wadata shi da Komi ya ci yasha yayi Santi, waziri ma ranan a gida ya wuni yasanya abin alfaharinsa a gaba anata labarin yaushe gamo, zayyan ya zama wani cikakken mutum Mai Kamala fuskarsa cike da nagarta, Bai canza saiide kana ganinsa kasan hutu ya zauna Masa zama na har abada, ahankali hirarsu ta gangaro kan yadda rayuwar annah dinsa ta Shiga, yayi kuka har Saida Dada tasoma Yi Masa fada da cewa " kaida nace kazo ko dn ka sanyaya Mata kuma seka bige da koke koke, idna kayi rauni ta Yaya zaka tallafa Mata kuma?

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now