SADAUKARWA

679 101 17
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na ishirin da biyu*


Ya dubeta cikin kaduwa yace " Daman ba abban LANGERI bane ya haifeki?

Ta danyi murmushi ganin Komi yazo karshe sanan tace " kwarai kuwa banana missionary babba, kuma ya rasu a wani fadan addini da akayi, shine Abba ya daukeni ya reneni, ni TUBABBIYA ce, kuma na taba aure har ma na haihu yarona yanzu ziq cika shekara uku a duniya Yana masarautar daura"

Se anan idanunta suka Dan kawo kwallah seta wayance Tace " toh kaga ai kuwa ni ba abin aure bace a gareka ko?

Shiru yayi Yana mazari ita kuwa saita dauka tsabar kaduwa ne da tsanarta suka sa ma yakasa katabus, dn Tana ganin Wanda addinin ma Bai damesu ba Basu dauki ire irenta ba da wata daraja balantana shi da yake da ra'ayin rikau na addini , tasan wanan kadai ba zai barshi Yama Kara kulata ba, Kai hanyar data bi ma aba zai bi ba.

Mikewa tayi zata bar gurin ta tsinkayi muryarsa Yana me cewa " dawo ki zauna Rahmatullah"

Ta dawo ta zauna Tana taraddadin me zaice da ita

Dubanta yayi sosai , wani Abu ta hango acikin idanunsa Wanda Bata taba ganin irinsa a idanun kowane namiji ba sai uncle dinta, da kuma baba waziri, wani tausayi ta riska a idanunsa da wani Abu da batasanshi ba, taga wani Abu tamkar na TAMBARIN soyayya

" Karki Kara kiran kanki da TUBABBIYA kinji ko, wannan kalma Allah Baya sonta, daga r anda kika amshi musulunci sunanki musulma, Allah ya gafarta Miki dukkan zunubanki, karkisha mamaki Allah yafi kaunarki fiye Dani, wanan kenan, Abu nabiyu ko kinsan annabinmu salallahu alaihi wasallam ya auri nana Khadija ra ne Tana bazawara kuma tazamo mace tagari gareshi har ya koma ga Allah baisamu kwatankwacinta ba, Idan Zaki zamomin Khadija banajin akwai wata matsala, sai batun mahaifanki wanan haka Allah ya so dasu, bamu da tacewa ,Amma kada ki Kara cewa ke arniya ce kin fito daga tsatson arna, ko kafirai zaifi kyau ki nemi Kalam jayyed kiyi amfani da ita, ki daraja iyayenki, sanan Abu na karshe shine ni imam naji nagani, inasonki ,Zan kuma ci gaba da so da kaunarki har iya wa'adin da Allah ya debarmin, sanan Ina Mai tabbatar Miki wadanan abubuwan da kika fadamin su sun karamin kaimi ne ma da kuma muguwar kaunarki tare da tausaya Miki, Ina kuma ji inason wanan abin da kika Haifa fiye da ma abinda zamu haifa, nasan a dokar masarauta Dan sarauta bayayin agola, dabadan haka ba Zan je na dauko Marwan nabashi soyayya irin ta uba mafifici"

Ya Dan ja numfashi Yana karantar yanayinta,

Tundaga kafafunta takejin Komi yayi sanyi takasa motsawa, Bata taba zata ko a mafarki akwia mutane irin da suna wanzuwa a doron kasa ba, Bata taba ji ba, bayan uncle dinta Bata taba ganin Wanda yasota haka ba , yanzu taji a ranta Koda Marwan Yana Raye batajin Idan ta fada Masa ko ita wacece zai iya aurenta ko aminta da ita, sai ga imam ya shallake tunaninta, wasu kwallah suka zubo Mata, shin har tanada wani zabi ne game da amince Masa? Bata da wani zabi irin su imam su take bukata tun bayan rashin uncle dinta datayi tanajin zai cike Mata wanan gurbin,

" Yanzu ya sayyadi......

Ya katseta da cewa " karkice Komi nide ki ban assurance na kina Sona kin amince Dani kawai kiga ikon Allah"

Shiru tayi na wani Dan lokaci

" Ya ilahi Rahmatullah kada kimin haka, inaji Babu wani namiji da zai kula da rayuwarku irina nasan Zan iya batare da gajiyawa ba ko gundura, pls give me that chance"

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now