SADAUKARWA

689 65 15
                                    

SADAUKARWA*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Babi na tamanin da uku"

GASKIYA ZATAYI HALINTA

Idanunsa jazur dn kukan Daya Sha, bayajin zai iya Kara awanni a cikin kasar Nigeria , Yana bukatar ya tafi can Abudabi dn ganin gidan jininsa, Ashe azara zata Haifa Masa lil princess da kullum take fatan samu, tausayinta ya Kamashi, haka Allah ya tsara musu tasu rayuwar kenan?, Saiga falmata da mijinta sun bige da bashi hakuri dn tsananin damuwar Daya Shiga. Kwana guda yayi  agarin abuja, ya yanki tiketin kasar Dubai, ya Lula, cike da doki da bugun zuciya na abinda zaije ya tarar!

Kwatancen falmata yabi tar tar har ya Isa babban apartment din Mai Kama da wani babban hotel, no 145 ya kwankwasa, bayan Yan mintuna wata tsohuwar balarabiya, ta bude Masa kofar, fuskarta cike da murmushi Tace " wa kake nema? Cikin larabcinta Mai ban sha'awa, Dan uwansa Kuma amininsa ya tuna, da Yana Nan Daya karbeshi anan, yaji Mai Tace , dn baya son tsawaita magana kawai de yace " RAHMATULLAH" ta fadada murmushinta zat bashi amsa kuwa saiga lil rahma ta yanko aguje Tana cewa " Kaka no bazanyi wanka ba ki barni"

Ganin bako yasata tsnkawa da gudu gurinsa ta rungumeshi Tana cewa abbu ni bazanyi wanka ba"

Tsikar jikinsa Saida ta motsa dn jin jinin jikinsa , ganin.mutum yasa ma'a tsayuwa kamar an dasata wazata gani kamar yareema?

Daukar lil rahma, yayi ya Soma sumbattarta Yana cewa "" ba Wanda zaimiki wanka, my lil princess I am here, ganin Nan kinji , dadddy is here Babu Mai tabaki, ya kwakumeta Yana maida numfashi, da kwallah ta murna,  ma'a ta tattako, ta tsaya gabansu Tana dubansu itama kwallar takeyi, " yareema"

Ma'a ta kirayi sunansa, ya dubeta cikin kuka yace " ma'a nine, nine ma'a, Ina AZARA?

Daki ta Masa nuni tsam ya ajiye rahma ya nufi dakin a hankali yashiga ciki Tana kwance kamar kullum, saidai yau ruf da ciki tayi, y karasa a hankali ya zauna gefenta, karfin turarensa na Burj Al Arab, ya sanyata bude idanu ta a hankali, suka sauka akansa, ta maida idanun ta rufe dn tasan Yana cikin ire iren mafarkan datakeyi, musamman dataji ance ma Yana Raye,, tasan tunda baizo nemanta ba, toh ya hakura da itane, ita ba macen zama bane tasani, ita azzaluma ce, yareema bazai Kara shaawar zqma da ita ba Inde rahma tana Raye,bayaga haka, ita din fa yanzu tanada ciwon kwakwalwa wa zai zauna da mahaukaciya? wanan yasanya ta kuma tsanantawa ranta damuwa ko zata mutu ta huta,

Sai de me, ji tayi ana goge Mata kwallar cikin wata irin siga data sani shekaru da suka wuce, wanan karon da sauri ta bude idanunta taganshi, Yana kwallah Yana girgiza Mata kanta, runtse idanun tayi Gam Tana cewa " dn Allah ka rabu dani ka tafi a mafarkina, nasan ba Kai bane, nasan kamin nisa, ka kyaleni na mutu na huta"

Rungumota yayi Yana cewa " it's ok dear, nine ba mafarki kike ba kuma ba gida bane, nine prince dinki, nine dai prince dinki kinji?

Wani kuka tasa Mai tsanani, tayishi kuwa kamar ranta zai fita, Yana makale da ita Bai Bari ta zubda kwallarta ba a ko ina sai kan kafadarsa da kirjinsa, sosai yayi kukan shima, ma'aa da lil suka shigo, suka samesu,lil ta dubi ma'a Tace Mata " meyasa mi mummy, da wannan daddyn?

Ma'a da Dan shafo kanta tace jeki kema ki tayasu, abbunki ne fa"

Yarinya ta dubeta Tace " ma'a kince abbu na Yana sama ba?

Da Yar dariya Tace " ai ya sauko , ance ya zo yaga Rahmatullah dinsa"

Da gudu yarinyar ta karasa ta Fado kansu Tana cewa " abbu ma'a Tace ka dawo daga sama, dn ka ganmu nida mummy ?

Rungumota itama yayai Yana cewa " nadawo har abada lil princess"

Seda sukaci Kuka suka koshi, sanan aka natsa aka Soma maida zantuka na ban mamaki, azara tana makale dashi, kamar zai gudu, Dr ma'a ta Kira, ya damesu kuwa anan falon gidan , yayi murna matuka, Nan ya Basu shawarwari, da kUma magunguna da zasu saya, ya ce yanzu Kashi 70 na ciwo ya Kare, zataji sauki a hankali, dn ciwo a hankali yake warkewa.

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now