SADAUKARWA

572 103 11
                                    

SADAUKARWA*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Babi na tamanin da hudu"

Wanan shafi tukwuici ne gareki M. ALI, yaba kyauta group, Allah yayi Miki albarka.

GASKIYA ZATAYI HALINTA

Yana tsaye daga jikin taga ta sama Yana hangota ta fito da sauri daga sashen Dan tsohon, jikinsa ya bashi akwia lauje cikin nad'i, meyasa ya Kasa Aminta da wannan tsohon? Idanun Daya Sanya musu yasa duk inda suka motsa Yana biye dasu, Dole yasan abinyi, Dole ya nemi sanin tsohon Nan, bazai taba yarda Yar Dan uwansa ta kuma komawa ruwa ba, Koda za'a tashi kasar najeriya da yak'i Mai zafi,baiga ta zama ba. Da wnaan tunanin Uncle Ben ya kwana, da sassafe kuwa ya Kama hanyan Niger Delta, so yake yaje yaji ko wani tsoho ya fito nemanta, a duk bincikensa baiyi katari ba, dn baiji labarin wani tsoho ya fito nemanta ba, saide ance wani soja ya fito nemanta a Karo na biyu!

Toh wane wane? Ko su wane wane wanan da suka nace Jan nemota?

Yana bukatar sanin dukkan rayuwarta ta baya. Toh Amma a Ina??

Shiri yayi sosai ya Kama hanyar Kano baisan wasu abubuwa ba game da ita yasan dai ta zauna a kano, kasancewarta Mai mugun zurfin ciki babu abinda suka sani game da ita, sai de yakan tuna sunan Kano da langeri shine iya abinda ya sani.

Abokinsa fatah ya tuno, ya Nemo lambarsa, bayan gaisuwa ne ya sanar dashi ya iso kano fa, fatah ya cika da mamakin zuwanben,

Yasan yanda Ben ya tsani hausawa da musulmai, shima dn shegen kansa ne kuma irin wadananda addini Bai damesu ba dinan ne, suna kirista suna musulmi irin yarabawan Nan ne da suke raba dayan biyu, kuma mayun naira, zai iya Komi dn naira, mafarin gamuwarsu a makaranta ne shi da Ben, har alaqarsu ta Kai haka.

Bayanin da Ben yazo Masa dashi babbane, Amma yayi Imani Idan zai saki naira toh Komi zaizo da sauki, kudi agurin Ben ba Komi bane, yanadasu Babu adadi, harkokin Dan uwansa kusan rabi a hanunsa suke, da legal da inlegal one's, Banda wasu harkoki dayakeyi NASA na boye kamar Saida makamai, da kayan maye, irin kudin dayake samu bazasu kidayu ba, tashin farko miliyan biyar ya dankawa Fatah, dn zai iya Komi Akan wanan zancen, fatah ya rude ba shiri ya bazama gari neman kan zance, ai cikin kwana biyu ya hado rayuwarta ta Kano, daga Nan suka fada LANGERI, Nan ma kwana biyu suka nad'o bayanai, bayan kaman kwana hudu duk puzzles din sun had'u,

Yayai murmushi lokacindaya Gama hada bayanan kaf! Ya dubi fatah yace " wato maza biyu ta aura? Dukka sojoji"

Fatah yace " dukkansu sojojine, masu kokari , sun Kai wani matsayi a military, abin zai danyi wahala"

A turbune Ben ya dubeshi yace " this time around the game is ours ( wanan karon wasan namu ne ba nasu ba), jinjina Kai Farah yayi yace "ok fine"

An zayyana Masa Komi, sede baiyi katarin samun zaid a kasar bama gaba Daya, Nan ya fara suspecting Anya tsohon na. Kuwa ba zayyan bane ko wani nasa, cikin matukar bincike aka Samo Masa hotunan cikin kankanin lokaci akasa a kwamfuta akayi Masa furfura da sauransu yadda duk Ben ya kwatanta saiga zayyan ya koma baba tsoho, wani tafi Ben ya somayi kamar mahaukaci , inda akwia wani Abu toh Bai wuce tsananin mamakin dayake dauke dashi ba na ganin basira irin ta zayyan, wato har hausawa musulmai sun San irin haka? ( Kaji Ben fa ko me ya maida mu? Bai San zamu bashi mamaki ba).

**************************************************************

"Yaran zaki kwasa kaman zaku fita motsa kafa, sai ki nemi Mai mota ya kaiki wanan adireshin dana Baki"

Muryar zayyan kenan bayan sun Yi kwana uku da tattauna yadda Ann zata koma can gida, saboda hankalinta ya tashi, so take ta koma kawai, tsoron Allah ya Mata katutu.

Ta dubeshi cikin rauni Tace " we don't have to do dis hibbini pls, iyayena zasu fahimceni dis time around"

Duba ya Mata na gaske kafin yace " kada ki yaudari kanki Ann wanan farki ne kikeyinsa ba gaskiya bane"

Mikewa tayi jiki yayi lakwas, tanaso ta rungume shi Amma batasan matsayin hakan ba, batasan matsayinta ba gareshi, Dole ta Masa sallama, ta ffice da yaran bayan ta fadawa mamanta zata kaisu gun siyan ice cream, da kyar ta barta kuwa dn Tace ta Kira driver itakuma Taki.

Tafiyarta da kaman Yan awanni shima ya shirya ya fice.

Can life camp suka hadu gidan abokinsa, shiri suka somayi na tafiya, mota zasu hau su tafi kano kafin a farga acan gidan....

Saide me? Ashe sunyi shuka ne a idon makwarwa, maigadi ya Shiga can Yana larabtawa father wanan tsoron fa ba tsoho bane Ashe, yaga suna magana da madam, yanzu ya Shiga dakin bayanan da sauran kayansa dukka.

Har tuntube father yakeyi tsabar sauri yaje ya duba yaga gaskiyar zancen. Aikuwa hakanne, suna tsaye cirko cirko Ben ya Fado gidan a haukace Yana cewa " where is Ann, where is she?

Maigadinne ya karanta masa Komi, duka ya kaiwa gini Yana huci " ohhhh they want to try us again, he took her away"

Father ne ya ce Masa who?

" Mijinta ne na  Baya data aura yazo ya Mana basaja kamar tsoho, ya gudu da ita"

Idanun father sun rine sunyi ja jazur yace " we must beat them dis time around, I will never let this happen even if it will cause my life"

Waya ya Soma bugawa duk wani Wanda ya sani mai fada aji, basa raba dayan biyu hanyar Kano yasan zasu bi, an hada plan Akan yqnsandan da suke wanan hanyar zasu sa road block kafin su pa su iso. Shiri akayi sosai duk wani Dan uwansa na Abuja da kaduna ya samu labarin, sun kuwa Yi tururwar fitowa , har daga kafancan sun kamo hanya, yau zasu nunawa hausawa musulmai karshensu, sun mance zaman lafiya yafi Komi Dadi, harda zama Dan sarki.

**************************************************************

Wazeeri Wanda bacci ya kaurace Masa a Yan kwanakin Nan Yana ta'ajubin rayuwa, da yadda mutane suka dauki MULKI wani babban Abu, inda har zasu iya Saida imaninsu, har su bada komi nasu, su hada da shirka, da manyan zunubai marasa adadi, Banda kisan Rai duk Akan mulki, mulki dai mulki dai, duk an tabe baa ta neman lahirar yanzu sai duniya wacce take budurwar Wawa, " akwai babban sirri game da diyanku Dana boye, fula
...ni saady, fulani yahanas danta Bai mutu ba, na sa jikana talle ya rubuce Komi ka nemeshi.......yareema....da SADAUKI duk.......ba... Ba...."

Zancen ya sarke, Amon mmuryar jakadiya ya ke jiyowa lokacin da take GARGARA,

Neman talle ya kamashi dn yaji wnaan sirrin, dn yasan tunda yaji zancen f Sadi yasan Abu ne dayake cike da rashin Imani da hadari, Yana iya tuno karonsu na karshe, ba irin bakaken aljanun dabara turo dn su sabautashi ba, dn ma shi din jajirtacce ne, da yanzu se buzunsa ai.

Cikin sirri yasa aka Nemo Masa talle, saide Kash! Baa samu talle ba ya tafi legas ci Rani! Ba ranar dawowa.hakan ya sake ruda waziri, yanaso yaji kan zancen tsoronsa Daya kada halimatou ta gurbata musu rayuwar diyansu.

Baisan abin ya wuce haka Nan ba.





SADAUKARWAWhere stories live. Discover now