SADAUKARWA

492 66 6
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi na saba'in da uku*

Donut fairy is my fan!💃🏻💃🏻💃🏻 I am dancing azanto,  kaman a mafarki, masoyan littafin nan kara karuwa sukeyi, nagode kwarai da kaunarku,   yau murnar comment na donut fairy ya sanyani rubutu ko da kuwa gajerene......... Shafinki ne donut fairy Kano.

Da asubahin farko waziri ya tashi fita masallaci, zayyan Daya kwana idanu biyu yana nazarin abubuwan dasuka wakana Wanda suka cabe masa, alwala ya dauro ya fito ya samu waziri yana tsaye yana salati ya kafa wa kofar gidan datake wangale idanu, zayyan bai fahimci me waziri din kewa wanan tsayuwar ba, seda ya Dan daga murya yace " Waye ya bar mana kofa ta kwana haka, a zamanin rashin tsaro haka"

Da ga bayansa zayyan yace " inaga nine baba cikin mantuwa"

Ya Dan dubeshi yace " toh gara ka rika kulawa de, wa nan zamaanin ka rufe kofa ma yaya ka Kare bare ka barta a bude"

Yace " toh baba"

Sun samu yareema a masallaci yanata nafiloli, waziri ya jagoranci sallar asubahi tare da yareema a matsayin ladanin sa abin gwanin sha'awa, wnaan Abu ya Dada sanya zayyan jin matakin Daya dauka kan bar masa rahman shine dai dai ko don ya kara tallafar rayuwarsa, tabbas rahma zata sake inganta rayuwarsa har ya zamo yanda yake mafarkin ganin ya zamto tun da can, yanajin kaunar Daya ke ma zaid ta daban CE ko Dan uwansa na jini albarka, bai sake tsinkewa da lamarin ba har saida yaga an idar da sallah zaid ya kama guri yanata tilawar karatun qurani cikin sauti mai dadin gaske amon muryarsa cike da karaya da wani irin ikhilasi, lallai ya Yarda akwai Wasu mutane da Allah yake nufar su da gyara ta hanyoyi zafafa yakuma yi musu Rahma ya shiryar dasu kan bigiren tsira, bakomi bane mutum yakeyi zaka bishi da tsinuwa kace Allah shirya kawai, wanan shine kulum abinda  waziri yake ja musu kunne akai, ko yace idan Kaga mutum yana aikata sabo, ka gode wa Allah kai da bakayi shi kuma kayi masa aduar shiriya saboda kaima din ba wayo da dabarar ka bane ya sanya baka sabon Allah, Sanan kulum yana Dora musu da wanan babban hadisi na hudu daga cikin littafin arba'una hadith inda karshen hadisin yake nuni da Dan Adam zai kasance yana aikata aiki irin na yan aljanna har ya zamo tsakaninsa da aljanna bai wuce zira'i guda ba sai littafi ya rinjayeshi ya koma aiki na yan wuta, ya mutu akansa sai ya shigeta, ko Dan Adam ya zamo yana aikata aiki na yan wuta har yazamo bai wuce zira'i guda ya shigeta ba sai littafi ya rinjayeshi ya koma aiki irin na yan aljanna sai kuma ya shigeta. Tun suna yara waziri yake biya musu hadisin nan har sun haddace , amma amfaninsa yau gashi ya taso, kudirar Allah ta wuce komi fa, yanzu shi din nan da ake gani salihi sai Allah ya jefo masa wata masifar da zata sanyashi sabawa Allah dumu dumu duk da baya fatan hakan amma in hakan na cikin kaddararsa shi ya isa ya hana faruwar hakan? Kuma shima ai ba ma'asumi bane Dan Adam ne me tarin laifuka, baka fankama ko k'ababa Dan Allah ya tsameka daga cikin masu aikata zunubai.

Zaid saida ya dauro Harda salatul duha Sanan ya mike zai bar massalacin suka hada idanu da zayya, ya Dan sakar masa murmushi , yakarasa sukayi musabiha Sanan suka fito, suna Dan hira, zaid ne yake CE masa " zayyan gaskiya banajin zan iya tarwatsa maka iyalinka dn ni naji dadi banajin na cancanci haka din gaskiya"

ya riko hanunsa yana gyara tsayuwarsa yace masa " Inajin bakasan yanda na dauke bane Dan uwa , INA kaunarka fiye da komi a rayuwata Allah ya dauramin kaunarka, kuma banajin akwai wani Abu da har zaka nema nagagara yi makashi ko menene shi ciki Harda iyalina gabaki Daya, Sanan ai sharia ta baka rahma takace sede in tak'i"

SADAUKARWAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin