SADAUKARWA

533 46 5
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na ishirin da uku*

Hayaniyar su hamrah ne ta fargar dashi, sun biyota waje suna cewa " yehhh tazama dauko dauko, ah tazama dauko Riga, ahh tazama dauko wando"

Ganinsa ya Dan sanyasu risina suna gaidashi, tana kwallah ta rungume hamrah Tana cewa hamrah ga uncle Dina"

Hamrah duba kiga ko mafarki nakeyi?

Uncle ne rayuwata hamrah kunga babban masoyi na abokina uwata da kuma ubana"

Yadda ta kankame hamran zakasan shi takeso ta runguma haka tajita cikin jikinsa tayi wanan kukan data Debi shekaru Bata yishi ba a hankali hamran ta Soma bubbuga bayanta Tana cewa " kiyi hamdala ga Allah tunda ya dawo Miki dashi lafiya"

Aduar samun natsuwa ya Soma Yi cikin zuciyarsa jikinsa har wani mazari yakeyi, yayi ta maza ya jingina ajikin garu dn kiris ya rage ya Fadi kasa sumamme, bayan yasamu natsuwa daga ilahi , ya tattaro wani murmushi Dole da yake Wanda yafi kuka ciwo ya dubesu

Yayi gyaran murya " ehemm eheemm"

Dukkansu suka dubeshi , idanunta jage jage da kwallah ta dubeshi

Yana tattakowa kusa dasu Yana cewa " amarya bakya laifi ko kin kasheni"

Dariya sukayi dukkansu ganin Yana saye da kayan manyan SOJOJI kuma ya Fadi haka

Hamrah ce Tace " tabdijan uncle Aiko de da munga dodan BARACKS tsaf sunyi Mana dirar mikiya su tada garin Nan gaba daya wallahi"

Yakura dake gefe Tace " uncle zayyan kaima de Wasa kakeyi ai ko marinka tayi wallahi zamusha tsallen kwado,"

Se a lokacin yayi Yar dariya yace " a'a wane su? Ai annah ta Yar gata ce ko obasanjo ta kashe zata kwana lafiya balle ni danake karkadhin ikonsa"

Dan dubanta yayi kafin ya kauda Kai ya dubesu yace " pls kuce Mata her tears are hurting me right here"

Ya Kare maganar yana Mai daura hanunsa kan saitin bangaren kirjinsa na hagu Dede Rabin zuciyarsa

" Kuma ku fada Mata ranar farinciki baa kuka, sanan kqjol dinta zai baci"

Ya wuce cikin gidan bayan ya dauki Marwan Yana Masa Wasa,

Tsareta sukayi da idanuwa har ta Dan tsargu ta dubesu Tace " meyene haka Kun tsareni da idanuwa kaman na mujiyoyi"

" Anya uncle ba rival din Yaya bane" cewar hamrah

Salma ta ansa ita ma tace "da dai walakin goro a Miya, irin wanan kalamai masu tasirai haka"

Dafe kirji tayi " ku rufamin asiri dn Allah kar ya ji, dn wallahi fushi zaiyi uncle tamkar uba yake agurina"

Yakura ma tayi belinta agurinsu

Da cewa " ahhh guys don't say dat zayyan uncle dinmu ne for long, irin kaunarsa da ita daidai take da ta mahaifi da diyarsa, Bai taba barinta tayi kuka ba tun tasowarta, shakuwarsu ta dabance"

Jinjina halayyarsa da irin kaunar dayakeyi Mata sukeyi sosai, kafin suka bi bayansa

Shigowarsu ce ta katse Dada daga ban Baki da tausasarsa da takeyi, ya kankame Anwar yanaji tamkar itace acikin jikinsa, yayi kokarin shanye kwallarsa cikin jarumtar da ko a fagen yaki bayajin ya tabayin irinta, a gabansa ta zauna ta zuba Masa idanu bakinta nason furta Masa kalmomi da zantuka masu dama, ko zataji sanyi a ranta, rashinsa yayiwa rayuwarta wani irin babban gibi .

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now