SADAUKARWA

470 61 1
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na sittin*

Sun murji juna kamar me, sanan komi ya natsa.
Azara CE ta dawo masa a rai ya rika sake sake, daga karshe yayanke hukuncin zai aureta kawai inde har zai iya zama da rahma wacce bai so toh yasan zai iya rayuwa da azara fiye da wacce yakeyi da rahma din dn yanason azara din kuma kusan ita ya fara so a rayuwarsa toh dama meyake nema? Zuciyarsa tace SO! Kuma ya samu, ya dan dubi rahma da take bacci a gajiye innocent face dinta ta bashi tausayi, Yana jin zai iya adalci kuwa? Ga kishi irin na azara, toh koma de meye Yana jin ya yanke shawara, saboda samawa kansa sauki in bai auri azara ba zai iya komawa ruwa cause he can't resist her, gashi yqna tsoron zinar nan saboda abinda monifa ta masa.. Haka har safiya Tayi , ta musu break fast ya fice aiki.

Wayarsa ya dauka ya kira layin Daya siya mata din, bugu biyu ta dauka muryarta a shake alamun tasha kuka sosai sai ta bashi tausayi ita kuma ta soma narke masa, shikuma Yana biye mata, kafin kace kwabo tsohon soyayya ta motsa suka tsunduma kamar bazasu fito ba, sun tsinci Kansu cikin shauki da bege, da kauna, suka koma ruwa!

Soyayyar azarah ta canzashi ya koma me faraa acikin gidansa, da wadatasu da komi, sudden change dinsa ya bata mamaki matuka , nan ta Dada samun kwarin guiwar kyautata masa tana godewa Allah kila karshen wahalarta tazo ne.

Gaba gaba fa abin ya fara zafi auren kawai yake bukata yanzu Amma ya rasa ta inda zai bullo, dole ya kirkiri kyautatawa iyayensa da ita Rahman. 

Yau kamar kulum ya dawo gida cikin faraa ya samota tana kallon tashar Islamic channel waazin  Dr zakir naik ya dauke hankalinta waazine akan convert da yadda zaa tattalasu, shima hankalinsa yakai kai, yadda malamin yake ragargazan musulmai dasuke nunawa convert matsi da takura, ya fede daga biri har wutsiya, jikin sa yayi sanyi jin wanan abubuwan Ashe nauyi ne babba bisa wuyansa.

Juyowa Tayi kawai ta Ganshi zaune gurui dashi, ta dan murmusa " yaya yareema yaushe ka shigo"?

" emmm yanzu nashigo, kina nan Ashe ya gidan ina boy kuma"

" Yana daki Yana bacci yaci abinci"

Ya gyada kai " hmmm, yayi kyau, guess what!?

Ta dan dago tace " what?

Ya miko mata tiketi 8 na hajji , ta zaro idanu tace na meye?

" na aikin hajji ne ki zabi duk Wanda kikeso Ku tafi"

Ta rasa inda zata sa kanta. hajji! Zata je.

Barin ta yayi agurin dan Tayi murnarta sosai, can jimawa ta hau gurinsa tasamoshi a tsaye batayi wata wata ba ta rungumeshi ta baya tana godiya , ya dan juyo da ita yace " seki shirya jibi zamuje gidan ki bawa duk Wanda kikaso,"

Tace " ai nagama shawara,daddy,waziri,dada,hajj,baba isah,, umma, mamma, sai ni"

Ya rike haba Yana kallonta ita batada son kanta duk abinda mahaifiyarsa ta mata bata damu ba ta sako da ita lallai masu irin zuciyarta daban suke.

A motarta sukayi tafiyar cikin nishadi duk da bawata hira sukeyi ba Amma de a sake suke tafiyar, gida ya rude da zuwansu itakam gidan waziri ta tafi tsabar murna, nan ta fada musu abin arzikin da ya samesu,  anan sukayi waya harda uncle dinta sukasha hira, hankalinsa ya kwanta tunda ta samu kwanciyar hankali. Abokinsa ya natsu ya rabu da wanan shegiyar matar. Nan take maida musu zancen rabuwarsa da matarsa Wanda basuji dadi ba duk da basusan dalili ba, ta wuni abunta anan kafin ta koma.

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now