SADAUKARWA

3.7K 235 15
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

Barkanmu da sake gamuwa cikin wanan Dan littafi nawa me suna sadaukarwa, wanan littafi dagaske sadaukarwa ne ga dukkan masoyana, sadaukarwa ne ga dukkan converts, sadaukarwa ne ga dukkan mata da suke zaman aure, kuma sadaukarwa ne ga kawata HAJEER NASIR ILA, Wanda mafarkinmu gudane kan converts, INA yiwa kowa fatan Alheri, nasake fada duk abinda ya faru cikin littafin nan da yayi kamanceceniya da rayuwar wani bayaga Mary Ann Rahamatullah toh tsautsayine ba yin kaina ba....

Masauratar LANGERE masarautace babba wacce take sananniya acikin nahiyar Africa ta kudu, a kasa mai albarka najeriya, masarautace me babban tarihi wacce tafice tsufan masarautar shehun barno a shekaru, masarautace kwarai da akeji da Ita a najeriya, tun daga kan sarki bilyaminu, zuwa sarki bobo, sarki idrisa,sarki muazzam,sarki bin baz, sarki ameer, sai sarki Shuwa, se sarki Talba,na karshensu sarki HARITH Wanda shi yake kan karagar mulki a yanzu haka. Ya mallaki diya goma sha biyar, namiji kwalli Daya ke gareshi, matan aurensa biyu, Fulani yuhanasu itace babba sai Fulani sadi, Fulani sadi Yar mutan agadez bazamarniya kyakkyawa, itace mace mafi izza da kishi, da German kai kasancewarta diyar sarauta, Fulani yuhanasu kuma diyar malamaice shiyasa ta fiye sanyi da kirki, da haba haba da jama'a, itace me dukka diya mata goma, Wanda duk sarakuna da diyan sarakuna suke aure, Fulani sadi ita ta mallaki da namiji haihuwar fari Wanda tsabar farinciki saida dukkanin najeriya ta shaida hakan, sarki harith ya sanyawa jariri suna ZAID, sunan saiyazo dai dai da madaukakin sahabin nan wato ZAIDU BN HARITHA, banjin akwai wani Abu da Allah ya dorawa maimartaba soyayyarsa irin ZAID, sone yake masa budadde da kowa ya Sani, Zaid ya taso cikin gata gatar data sanya masa izza,girman kai, fushi, fada, bayajin akwai wani Daya kaishi cikin fadin duniya , sarautar datake yawo cikin jinin jikinsa har bangare biyu ita ta sake tunzurashi, wanan daddage kansa sama yana shan kamshi. Duk wadanda suka biyo bayansa kuma matane, idan kanaso ka shirya da mai martaba toh kaso YAREEMA ZAID, wani abin mamaki kuma Zaid a hanun Fulani yuhanasu ya taso wata irin kaunace take tsakaninsu da Ita wacce mahaifiyarsa Tayi duk mai yiwuwa dn ta rabasu amma Abu yaki yiwuwa ya faskara, haka ta zuba ido,  Fulani yuhanasu da yaran ke kira da mama ta rike Zaid tsakaninta da Allah sonsa takeyi tamkar jininta hakan bai rasa nasaba da muguwar soyayyar da takeyima mai martaba.

A dakin mama kominsa yake, abincinsa itace, kominsa itace, tun yana kankani har ya soma girma.

Yareema ya debo kamar mahaifinsa kwabo da kwabo inka debe fari na mutan agadez da gashin Kansu me laushi daya dauko na daga mahaifiyarsa.

Wazeer zubair shine makusanci, masoyi kuma aminin mai martaba, Wanda amintakarsu tun yarinta ta samo asali, shima waziri gado yayi gun mahaifinsa kuma malamine, shi yake Jan ragamar limami, kuma malamin masarauta, mutum ne me adalci, me sanyin hali, me sanin yakamata, shima yanada matarsa guda, kuma dansa daya me suna ZAYYAN bn ZUBAIR,

Soyayyar da waziri kema dansa zubair soyayyace ta tarbiya islama, shiyasa ma ZAYYAN  ya fita zakka, cikin sakoninsa yanada tausayi,jinkai,hankali, da kuma uwa uba ilimin addini me zurfi dn saida ya sauke quranibda duk Wasu littafa masu amfanin tun yana shekaru goma , abotarsa da yareema ta samo asaline tun lokacin da iyayen sukayi shaawar kullata dn sun kasance aminai, tun ZAYYAN Yana yaro yake shan wahalsr zaid. Zaid na wahalar dashi matuka, tafuskar halayya halayyarsu ba iri guda bace ko kadan, duk wani hali na Zaid mabanbanci ne ga na ZAYYAN, Amman kasancewarsa me hakuri se hakan bai dameshi ba duk da matukar wahalar dayake sha.

Akwai wata rana sun fita hawa lokacin basu fice shekaru goma goma ba, dokin Zaid ya fara haniniya kuma suka rasa menene, ga yarinta tare dasu, kuma Zaid ya kori duk dogarawa yace duk Wanda ya biyosu seyasa an tsireshi, tsoron hakan ya hanasu binsu, nan Zaid da karanbani ya lulasu cikin wani daji, nan suka gamu da tsautsayi, Gurin Ashe cike yake da mutan boye, aikuwa doki yayi tutsu ya zubda Zaid a kasa har ya suma, zai tattake kirjinsa ya ida kasheshi, zayyan yayi saurin kifuwa akansa dokin ya tattake masa baya, ya barsu a yashe.

Gari ya soma duhu baaji duriyarsu ba hankalin masarautar ne kaf a yashe, mai martaba da kansa ya fita nemansu, tafiya me tazara sukayi kafin suka samesu sede kaf dinsu babu ma numfashi.

Gidan waziri zubair aka nufa dasu inda aka musu magani, duk sanan tarzomar hanunusu na sakale Dana juna.

Kwanansu guda ba Wanda ya farka, hakan yasa wazeeri yin tunanin ko harda sharrin shaidanu cikin lamarin, ruquiyya ya soma yi musu bayan mintuna kalilan kuwa guri ya dauki sowa da Wasu gurnanai na ba gaira ba dalili, kuka sosai aljanar ta soma tana cewa " zan fita wallahi zubairu kadena konani"

Wazeeri yace " karya kike munafuka bazan dena konaki din ba, me yaranmu suka miki zaki musu sanan muguntar"

Cikin sowa tace " wallahi wani abin alajabi ke garesu, wata iriyar SADAUKARWA na gani tare da tarihinsu, duk da KADDARA zata so rabasu, amma ka jajirce lokacin"

Wazeeri ya harzuka " munafukar banza mu bamu tambayeki w anan ba, Allah kadai yasan gobe, maganar da akeyi shine ki bar jikin koma wa kika kama in ba haka ba zan babbakaki"

Yaci gaba da karatun Yana tofa musu, aiko de tasa ihu tana cewa " natafi bazan sake waiwayarsu ba sai randa zancena ya zamo gaskiya wazeeri"

Cikin yan mintuna suka mike ras dasu, tun daga wanan rana ake kaffa kaffa dasu, kuma labarin da mai martaba ya bawa yareema yasa yaji ya kara kaunar zayyan amintarsu ta kara girmama, Fulani sadi batason wanan abotar acewarta abotar dan sarki sai dan sarki bawani kaskantacce dake karkashinsu ba, amma ba yadda ta iya dn ko shi Zaid din baima saurareta ba, duniya Abu biyun nan ta gagara galaba akansu Zayyan bn zubair da Fulani yuhanasu, ta gagara rabasu da danta.

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now