SADAUKARWA

544 78 11
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na hamsin da hudu*


Wanan zaman wani babban kalubale ne na rayuwarta, yadda suke cin karensu ba babbaka ya Sanya duk ta sukure, Sam Taki Bari ma su hadu , dawuri take tashi tayi abinda zataci tun safe har dare ta Kai daki, ta dauki duk abubuwan datake bukata ta garkame kanta a daki,Bata koma fitowa sai wata washegarin.

Tun Tana kuka har ta gaji ta daina, Takoma yin tilawarta da sallolinta saiko Hawa yanar gizo gizo Tana Yan bincikenta na ilimummuka masu amfani, kullum setayi niyar kiran uncle dinta saita fasa DN tanaganin yanda duk ya sake canzawa tun bayan aurensu da yareema ko meyasa oho?

Ta danja tsaki daga kwanciyar datake , yau ta gaji da Komi, sotake ta fita Tasha iska ko zataji sanyi cikinta Daya fara girma da kuma kafafunta da suka Soma kumbura ne suka dameta, ba shiri tasa hijabinta ta fito, Bata Tara's da kowa ba ta fice ta Soma shawaginta cikin barikin Tana ganin abubuwa daban daban, ko Ina da tsarinsa , iskar 'yanci datake shak'a tayi Mata dadi.

Saida tagaji Dan kanta ta dawo, sede sabanin yadda ta bar gidan tasamo Mata kadangarun bariki sun cika gidan  anata shewa gabansu kayan shaye shayene da batasan ma na meye ba, gidan ya turnike da hayakin taba, Tana shigowa ta Soma tari, hakan ya jawo hankulansu kanta suka bita da kallo, dakinta ta rufa Tana toshe hancinta dn wani amai Daya taso Mata,Allah yasani ta tsani warin taba Yana gigitata, tsabar amai wani zazzabine ya doketa ta kwana a haka.

Da safe zazzabin Bai barta ba, Dole ta nemi wayarsa Amma batama Shiga, Dole ta Kira uncle dinta , kamar bazai dauka ba saikuma jikinsa ya bashi akwai abinda ke faruwa , Sam bai yadda da wanan shegiyar kilakin ba, da azama ya dauka

" Uncle dn Allah Idan kana gari ko kuma akwai Wanda kasani yazo ya kaini asibiti Zan mutu"

Iya abinda ta iya fada kenan ta katse wayar ,

Gabansa ne ya yanke ya Fadi jin muryarta kadai ya Isa yasanya kasan tabbas batajin dadin sosai, dama isowarsa kenan ko inda zaije Bai Isa ba ya bada umarni aka wuce dashi can.

Kiran duniya yayiwa    Zaid amma baya dauka, Michele yasa ya musu magana, Amma Monifa ko kulashi basuyi ba ita kawayenta da suka kwana agidan Ashe wai Zaid din bayama garin,

Ransa a bace ya fada gidan , salati ya Soma saukewa ganin yadda gidan ya koma mashaya, kwalabene na tsadaddun barasa, kala kala,  da kwalayen rotimas,

Mikewa tayi ta Sha gabansa Tana kwalala wai kato ya shigo musu gida mijinta bayanan,

Ko kallo Bata isheshi ba, matsawa yayi inda yake kyautata zaton annah din zata iya jiyo muryarsa ya Rika kwada Mata Kira, da kyar ta lallaba tafito Tana dafe jikin gini

" Subhanallah Ann"

Ya karasa gareta kamar zai rikota sai kuma ya fasa, da kyar ta Isa motarsa suka tafi asibiti, shi yayi ta jelen Karin ruwa, harda Karin jini Wanda jininsu Daya, Daman kamar hadin Baki, .

Sai kusan magriba wayar gogan naku ya shigo, azafafe yace " Ina kuka fita da rahma?"

Ran zayyan ya baci irin mutanen Nan ne da Basu iya fushi ba Amma Ida. Sukayi fushi toh fa Babu Mai tarosu, cikin masifar fa Bai taba sanin yanada shi ba yace " Allah zai sakawa Ann kwatankwacin cin zalinta dakukeyi kaida matarka, Allah bazai barka ba Zaid, insha Allahu wataran Ann saitayi maka wani irin nisan da zakayi begen jinta da ganinta.....sai....."

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now