SADAUKARWA

549 64 2
                                    

✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babu na talatin da uku*

Waiwaye adon tafiya

Dagowa yayi yana duban kowannensu idanun ya ka mairam na kqnsa tsam babu alamun sassauci ko wani wargi, cikinsane ya bada wani kululululu!  " wanne ka zaba acikin sharuddan nawa?

Ta fargar dashi, baisan lokacin da wani karfin guiwa ya zo masa ba ya bata amsa da cewa" na zabi na fara auren Rahmatullah sena auri zahrah saboda ban taba mata alkawarin aure ba duk da ta nuna tana sona kuma..........."

Katseshi Tayi rai a bace tace " karyarka sadik ubanka ma dana Haifa bai isa ba baran kai, nagama magana seka aure Zahra ka auri waccan Baren, in kayi gardama na hana auren gaba Daya tunda an munafurceni a boye min yarinyar ta taba aure"

Sai a nan babansa yace " ah ah Allah huci zuciyarki baayi haka ba hajiya, tunda har ansa rana ,semuyi na Zahra din da wuri kafin wancan din dn mu kare martabarmu"

SH tashi yayi ya fice kawai tsabar takaici da bakin ciki, Dede korido suka hadu da zahrah, se wani karairaya takeyi, zai giftata tsautsayi ya sanya ta masa magana aikuwa ya huce kanta tsab kamar zai mareta, ya rufe gargadin dayake yi Mata da cewa " tun wuri kinemi miji wallahi dn nayi miki nisa sadeeq na rahma ne"

Ta tsaya sororo tana bin bayansa da kallon mamaki, aure kuma? Hmm da zata samu hanyar aurensa ai datafi kowa murna, irin kudaden dasuke kashewa su da iyayensu akansa baa cewa komi, wai duk dn su samu ya amince ya aureta...

Wacece Zahra? Zahra Bulama diyace ga alh Bulama Dan kasuwa Wanda zaman kano yasa suka zamo aminai da ahalin ka mairam , mutum ne Mai kudi nagani na fada Yar sa Daya tilo ZAHRA, tun tasowar Zahra Allah ya Dora mata son sadeeq, amma shi baisan ma tanayi ba, wasa wasa soyayyarsa ta kasa boyuwa agurinta, kasancewarta Yar gata yasa iyayenta suka nemi yadda zasu samu kan sadeeq din, Zahra irin shagwababbun yaran nan ne da iyaye suka gaama lalata musu tarbiya hakan ya dada nesantata da sadeeq dn duk kyaunta bayajin zai iya aurennta a matsayin uwar diyansa, haka iyayenta sukeso abin ya kasance kota tsiya tsiya, toh suma dia iyayen nasa suka nuna bazai yiwu ba gaskiya, suna son farincikin dansu, haka zance ya lafa, iyayen Zahra suka fara narka kudadensu gun malamai da yan tsibbu, cikin haka sadeeq ya samo annah, iyayensa suka Goya masa baya, alh Bulama ya karbai zancen auren sadeeq, dashi kuma akayi komi, se me zai faru?

Bayan dawowarsu daga langeri gun iyayen annah, sai ya samu ka mairam maahaifiyarsu bayan ta dawo daga wata doguwar tafiya datayi kasar saudi da zancen yarinya dai ba kabilarsu Daya ba, kuma ma ta taba aure ya gani haka a bincikensa nan ta tada kayar baya tace bazai yiwu ba sede a FASA dama tayi wanan kudirin, slh bulama ya bata hakuri kan kada Tayi haka girma zai zube, tadai  San yadda zaayi a aura masa ta gida se ya auri waccan, tunda kudi ba matsalarsu bace, abinda bata Sani ba bulama kanfen yakeyiwa diyarsa Zahra aiki de ya  dace dn seta zabi aura masa Zahra din, kuma ta haneshi dayace komi ga kowa har saita furta bakinta.

Zahra ta shigo ta samesu har lokacin suna tattaunawa, tamaida gidan su sadeeq naasu. ganin ta yasa ka mairam Dan yin faraa " su kwaise manyan mata"

Zarah tayi wani wal wal da idanunta dn jin dadin sunan, ko gaida su batayi ba dayake lelen ka mairam ce bawanda zaice komi, ko mamar sadeeq din Zahra bata kwanta mata ba saboda dabiunta, nan ka mairam tace mata " idan kin koma ki fadawa babanki yazo mu karasa zancen aurenku keda yayanki"

SADAUKARWAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن