SADAUKI

839 102 9
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*
 
*Babi na bakwai*


Babu shiri yaji shima wasu kwallah na zubo Masa,  dakyar yayi controlling kansa ya Yi ta maza ya Soma lallashinta, ya zaunar da ita Kam wani dunguren dutse, ya sa hannunsa bibbiyu Yana share Mata kwallah

" It's ok stop crying I am here Ann"

Dan dubansa tayi Tana ajiyar zuciya , muryarta a sanyaye tace " uncle why did she hate me so much"?

" Who is she"?

Ya tambayeta cikin bacin Rai

Ta Dan bude Baki a hankali tace " mamma"

Seta fashe da kuka,

Kunenta ta Nuna Masa dukka biyu Wanda sukayi jawur dn murda da suka Sha

Taci gaba " she always pull my ears nd se tsinanna kafira, me idon mayu, what those that mean?

Tausayinta ne y Kara lullubeshi, hanunta ya rike ya Soma janta dn su fice daga gidan , dn yanajin idan ya Kara mintuna anan zai iya fadawa sashen f.sadi ya Mata rashin mutuncin da bai ma San irinsa ba, suna tafiya ko kallon kowa bayayi har ya dire ta a dakin Dada

Fuskarsa ba annuri ya dubeta yace " have u eaten?

Ta girgiza Kai " no uncle"

Madafi ya Shiga ya debo musu abinci, a kan idanun Dada suka zauna Yana Bata shima yanaci , Yana tambayarta abubuwa Tana bashi amsoshi gamsassu, da hausa da turanci Nan ya fahimci ta Soma gogewa a hausa.

Dada ce ranta ya baci Ganin yasa tayi wanka yace ta kwanta anan ba inda zataje

Ta dubeshi Rai abace tace " Kai sadauki banason rashin kunya , kaje kanratsa tsakiyar masarauta ka dauko yarinyar Nan ka dawo da ita gidan Nan Kuma Banga alamun kana Shirin maida ta ba, me kake Shirin Yi Haka kenan"?

Shima fuskarsa a tamke wacce ta nunawa Dada din da gaske yakeyi. Yace " bazata koma ba Haka kawai arika cin zalinta yarinya marainiyar Allah Dada kin zuba idanu anata cutar da ita, da Haka zata koyi dabiu masu kyau kenan har ta ji shaawar zamowa daya daga cikin mu? Bayan bamu iya sadaukar da Komi dn rayuwarta?

Dubansa tayi a Dan sassauce tace " waye ya ke cutar da ita din"

Ba wani shakku yace " yarinyar Nan ta fadamin kullum se mamma ta zazzageta ta mammareta ta mude Mata kunne ta Rika ce Mata tsinanniya kafira Yar mayu, wanan shine halayenmu da zata kwaikwaya? Sune abubuwan dazataji tana shaawar mu? Dada in hakane kuwa muna kuskure, yawancin lokuta Wanda suka fita girma ma idan sun musulunta mune muke kyamatarsu muke muguna musu har suji sun hakura da musulunci saboda Basu ga wani haske cikinsa ba, dayawa ahakan suke komawa ruwa, Amma idan kinga yanda Wanda sukayi reedda suka koma addinin da bana musulunci ba gatan da ake Basu kadai ya Isa ya Sanya ma su ji lallai nanne gurin zamansu, Amma mu common karamar yarinya mun kasa sanyata taga kyawun addininmu da dabiun mu Dada? Saboda Haka na e bazata koma ba"

Tashin hankalin Dada bibbiyu ne, da halin da Ann take ciki da Kuma kokarin danta gurin jajircewar Ann bazata koma masarauta ba, waya Isa ya hanata komawa? Yadda sarki yake ji da Ann akwai Wanda ya Isa rabasu? Idan maimartaba yasa doka ubansa ma bai Isa taketa ba bare shi, toh shi waye da zaice Ann bazata zauna ba acan?

Wadanan batutuwa sune tashin hankalinta, shigowar waziri ne ya sanyata  yin shiru, a tsaye ya samesu cirko cirko,

" Lafiya naganku kuwa a tsaitsaye?

" Saukar yaushe kaikuma zayyanu?

Kawai kuka ya sanyawa waziri Yana cewa " baba dn Allah kar amaida Ann masarauta wahala take Sha"

Idanunsa akansa cikin mamaki yace " dama Kai kaje ka daukota anata nemanta hankulan kowa ya tashi musamman na Mai martaba, toh maza sakota a  gaba mu mayarta banason sakarcin banza"

Da kyar ya tursasa Masa tashinta daga daddan barcinta, itama kukan takeyi ta kankame sadauki  har suka Isa , iso akayi musu sashen hutawar sarkin Wanda duk hankalinsa a tashe, Zaid dayake Ganin ikon Allah yayi tsumu a gefe, mikewa Mai martaba yayi ya rikita ya rungume Yana cewa " gimbiya Ina kika Shiga Haka kin daga Mana hanukula"

Wazirine ya Dan gyara zama cikin kunya yace " ayi Mana afuwa rankashidade Ashe yaron Nan ne yazo ya dauketa dazu daga dawowarsu"

Murmushi maimartaba yayi Yana jinjina zazzafar kaunar datake tsakanin zayyanu da Ann, yanaji kaman yafi sonta a kansa ma, ko don abin nasu harda ya rinta ma

Maganar zayyan ce ta katseshi

" Rankashidade Ann fa batajin dadin rayuwa anan"

Wani duka waziri yakai Masa

" Ashsha ashha waziri meye Haka ma barshi ya Fadi abinda ke ransa kasan kowace hujja ce gareshi, Kai zayyan Fadi duk abinda kake gani zai taimaka mana gurin ceto yarinyar Nan"

Babu kunya ya zayyane Komi, idanun sarki suka jirkice suka zamo jawur, ransa yakai matuka gurin baci,

Cewa yayi su dauki Ann din su tafi da ita har hutunsa ya kare zaiyiwa tufkar hanci, waziri kunya kamar ta kasheshi, gashi yasan yau Babu zaman lafiya shida SARAKI Allah kadai yasan abinda zaiyi Mata, shifa kaunar da mutane biyu ke yiwa Ann ta fara bashi tsoro, wanan bazai amfana Mata Komi bafa Sai tsagwaron tsana tunda gidan sarauta ne bakin jini zatayi.

Cikin tashin hankali ya Tisa zayyan da Ann din agaba sukayi gida.

Zaid mamakin mahaifinsa yakeyi, Wai har yaushe yarinyar Nan tazo ta mallake kowa? Kowan ma harda babansa, dakansa ya nufi sashen f Sadi , Sai ji tayi ana Yi Masa iso, ta Yi mamakin ganinsa a wanan lokacin dn bakasafai yake zuwa sashen nasu ba  Sai wani gagarumin Abu ya taso, yadda ya Fado ya wuce uwar daka tasan ba lafiya ba, tashi tayi Tana yauki tabi bayansa, sede yadda ta Tarar da fuskar Nan tasa yasata Shiga taitayinta dubanta yayi ba sassauci yace " me yarinyar Nan tayi Miki kike cin zalinta?

" Wace Diya fa?

Ya tattako kusa da ita yace " diyar Dana maidata tawa, na Bata yanci nayi Mata shamaki da bauta, na bata gurbin Yar halal acikin masarauta, kin ganeta yanzu?

Dubansa tayi zuciyarta har wani fat! Fat! Fat! Takeyi dn tsabar rudu, bakinta na in Ina ta har hado kalmomin da kyar

" Kace Yar halal? Toh ni agurina tsintacciyar mage Bata mage kum.............

Tsawar daya doka matace wacce ta sanyata har Taja Baya cikin razana ya sanyata kaduwa cikinta ya bada wani Kara kululululu,

Ya nunata da yatsarsa Yar manuniya yace " wallahil Azeem duk Randa kika Kuma tabata Zan Yi Miki hukuncin da har ki mutu bazaki mance ba, Azzaluma marar Imani kawai, wallahi nayi nadamar saninki sa'adiya"

Ya fice ya barta Nan, jikinta har rawa yakeyi, luuuu tayi zata Fadi dn tashin hankali taji an rukota , Zaid ne Wanda idanunsa ya cika shima da tashin hankali...............

Barka da juma'a

Ya tafiyar takene

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now