SADAUKARWA

696 105 14
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na goma Sha  uku*



Gareki anty rabin katsina yaba kyauta.

Rayuwar ta mikawa dukkanin bangarorin dodar, babu wani gargada, komi na tafiya dai dai, I zuwa yanzu habeeba ta Dada gogewa, hausa kuwa abakinta tamkar jakar kano, ta saje da dukkanin hausa Fulani, sede Idan kaganta tafi Kama turawa haka ko Barbara yanyawa saboda farace tas Kun San farin kabilar Igbo de har wani jaja jaja yakeyi, jin hausarta kuwa da iya Karin maganarta ya Samo asali lokacin data maida hankali kan littafin magana jarice, daganan ta Soma lalubo su ruwan bagaja, jiki magayi, iliya Dan Mai karfi, malikussaifi ibn ziyazanun, ruwan bagaja, kallon kitse, su alfu Laila da maka mantansu Tana jin dadin labarun nan sosai takumayi zurfi cikinsu, karatun addini kuwa nema take tazama wata karamar malama, kafiyarta da naciyarta ya kaita ga gaci.

Alakarta da da maimartaba datake Kira da daddynta, ta zama wata Mai karfi kullum suna tare, ahankali ya dorata turbar zaman gidan sarauta ta gane Komi ta  fahimci komi,Tana kuma bin tsarin Komi, annah ta koma Yar gida dai kowa yasaduda, kirkinta kuma ya jawo Mata farin jini gurin barorin gidan,Bata dauki kanta Komi ba, har a cikinsu Tana zama ta karanta musu labarai na ban tausayi da ban dariya, haka zalika mutum ce Mai yawan alheri, kaifin kwakwalwarta kuwa har Yana bawa waziri mamaki, har yakan ce a ransa " da yanzu mun rasa mutum irin annah da mun tafka babbar asara ai"

Yanaji ajikinsa yarinyar Nan zata amfani alummar musulmai Nan bada jimawa , Yana Mata aduar samu ingataccen Imani ko bayan ransu, Yana Mata fatan samun mini nagari, Wanda zai riketa da gaskiya da Amana ya tallafawa zuciyarta wajen tabbatuwar da kafuwar imaninta.

Bayan shekara biyu ta sauke littafai da dama, cikin su harda qurani Mai girma, Dede wanan lokacin ne kuma ta shiga ajin sakandare na shida, Tana kuma da shekaru goma Sha shida na haihuwa, ta sake girma abinka da Mai gabban jiki, budurcin seya amsheta sosai.

Ko Ina mutanen RASHA??


St Petersburg FL

Kowa hada hadarsa yakeyi, ba kowa da ruwan kowa, suna zaune wani guri Mai ban shaawa, teburi ne Mai tsari dauke da abubuwan Sha irin cimakar fararen fata na RASHA, zayyan bredin donot yakeci da lemon mangoro, shikuwa gogan naka beer yakesha, kadan kadan Yana kurba, tun fitowarsu daga gidan horo na soja ya daurawa kansa dabi'a Shan karamar barasa, Wanda kussan dukka garin suna ta'amulli da ita saboda mugun sanyi da akeyi, acewarsa shima sanyin na damunsa, shikam zayyan bai Dora a ka ba, adua ma yakeyi shima ya daina, raurin Kai irin na yareema Zaid yawuce duk yadda ake tunani, tun zayyan na masifa, Yana fushi, har ya hakura ya koma nasiha, Yan Mata kuwa yayi su kala kala, yace Dole ya nemi Mata dn halittarsa ce hakan, kuma ga sanyi shi bazai kashe kansa ba Allah gafururrahim wata Rana bazaiyi ba,

Shikam zayyan Yana mamaki inda zaid duk ya baro iliminsa na addini sallah da azumi kadai su ya Rika wajibi a rayuwarsa, sauran duk gani yakeyi takura ne, abinsa ya Kara kaimi ma tunda ya shigo cikin turawa, rayuwarsu na bashi shaawa suci karansu ba babbaka, ba Sanya idanu, inda Mata dubu zaka kwana ba Mai tuhumarka, Yar guntun tarbiyar tasa duk ya zubar, dama Bai maida mace Komi ba, shiyasa yake canzata yadda yaso sukuwa sai suyi ta binsa, abin Kamar jaraba dama ance wai Idan shaidan ya kada maka ganga toh fa bakajin Kira!

Zayyan najin takaici marar adadi kan halin da Dan uwansa yake ciki.

Aduk iskancinsa Bai dauki macen da musulma ba wata aba, yakance maleji yakeyi Idan Yana muamala dasu, ya kirasu WUTAR KASHE GOBARA, sune Mata mafiya kaskanci agurinsa komin kyawunsu. Nace to muje zuwa dai!

A hankali ta ratso cikin gurin Tana wata irin tafiya Mai daukar hankali, mace ce me matsakaicin kyawu, sede akwai halitta wacce ita take Kara Mata kyawu nagani na fada, daga gefensu ta zauna ta zubo Masa idanunta Kamar zata cinyeshi, yanayin shigar Tata ta nuna ita musulmace dn ta yane kanta da Dan yalolon mayafi, gashinta irin na zabarmawa ya zubo an tufkeshi ta baya, akwai Dan wani Zane kanana a fuskarta Kore Kore dayake nuna ita Yar kasar NIGER ce, ganin zatayi asararsa a yau ya Sanya tayi saurin mikewa dn suna Shirin fitane daga gurin cin abincin

" Privet dobryy vecher" ( sanunku Ina wuni)?

Kallonta sukayi da tsananin mamaki, jin sunyi shiru tace

" Sorry English"?

Haushi ne ya Kama zayyan yace " hausa"

Wani Dan ihun dadi tayi tace " Kuna jin a hausa?

Mamaki ya Dada kamasu Kamar me

" Dn Allah kunajin a hausa nace?

Zaid ne yace " eh munajin hausa meyene?

Yar dariya tayi ta matso kusansu tace " a yau na samou Yan ouwa a kasar ga, finally, pls inaso mu kills abatta da Kai"

Ta nuna Zaid, tuni zayyan ya bar gurin Dan yasan kwanan zancen , Yana girgiza Kai tare da tausayawa wanan baiwar Allah dn yasan tashiga tarko mummuna.

A tare suka fito suna takawa

Tana wani firirita Tace " sunana AZARA Yar kasar NIGER"

Ya Dan gyada Kai yace "umm yayi kyau"

" Kaifa?

Ya danyi shiru kafin yace " ni Dan Sudan ne"

Ta juyo da mamaki tace " kumma kakajin hausa?

Ya danyi murmushi ya ce " namata Yar Nigeria ce shiyasa"

" Ou tou ko da naji fa"

Sunyi musayar adireshi da lambar wayoyi suka rabu.

A gida ya samu zayyan har ya shiga daki yana Shirin kwanciya hanunsa rike da qurani Yana tilawa, baiko kalleshi.

A zafafe yace " wia me kake nufi ka taho ka barni?

Saida ya sauke wata Aya acikin suratul naml sanan ya dubeshi Ido cikin Ido

Yace " Koda ka zamo sarki bazan taba bin dokarka ba dn na sabawa Allah na, Mai yasa Zan tsaya a inda aka kullah Haram? Dn meyasa in Kai bakajin tsoron Allah ni inaji Zaid, after all is ur life kayi duk abinda kaga dama Amma karka manta de duniya budurwar wawace walalhi!"

Sakwato yayi Yana dubansa yace " kana maidani Kamar wani Arne wallahi, ance maka musulmi zai dawwama a wuta ne?

Kuma ai Allah gafururr ahim, Idan nasake girma nayi aure zanyine aka fada maka, kai tunda ka tsaya kidahumanci toh karka matsamin aljanna tamai raboce"

" Hmmm kana ban mamaki Zaid walalhi, ai arnan dayawa basa ma irin muguwar halayyarka da zasu karbi kalma rananr su bar duniya da zasu shiga aljanna su barka Baki bude, akwia dayawa daga cikinsu ma da suka musulunta sunfika agun Allah"

.tsawa ya doka Masa yace " wallahi Karya ne Arne ko ya zama limami ni bazai fini agun Allah ba, nida musulunci ya haifeni na tashi cikinsa kuma ace wani Katon kafiri yafini ya fini, nasan Akan wanan banzan yarinyar kake magana ko kanaso kace ta..............

Shima tsawar ya doka Masa " karka kuskura ka zagi annah wallahil azemm kayi wnaan kuskuren zakasha mamaki, baba Zan Kira na sanar Masa da Komi, kuma try me and see"

Ficewa yayai Yana huci Yana cewa " u want to black mail me ko"

Ransa ya baci sosai, shikam yaya zaiyi da yareema ne?.

Ahankali Zaid suka fara dinkewa da AZARA wacce ta baje kolinta, tabbas AZARA itace macen sayaji ya taba sonta da gaske, yanaji Zia iya rayuwar ma da ita, ta zame Masa jiki, AZARA irin matan nanne da suka San kan maza kuma suke sace zuciyarsu, kominsu yazo Dede Kama daga girman shaawarsu da kuma halayya, ya rufe Mata koshi wanene.

Ta zame Masa tamkar Mata, daga baya ma gidanta ya koma ya bar wa zayyan gidan gaba daya shima sai ya hakura ya zuba Masa idanu Amma zuciyarsa cike da Yi Masa aduar neman shiriya.

Toh fa ga AZARA ta Fado cikin majigin kallon namu ko da me tazo kuma??

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now