SADAUKARWA

457 60 5
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi na arbain da Daya*

Washegari da safe suka gama shirinsu, tsab duk convoy dinsa sun hadu, gidan maimartaba suka nufa, waziri da zayyan tun safiya suka Dira a gidan, duk dai daukacin gidan sun taru, sun shigo sun gaggaisa a tsatstsaye,

Dubamsu yayi idanunsa rufe dn ya tsanesu kaf! Yanaji zai iya cinna musu wuta duk su mutu a huta ko yayi hakan kuma yanaji bai rama kwatankwacin cutar da sukayi masa ba.

" thank you for all what you have done to my daughter , please name any price for what you have done to her, shelter, clohthings, food and more we are ready to pay back and go with our daughter, so name any price"

Ran maimartaba ya baci, ya mike shima agabansa ya dubeshi yace " we did it not because of money ann is our daughter with or without you so please we don't want ur money for what we did for the sake of Allah"

Aiko de paa ya kufula dama a wuya yake nan ya fara masifa " owo owo is it why turn my daughter to Muslim, is this your plan? Let me tell u dis will Neva work , I reject it in d name of Jesus"

Shima sarkin harzukowa ya somayi seda aka shiga tsanani, Mai shela ne yake maidawa yan falon wanda basuji zancen ba dn rashin iya turanci, Rahmatullah itade se kuka, wani Dan brief case ya bude ya debo dalolin amurka ya watsa a fuskar  maimartaba da waziri dan tasabar wulakanci acewarsa ya biyasu ladan rike diyarsa,

Ya juya ya kamo hanunta ya na janta, zasu fice daga falon kowa yagama sarewa, da lamarin, yau kowa ya San Rahmatullah idan ta tafi ta tafi kenan, yareema  dake gefe ya rufe idanunsa yana sauke numfashi me dadi najin samu nasara, se me?

Suna is a bakin kofa rahma  ta turje taja ta tsaya cak father ya jata ta turje, ya juyo ya dubeta sosai,yanaso ya gaskata abinda yake shirin faruwa, ta zare hanunta daga cikin nasa tana komawa da baya da baya, tana girgiza kanta, tana kwallah, daidai tsakiyar falon ta dubi maimartaba da wazirin, Wasu manya manyan jigogine na  rayuwarta gaba Daya, ya zata manta halarcinsu akan wani dadin na zuciyarta ta tafi ta barsu, ta tafi tabi makiya Allah duk da iyayenta ne, duk da tana sonsu, tana jinsu a ranta, amma hakan bazai hanata sonsu fiye da ALLAH ba, ubangijinta shiya cancanci tasoshi fiye da Komi, tasani sarai idan Tayi kuskuren binsu lallai sede Tayi RIDDAH itakuwa Allah ya tsareta, gwara ta rungumi kaddarar auren yareema  ta rayu cikin MUSULUNCI, ya zame mata TAMBARI dukkan rayuwarta, wanan shine hukunci mafi wahala data daukarwa kanta, hukunci mafi zafi hukuncin dabatasan wace kaddara zai saukarwa rayuwarta ba!

" daddy this is were I belong to, these people are part of my life and Islam is my identity, I want to live with this people for the rest of my life, and beside I can't go any where with out my husbands permission "

Zaro idanu father da yareema sukayi dn sunfi kowa shiga tashin hankali, sumane kadai basuyi ba, father baya bukatan wani Karin bayani, cikin tsanar da baitabaji yana yiwa wani dan Adam ba ya dubeta yace " you will regret dis for the rest of your life, from today hence forth u are not my daughter I have denounced you, I have disowned you"

Ya kalli maimartaba yace " and dis is a war!

Ya kada iyalansa suna kuka suka fice.   Rahmatullah  ta zube agurin tana kuka, taruwa akayi akanata ana tayata kukan, waziri  ne  ya riko hanunta yana cewa " sannu h
Rahmatullah, sannu diya ta kincika musulmar kwarai Allah ya dawwamar dake cikin haske musulunci, idanu ta dago tace " baba wazirina shin na kyauta abinda nayi kuwa? Shin na zama cikakkiyar musuluma yau kamar Ku? Bazaa sake kirana da tubabbiya ba ko? " wani kuka yaci karfinta, kowa agurin ya tayata kuka, waziri ya rumgumeta tamkar uba yana shafa kanta yace " kin kyauta annata, Allah miki albarka"

Ta goge kwallarta ta dubi Maimartaba tace " daddy na amince da zabinka kuma bazan taba baka kunya ba insha Allahu, zanyi zaman aure nayi biyyayya ga mijina kuma dan uwana, daddy daga yau nazamo abin ikonka nazamo diyarka ta har abada"

Kabarbari Gurin ya dauka, duk wani me imani imaninsa ya dadu ya kuma karu, girman Allah da mu'ujizarsa sun wuce wasa!

Wani farin jini da daukaka Rahmatullah ta kara samu a idanun kowa, murna Gurin maimartaba da waziri kam baa cewa komi kowa alfahari yakeyi da Ita.

Se gabanin yamma komi ya lafa, kowa nan nan yakeyi da Ita, a dakin haj Rahmatullah ta na kwance kan cinyarta tana kara mata nasihar rayuwar , da kuma jaddada mata nauyin aure dake kanta, da biyayyar mijinta, tsaf Rahmatullah take nade abubuwan da take fada mata, zuciyarta cike take da taraddadin yadda zasu kaya da yareema, amma ta kudurce zata dauki duk wata tijara tasa akan aure. Nan dn tasan domin Allah takeyi agurinsa take Neman lada.

Sakon yarema ne yashigo yana nemanta a dakinsa, ta dubi hajj tace "ya yareema ne wai yake nemana"

Yadda ta rude yasa haj ta rikota tana cewa " ji shashasha duk kin wani birkice sekace kinga zaki, ke damarewa zakiyi fa ki nuna masa bakyajin tsoronsa, in ba haka ba zaidu wahalar dake zaiyi, kuma ki nuna masa kema mace CE mai yanci saboda haka ki natsu kije ki sameshi ayita ta kare."

Mikewa Tayi cike da kwarin guiwar tunkararsa, a falonsa ta same shi kansa a sunkuye, tana shigowa ya dago kansa, idanunsa tagani kamar na mayunwacin zaki, tuni cikinta ya bada kulululu ya mike zai nufota ta fara ja da baya, yau alurar sojojinsa ta motsa fa, ya birkice ya koma wani karamin ifiritu, kafin ta FIta ya Dakota wuf, ta fado jikinsa, idanunsa ya zuba a NATA  ya matso habarta kamar zai karya mata kasusuwan bakinta, da wata kakkausar murya yace " INA mai sanar dake cewa kinyi babban kuskuren k'in bin iyayenki da Kuma amincewa da aure na Rahmatullah, kinyi kuskure"

Tuni kwallah ta wanke mata fuska tanason bashi amsa amma ya murde mata bakinta,  kici kicin kwacewa ta soma, ya saki bakinta amma ya damko tudun gashin kanta tartare da hijabinta, ta yi wata karar Azaba  yau tana ganin ukuba,

Baki na rawa tace " ya yareem zafi dn Allah ka sakemin gashina" Dada damke gashin yayi yadda zataji zafin sosai yayi wata shuumar dariya kafin yace " wanan kadan ne daga cikin irin naui na azaba Dana tanadar miki acikin zaman auren mu, zaki gwammace kidi da karatu rahma, ni saraki sai nai ajalinki"

Ya hankadata ta fadi can waje ya jawo koafarsa ya barta nan kanta na Sarawa dn ta bugu acikin balcony........wanan itace rayuwar, wanan shine mafarin kaddararsu su ukun, wanan shine ZARE NA BIYU na FARKON labarin.....

Karku gaji Dani dai zamu tsallaka tsakiyar labarin

Wani abin mamaki ke shin faruwa, ku rike zaren labaran gaba Daya zamuzo mu hadesu, I love it when I twist za story....

Muje zuwa wai mahaukaci ya hau Kira........,.....................




ZAREN TSAKIYAR LABARIN

*********************************************************"*********

Wani daga cikin su ya saitashi da wata katuwar bindiga, dai dai kokon kansa,  yace  " kayi kalmarka ta karshe d'agutu"

Rufe idanunsa yayi yana tunano duk wata tsiya da sabon Allah Daya tabayi, yana Neman gafarar ubangijinsa dn yasan yau tashi ta kare, istigfari yakeyi, sai ta fado masa tuni ya shiga tashin hankali, zai mutu da hakki babba akansa, hakkin dayasan ko ya mutu ba yafe masa zata yi ba, nadama tazo masa karara, amma lokaci ya kure, salati yayi tare da karajin SHAHADA, ji kakeyi tau tau! Karar bindigar ta karade busashen jejin, kabbara suka yi , daya n yace " Sauri ka tube mana kayan jikinsa zasuyi mana amfani"

Haka suka tubeshi suka kwashe wayoyinsa, da duk wani Abu me amfani rufin asirinsa Daya yana saye da Yar singileti da gajeren wando, suka barshi nan a jefe gawa murus!

Toh fa twist twist kenan

Waye wanan Kuma? Shin INA labarin ya dosa?

Kada ku gundura!

SADAUKARWAМесто, где живут истории. Откройте их для себя