SADAUKARWA

469 68 2
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi na talatin da takwas*

Ganin yanda Ann ta tare gidan waziri, ya sanya maimartaba jin anya yayi mata adalci, bayajin Tayi naam da abinda yayi mata, toh yaya zaiyi? Nan ya tuhumi kansa da tsantsan SON KAI! Soyayyar zaidu ta rufe masa idanu, burinsa dansa koda gurbataccene ya hadashi da Abu mai kyau mai tsafta, Wanda zasu gauraya su bada ko su fidda Abu mai kyau, yana tunanine kan tsatson yareema din, bayajin duk duniya akwai macen data dace da zaidu irin Rahmatullah, amma Abu dayane bazai iya ba shine tursasawa mata zama da Zaid, wanan shine tunaninsa.

A gefen waziri adua yakeyi tukuru kan wanan abin dn ya gama sallamawa hadin auren nan kadai ya isa ya sanya mutum tsoron Allah in ba Allah ba waya isa wanan abin?
Fatansa daya Allah yasa Alheri ne garesu baki daya, yanda zayyan yaketa dauriya da kokari ya sanya waziri din jinjina masa da sake karfafa masa guiwa kan abinda yakeyi.

********************************************

A dakin mamma ta tusa zaidu Agaba  da koke koke zuciyarsa cike take da kunci marar misali wai duk akan annah yashiga wanan halin? Lallai ko in haka ne rahmatullah zata dandana kudarta a hanunsa, seta gwammace kida da karatu, dakanta zata nemi ya sawwake mata zai dafata ya gasa ta ya dumamata ta ruwan sanyi, amma yanajin zai mata alfarma daya, tunda yaji maimartaba yace aurensu bazai rabu ba sai de har in itace tace bataso zai lallabata ta CE batasonsa duk su huta.

Ya dawo daga dogon mukabalar da sukayi da zuciyarsa, ya dafa mamma ya CE mata " ni mamma banga dalilin kukan nan naki ba inde ba damuwa kikeso ki karamin ba"

Ta sharbe majinar data zubo mata wace ta gauraya da kwallar idanunta ta CE
" ai dole nayi kuka an cutar min dakai, kuma kai ko ajikinka"

Ya runtse idanu wai ko ajikinsa? Datasan a binda yake ji bazata CE haka ba, ita akan wani son zuciya tata ta daban take bori, shikuwa gaskiyar zuciyarsa CE ta ke nukurkusarsa bai taba son annah  ba bai tabajin yana sonta ba koda wasa, kuma duk jarabarsa bai taba sakata aransa ba duk da yasan ta hadu amma bai taba kissimata ba sai hana rantsuwa sau guda lokacin aurenta da sadik dasuka zo suka hadu da kawarta yakura dinan shima daga nan ya kwabi kansa, ga uwa uba yaki jinin Christian wallahi kyamarsu yakeyi komin tsaftarsu kai kko sun musulunta bai sonsu shi, kuma ace wai itace matarsa ta har abada, ai yanaga shine yakamata yayi kuka, ba amaryaba ko waninsa.

Yake yayi yace " ki dena kukan toh zan San abinda zanyi kinji Mamana"

Ta dubeshi alamun da gaske kake?

Ya gyada kansa " karki damu zan yi iya kokarina tunda kema bakyaso ki kwantar da hankali ki"

A dakinsa tunani ya fado masa, ya rarumi wayarsa ire iren sakkonin monifa ne da suke ta tururuwar shigowa wayar sa yaja tsaki, tun randa aka daura masa aure ya yi sallama da kwanciyar hankali, monifae da iyayenta sunyi hauka har sun gaji ,shiyanzu bai Masan da wane ido zaiga major aremu ba,zaidawo ta Kansu ne inya gama da nan, bazai bari Hutu ya kare ba bai gama da komi ba.

Lambar  zayyan ya lalubo ya kira bugu daya ya dauka cikin zolaya yace " ango kasha kamshi, duk angoncinne ya sanya ka buya, toh idan aka kawo maka Kanwar tawa kam sede mu dena ganinka"

Wani takaici ya turnike shi da kyar ya hadiye damuwarsa ya CE " toh dan iska banson sharri, kaida ka gujeni kiri kiri mezaka cemin"

Jikin zayyan ya dan sanyaya tabas ya dan jima rabonsa dashi

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now