SADAUKARWA

471 70 1
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na hamsin da takwas*



Ina godiya gareki antyna Rahma Nahaja me zance dake? Da bazarki nake taka rawa wallahi, na karbu a duniyar online writing ta sanadiyarki, sakona ya isa ga alumma dalilinki, kuma mata bila adadin sun karu da duk darusana wanan shine abin farinciki kuma burina, INA fata Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani dukkanin matan duniya, na tashi ranar lahira INA alfahari da duk abin da na rubuta, nayi alfahari da baiwar da Allah ya bani ta Isar da sako through hanyar rubuta, kin sanya tsohon mafarkina zama gaskiya, Allah ya sa aljannace makomarki kawai shine aduata gareki.

Gareku duk masoya  wanan novel Allah ya muku albarka, ya rufa mana asiri, ya cire duk wani me kunci cikin kunci, yasanya alkalamina nema muku mafita, INA SONKU domin ALLAH..

*******************************************"

Idan ya biyewa sn ransa zai iya fursuna dn bayajin zai iya kyalesu da ransu, amma idan ya tafi ya barsu haka sun cuceshi, wata zuciyar tace " kaima ai mazinacin ne ko? Meye najin bacin rai kuma kasan zinar kukayi ai har ka aurota yo meye abin jin haushin kuma?

Nan yaji kamar ya kashe kansa, Ashe haka abin yake da ciwo, ciwo mai radadi da kunar gaske, rabarsu yayi yayi ya shige, ciki ya kwashi duk wani Abu mai muhimmanci, ya hada jakarsa baijin ma zai iya kwana a gidan koda kuwa Basa ciki, ficewa yayi, ta biyoshi da gudu tana kukan Neman yafiya , suari yakeyi kada ta cimmasa, dn zai iya tattaketa ya kashe ta, abakin kofa yasamu john ya bashi daman kwashe duk wani kaya dayake cikin gidan nan, ya bashi kyauta (nace yau zaid ne da yiwa Arne kyauta🤣🤣🤣).  Ya kuma bashi daman kulle gidan ya koma can bariki, daman yazo gama komi nasa ne na abuja din , kuma yasata Agaba su tafi, toh amma yanzu kam tafaru ta Kare, sunan abujan dinma bayason yajishi koda wasa. John ya gano yau dubun matar gidan ya cikane dama yanata fakarsu, yanzu ma aikensa Tayi ta shige da driver cikin gida, shima dabadan me amana bane da haka zatasashi cikin masifa, amma bai taba jin shaawar lalata da matar ogansa ba acewarsa tazamo the forbidden fruit gareshi.

Gidan zayyan yaje , yana ganinsa yasan ba lafiya, ragwaf ! Ya fada kan kujera yana maida numfashi sai a lokacin kwallah ta zubu masa, mai yasa Monifa zata masa haka? Bai gamata da kowa ba har cutarda mahaifinsa yayi akanta, ba abinda baiyi ba tasaka masa da haka, wace irin bukatartace baya biya. Mata, duk abinda taso shi yakeyi har Dan kora ruwan barasarnan ma ita ta kuma mai dashi ruwa  shine zasu kare a haka? Kai Allah wadan auren bariki!

Dafashi zayyan yayi cikin tashin hankali yana tambaya ko lafiya, har zaidu din yayi kuka toh wani babban lamari ne me tsoritarwa,

Cikin sheshsheka yace " na saki monifa zayyan"

" ya salam" zayyan din yace

" amanata taci zayyan, amanata taci wallahi da peter fa na kamasunturmi da tabarya, innalillahi wa inna ilaihi rajiun na shiga ukuna Allah na tuba Allah na tuba"

Seya fashe da kuka, zayyan ya rungumoshi cikin tausayawa, duk da halayensa yana mugun son zaid sonda bayaji gameda kowa banda annarsa, maganganu masu taushi yasoma yi masa " zaid kayi hakuri komi zai wuce,  ka kwantar da hankalinka dn Allah, Allah ne ya nuna maka tun yanzu dn yana kaunarka da bataje ta debo maka wani ciwo bama ta yaba maka ka cutar da matarka ta gida, dn haka ka godewa Allah tajecan da halinta dama tun farko na hanga maka hakan amma yanzu kam ai komi ya wuce tayiwa kanta"

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now