SADAUKARWA

526 59 3
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi na arbain da biyu*

Ruwa aka sheka a wanan dare kamar da bakin kwarya,  se gabanin asuba ruwan ya tsaya, sassayar iskar ta wadata ko ina,  korayen ganyayyaki sunyi shar! Yabanya de Tayi Kore shar shar abin gwanin ban shaawa, fararen shanaye kimanin 50 da tinkiyoyi da raguna se karnika ne guda uku , suketa shawagi agurin , haushin da karnukan suke Tayi ne ya fargar da mutumin da suke kiwo da Yar diyarsa, da basu kula ba seda yarinyar taji abin yayi yawa, ta kwasa da gudu Tayi gurinsu, rike da Yar sandarta da abin busarta, ciyawu sun lullube wani Abu kaman mushe, a hankali ta tattaka ta isa gurin ihun data sanya ne ya sanya mahaifinta bin bayanta aguje yana kiran sunanta " BEEBAH" nuna masa abinda tagani Tayi, yaja ya tsaya turus! Seda yayi namijin kokari ya durkusa ya duba da kyau mutum ne! Ya dubeta yace " kai beeba mutum CE fa"

Ya dagoshi da kyar dn yayi nauyi, jinin dake fita daga goshinsa bai daine zuba ba duk ya malale gurin, ya sanya hanunsa kan kirjinsa yaji zuciyarsa na bugu, wanan shine ikon Allah, da sauri yace mata ta fillanci " da ransa"

Wani mikin ya sake hangowa na harbi a kafarsa, shikam jinin ya bushe, da Sauri ya umarceta data jawo jakarsu guda Daya takuwa jawota jiki na rawa, ya daura mutumin , ya kada jakar, yace maza suyi gida.

Rugar tasu batada girma amma sunada dan yawa dn har ARDO sunada shi, wato sarki ko dagaci zance, bai zame ko INA ba sai gida, matarsa dage yin fura ta hangosu sun dawo cikin yare tace " buba yau har kun dawo lafiya kuwa"

Nuna mata majinyacin yayi, ta taho da hanzarinta suka ciccibeshi suka kwantar a cikin wata bukka, tattaro kayan aikinsa yayi na magunguna kasancewarsa sarkin maganin rugar wanda akeji dashi, yasan kan magani, nan take Yakama aikinsa, yafi awa shida yana Abu Daya, da kyar ya fitar da alburushin dayake kansa, Dana kafar na kan nasa bai nutsa ciki sosai ba, ya cike gurin da wani magani ya manne gurin da tsumma mai kyau, shine iya abinda zai iya daganan kuma ya soma fatan samun lafiyarsa ya farfado.

Seda ya fito suke jajantawa da matarsa inna wuro cikin tausayawa tace " ayya wanan ko daga INA yake? Ko suwaye suka masa wanan muguntar?

Buba ya dan gyara zamansa yana cemata " ai yasha harbi kam Allah ma yasa alburushin bai shige masa kwakwalwa ba , yanzuma INA tsoro kada jini ya shiga cikin jijiyoyin kan nasa"

Tace "ameen" nan suka gama jimami, Sanan ya fice dn zuwa sanar da ardo.

Beeba ta zubawa wanan mutumin idanunta kyawawa tana fatan Allah ya bashi lafya, haka kawai taji tana tausaya mishi gashi kyakkyawa dashi ko meya faru dashi se Allah.....

Allah sarki beebah Ashe ba tasan tana kallon tata kaddarar bane ajikin wanan bawan Allah, ba tasan Allah ya hada kaddararsu ba kaddara mafi girma a rayuwarta da rayuwarsa me cike da ban mamaki da rabo mai karfi, kaddarar dazatayi sanadin rayuwar Wasu!


Rugar ardo ruga ce data jima agabashin kasar najeriya, rugace wacce takeda tarihi me yawa kqma daga kan ardo na farko har zuwa kan wanan Daya zamo na sha hudu cif cif, batada wani girma ainun se de tanada mutanenta dayawa kuma masu dimbin dabbobi, tsakaninsu da bodar nijar babu nisa zaace ma sune kan iyaka, GARGAJIYA shine abinda sukafi bawa muhimmanci sosai,  gasu dai da suna musulmi amma banajin akwai wanda ya iya cikakkakiyar sallah, bama wanda ya gama sanin Allah acikinsu, sunada surkulle na magunguna da asirai na kariya harda cutarwa, rugarsu bata taba shiguwa ba ga barawo dn sunyiwani. Abinda ake kira KAFI a garin. Shiyasa duk wani hargitsi bai taba hawo musu ba sede ko in an  bar nahiyarsu ya riskeka can.

Buba yanadaga cikin wadanda ake ji dasu a matsayinsa na sarki magani duk wata cuta shine maganinta da ikon Allah shiyasa yayi fice yakuma yi suna, har nijar da kewayen najeriya yana shiga, ya warkar da bila adadin, wani abin mamakin shine diyarsa Daya JAL a duniya sunanta BEEBAH, yanaji da Ita tamkar tsoka Daya a miya, yanaji yanason beebah kamar fiye da kansa, aduk magungunan dayake bawa mutane na haihuwa Allah baisa shi ya samu haihuwar ba dukda yadda ake dacen magungunansa hakan yasa ya zubawa sarautar Allah idanu ya rungumi Yar Daya dayar diyarsa, yanada burirrika akanta kasancewa ita kadaice, yanada burin ganin diyarsa ta gajeshi ta shahara Tayi suna a duniya fiye dashi shiyasa duk abinda yakeyi tana biye dashi tana kallo, cikin ikon Allah kuwa ta hardace komi har ya zamo itama ta fara shahara dn ma tanada mugun tsoro da abin NATA ya kere hakan.

BEEBAH yarinyace kyakkyawa kyaun da rubutu bai iya fasaltashi tanada kyau sosai kyau me ruda kowane irin namiji, Allah ya mata kira kamar ita tace ayi mata hakanan,  idanunta da dogon hancinta su sukafi kayata Yar fuskarta me haske, dan bakinta kamar tsagar reza, doguwace zar! Ga kira mai ban shaawa, yarinya CE me wayo da fasaha da iya kalami, maza na ruruwar sonta harda dan megari sede kash! Beebah bata tanajin wani Abu me suna SO ba, hasali ma tana gwada kanta da maza ne saboda yadda mahaifinta ya dorata bisa kan turbarsa, inka dauke tsoro datake dashi sauran ayyukamta duk irin na maza ne, hakan ya karawa mahaifinta kaimi wajen Dada dorata bisa turba, shekarunta na haihuwa zasu kai sha biyar , amma ko da wasa batason maganar aure inda saanunta ma sun hahhaifu ita tana gida, idan mahaifiyarta na korafi buba yakance " ayya inna wuro lokacin beebah baiyi bane zata yi auren ai, aure ma na alfarma birni zan. Kaita ta zauna da mijin"

Tun tana korafi har ta gaji tasa masa idanu.

Bayani yayiwa ardo harya fahimta, amma kuma ya gargadeshi kan kada ya jawo musu musiba suna zaune lafiya a rugarsu,  

Ya dawo gida ya samu beebah ta saka majinyaci agaba tanata kallonsa ko kyaftawa bata yi, ya dan dungureta " beebah ho beebah kinsa mutum agaba kina kallo haka"?

Ta dan sunjuyar dakai alamun kunya , dn bata Masan ya iso, ta zubawa bakon nan idanu tanata kallonsa kuma idan an tsareta bata Masan me zatace take kallo ba, tausyinsa takeji kawai tasan yanzu yan uwansa suna ta nemansa, ko yaya zasuji in basu sameshi ba?

Gaida mahaifinta NATA Tayi ta fice daga Yar bukkar , yan mintuna ta dawo dauke da abincinsa, ta zauna tasashi agaba kuwa sunata hirar majinyacin, madara ya umarceta data kawo , ya bude bakin sa yana. Zuba masa a hankali yake wucewa ta makoshinsa, ya sha kadan yace ta lullubeshi dn sanyi, a takaice de beebah kwana Tayi tangararas agurin nan tana jinyar sa, dama kuma dakinta ne ba Inda zataje ta kwana din.

Da sassafe ta tattara dabbobinsu suka fita, sede tunda suka fita bawon Allahn nan yake mata gizo takasa samin sukuni, har seda  suka koma gidan, yauma ita ta sake kwana dashi ko motsawa baiyi ba. Haka beebah ta kasance seta kwana gunsa ta Kuma fita kiwo da safiya, har sati guda buba ya fara fidda rai gameda bakkon sa, rana ta bakwai ne ya yanke hukuncin zuwa gayawa ardo halin daake ciki in be tashi bs zai maidashi gurin Daya daukoshi.wala Allah yan uwansa suzo nemansa.

Da maraice ta shiga dakin, tana binsa da kallo kyau yake yi mata matuka kasumbar datake fito masa tayi luf luf a kumatunsa, kominsa mai kyau ne tasha ji ana cewa tana da kyau kuma itama tasan hakan Amma yau taga wanda yafita kyau, a hankali ta kai hanunta cikin tafin hanunsa ta gwada sai me ji Tayi ya rike hanunta gam! Tayi Tayi ta kwace ta kasa aikuwade ta takarkara ta kwallah ihu n kiraan BAFFA!

Beebah uwar tsoro...... Amma soyayyar bako zai maidata jaruma......

ZAREN labarin kenan

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now