SADAUKARWA

663 92 16
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Babi na tamanin*

GWAGWARMAYAR SO!

Da misalin karfe goma na Daren ranan juma'a jirginsu na Emirates ya tashi, dukkansu suna zaunane a bangaren na musamman da aka tanadawa manyan fasinjoji Wanda ake Kira da ( first class) wai fa amasu kudin ma sai an banbance Wanda suka fi wasu Kai duniya labari!

Ta runtse idanuwanta daidai tashi da daidaituwar jirgin nasu a sararin samaniya, maganar Dan tsohon Nan Tana Mata yawo a ka, " Allah kiyaye hanya ammin harith, duk inda kike ki rike imaninki, tare da addininki, kada ki nawa shaidan kofar samu galaba akanki, wanan nasiha ce!"

Waye mutumin Nan?

Mai yasa takeji kamar tasanshi?

Meyasa takeji kaman tanada wani connection ( had'i dashi)
?

Mai yasa?

Daga karshe de zuciyar ta Bata amsa da "Babu Komi fa kece kike zafafa abin"

A haka wani barci yayi awon gaba da ita.

Bata farka ba sai gab da zasu sauka, daga taga take hango kayataccen garin na Abu Dhabi, ko Ina na walwali da kyalkyali, Mai ban mamaki, Bata sake tsinkewa ba da lamarin kasar Saida suka sauka, taga abubuwan mamaki , ta tuna wani malaminsu dayace shekaru goma da doriya da suka wuce kasar Dubai ta kaiwa kasarta najeriya tayin hadin guiwa kqn lamuran kasuwanci da harkar bude Ido, najeriya ta fututtuke Taki amsar tayi, yau ga karamar kasa kamar Dubai ta d'ara kasarta ta nunkata sau malala gashin tunkiya ta cewar Yara.

A wani apartment suka sauka, Mai dauke da d'akunan barci biyar, da Katon falo, da kitchen da gurin cin abinci, gurin dai gidane Mai zaman kansa, kuma sunada yawa Dan Hawa Hawa ne kamar guda 10.

Wanka tayi tayi sallar asubahi, ta koma ta kwanta yaran kam sun tafi can gurin su Uncle Ben.

Nne ne ta tasheta da kyakkyawan Karin kummalo Akan gado wand bature ke Kira da breakfast in bed, da kyayyawan murmushi ta ajiye babban tray Wanda ya kunshi lafiyayya shayin larabawa da burodin khubs, da kuma miyar kaza dage dagen larabawa, ga kuma kayan marmari dangin inabi Danye, da tufa, sai kuma Madara lafiyayya Mai sanyi labban, ta shafo kanta " hey princess wake up ND eat ur breakfast"

Yana Dan murmushi ta tashi itama, ta rungumeta Tana matagodiya, wanko bakinta tayi sanan ta Soma cin abincin suna irin ta Diya da uwarta ba kowa bane yake gane irin wanan hirar sai uwar da diyartata, taci sosai, ta koshi, Sanan tayi wanka, ta fara neman yaran Nne Tace Mata sun fita, ita ta shirya su Yi fitar Mata ita da precious tunda maza sun hade kansu sun fice.

A gurguje ta shirya cikin wata abaya doguwa, ta yane kanta da wani Dan karamin gyale, ita da kanta data kqlli madubi Saida tajika kamar ba ita ba, ita da Bata iya fita Saida hijabi dogo kuma ko abayar ne ba irin wanan take sawa ba, kuma Bata caba kwalliya dn tasan haramcin yin hakan a matsayinta na musulma , wasu kartai suyitaganin kwalliyarka suna cutar mijinka, haka ta kada ta fice saboda shaidanin dayake dawainiya da ita bazai Bari ta gane Komi ba!( Dayawa Mata sunaga kamar rashin 'yanci ne ace kada suyi kwalliya su fita, ko kunsan abinda kwalliya da nuna tsaraici ya jawowa mata dayawa? Wanan shine babbar kofar bude Barnar zinace zinace da matan aure suka fada ciki a duniyar Nan tamu ta yanzu, ubangiji Allah ya karemu da karewarsa, ya kyautata Mana zukatanmu, ya kuma yafe Mana zunubanmu badon halinmu ba).

Yawonsu suka Sha, inda Nne ta zaga shahina gwalagwalai, ta debesu kamar babu gobe, harda zabban lu'lu da Marjan ta saya, ganin Ann din batasayi Komi ba yasa ta dauko wasu dalolin amurka masu ya ta Mika Mata Tace su sai abinda suke so, itakam batayi wata siyayya ba, precious ce ta zage, daga Nan wani Dan la cafe' suka biya cikin mall din suka zauna dn cin abinci, itakam rahma tunaninta na kan wata Yar kyakkyawar yarinya fara tas tas da ita, data zuba Mata idanu, itama Rahman kallonta takeyi cikin shauki, da wani irin Abu, kamar tasan Yar yarinyar Nan? A hankali yarinyar ta baro teburinda suke zaune ita da sauran Yara 'yan uwanta, ta falfalo aguje sai teburin su Ann, kan cinyar Ann din ta d'are damar, tasa hannu ta kamo fuskar Ann ta hada da nata goshinsu guri guda ta zuba Mata idanu, wnan wata d'abi'a ce ta  lil rahma Amma Idan tanason mutum ko tanaso ya so ta, ko kuma dai Idan zuciyarta tanason Abu, takanyi haka ko a Yar tsana a shago inta ganata, wani Abu rahma tagano acikin idanun Yar yarinyar Nan, da wuri ta Dan janye fuskarta dn kamar yareema take ganowa! Yau ita kuwa Mai ya kaita wnaan banzan tunanin? Yarinya Yar larabawa meya hadata da yareema, toh Amma Kota ki koya so wanan yarinyarn Tana masifar Kama da harith dinta, dubanta tayi ta rasa da wane yare zata muamalanceta.

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now