SADAUKARWA

512 79 3
                                    

[7/2, 4:41 PM] Gimbiya Maryam: ✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

         

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi na talatin na Arba'in*

Ina Mika jinjinata ga duk wani convert mace ko namiji, Allah ya Kara muku hakuri da juriya, ya kuma saukaka muku duk halin rayuwar da zaku tsinci kanku, wato irin kuncin da wadan da suka musulunta suke fuskanta abin a duba ne, a fara rubutun Nan naci Karo da wayoyi da messages na da damansu, suna Kara budemin irin halin da muke jefasu, da wahalhalun da suke Sha, dn Allah dn Allah mu Dena cutar dasu da harsunanmu, da dabiunmu da al'adarmu, dayawansu sun ce na Basu hope suna fatan ace kowa yazama kamar ni, nakance musu Nima din kokari kawai nakeyi ni kadai bazan iya gyara Komi ba.😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

Salallami yan gurin suka dauka, shikuma ya ratsa cikin falon yana Dan yake, Rahmatullah datake sharce kwalllah ta dago kanta, zuciyarta ta tsinke, tqbbas ko acikin duhu zata iya gane mahaifinta, tambayar kanta ta somayi, Ashe ba mutuwa sukayi ba? Toh ya basu taba zuwa gurinta ba?

Gaisuwar da sukeyi da kowa ne ta katseta, sun gaisa paa ya dubi maimartaba cikin harshen turanci yace " kungani sai yau , kun ganni da iyalaina bamu mutu ba, dama nazo wucewa ne nace Bari nazo na tambayeku ko Allah yasa kunsan inda aka wurgar da gawar diyata ko aka binne gawar"?

Kabbara Gurin ya dauka, cikin sanyin jiki  maimartaba ya kamo hanunsa ya tattaka dashi har gabanta, kallon kallo suka tsaya shida ita " wanan itace diyarka annah bata mutu ba, waziri ne ya ceto ta"

Durkushewa yayi agabanta yana kuka itama kukan takeyi ya tallabo fuskarta ya kura mata idanu ya shashshafatadn ya tabbatar ba mafarki bane, ya rungumota jikinsa yana wani kuka, nan iyalinsa suka rufu akansu suna koke koke, wanan shine ikon RABBI!

Sunsha koke kokensu,   daga bisani ya mike ya ya fara musu godiya da Kuma bada labarin duk abin da ya faru dasu da matsayinsa a yanzu, kowa ya alajabta abubuwan dasuka faru, shima su maimartaba sun masa bayanin komi, nan aka sake wani sabon labari, wayarsa CE ta katseshi, speaker ne yake kiransa ya kara wayar akunensa, sanar dashi yayi an dage taron su juyo saboda Wasu matsaloli Daya taso kawai su juyo.

Kowa ya natsa taro ya watse ya rage saura daidaikin iyalin gidan ana ta yaushe gamu ya nuna murnarsa na yadda aka rike masa diya, sede ko Daya bai kawowa kansa diyarsa zata zama musulmaa ba ya zaci tanakan addininta na kiristanci shi a tasa wautar!

Har masauki aka kaisu Rahmatullah na manne da mahaifanta, hakan ya sanya jikunan mutane yayi sanyi kawai sunsan yadda Rahmatullah take cikin rintsin rayuwar nan tohh fa ba makawa iyayenta zata bi bama wani tunani na biyu.

Acan sashen mamma suna zaune da diyanta murna duk ta cikata,tasan ba makawa anna bin iyayenta zata yi yareema zaidu yafi kowa murna, yasan karshen abin yazo, har dariya yakeyiwa Mai martaba yana cewa " yanzu kam baba se ya kwantar da hankalinsa tunda Yar gaban goshinsa zata tafi"

Mamma Tayi shewa " gayyar tsiya arna a Idi ba, aahaf dama fa musuluncin karyane  tanaganin arzikin ubanta dinan INA zata yarda ta zauna, amma fa naso da tsatson musulunci CE da sena baka baki Ku zauna kawai dn naga fada ya kudance"

Takaici ya ishi zaid Sam mamma batada tunani da focused na rayuwa. Ana gafara sa ita batamaga kahon ba, wayake zancen wata dukiya yanzu? Ana maganar shi baison ta Ita tana kawo wata maganar ta daban.

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now