SADAUKARWA

606 103 27
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Babi na saba'in da tara*

GWAGWARMAYAR SO!

Duk rayuwa Tana faruwa da yadda Allah yaso, Komi rubutaccen daga lauhil mahfuz, mahluki Bai Isa canzashi ba kuma.

Yanzu ne yakejinsa sakayau, duk da tunaninta na addabarsa, Amma yau kuma sai azara ta Fado Masa, wallahi harga Allah ya mance da ita fa, koma meye azara masoyiyarsa ce ta hakika Wanda soyayyar da take Masa ya koma abinda ake Kira OBSESSION, sonda bakaji baka gani akansa, zaka iya komibakan son wanan abun.

Yana bukatar yaga azara dn itama kada ta kubce Masa, Abuja ya sake komawa, saide amsar data tarar ta kadashi! Mai gadin gidan ya tabbatar AZARA sun bar kasar, tun shekaru hudu da suka wuce, agurin ya tsuguna Yana kuka Yana cewa Allah na tuba, Allah ka yafemin, Allah kada ka barni da halina.

Haka ya dawo guiwa a sage, Koda Wasa yakasa jin labarin rahma bare yasan inda take, gga kuma azaran ma wai Bata kasar kuma baasan ma kasar dasuka koma ba,  ya Kira abokinsa kuma amininsa dn ya samu saukin damuwarsa Amma me? Shima shiru, ya bincika gurin aikinsa ance ya tafi secret mission da baa bawa kowa damar sanin takamaimain aikin ba, kuma andora da ce Masa aikine Mai mugun hadari, tun daganan ya sallama, baida kowa a duniya! Maimartaba ya barshi lokacin dayake tsananin bukatarsa, hajjo ta barshi itama, beebarsa itama batanan, wa zai gani yaji sanyi, Ina zai duba yaga haske?? Zuciyarsa ta bashi amsa da ka koma gida zaka samu sassauci.

**************************************************************

Aduk tarihin masarautar baa taba katari da masifa da tashin hankali ba irin wanan lokacin, karagar mulki Tana ajiye Babu kowa bisa kanta, basuda shugaba, tun ana ganin abin zai wuce har yazo ya zama wani Abu daban, mamma ta hura musu wuta saidai a damaka mata mulki tunda dai danta shine magaji, tunda baya Nan se abata ta rike kafin ya dawo, wasu kuwa sun biyewa shashancinta, t da ZALZALU yayi Mata zafafan ayyuka Wanda zai Sanya bakin mutane yayi shiru , saide waziri da wasu jiga jigai su suke Bata wahala sunki for su amince Kuma kusan sune majalisar dattawa ( king makers) da zasu yanke hukunci na karshe, wanan na Bata haushi, ta kuma kuduri aniyar saita raba waziri da duniyar tunda yaki bada hadin Kai, kowa ya gane t haukace kan mulkin Nan, tare da taimakon Yan uwanta hakan ke Dada assassa.

Dirar magriba yayiwa gari sai yaga garin duk wani iri kamar ba wanan annuri da hasken da garin ke dauke dashi, duk inda ya wuce jiniya ke tashi , Yana kuma tuna yarintarsu, wani guri yayai murmushi wani yai kuka, wani Yar dariya, har ya Isa gida Kai tsaye fadar y nufa, jin zuwansa yasa mutane suka taru suna son barka ko ba Komi rigima zata Kare kwana kusa.

Da kyar ya samu ya Shiga gidan , sashen umma ya Soma zuwa, yanajin itace uwa tagari, uwa mabada mama, wacce zai Sanya kansa a kafadarta yayi kuka komin girmansa , shigowarsa yasa kowa ficewa daga sashen bayan gaisuwa da suka Masa, Tana lazimi, gabanta yaje ya tsuguna, ya Sanya kuka, ya Dora kansa kan cinyarta, wanan shi kadai yake bukata a yanzu, hannu ta Dora bisa kansa ta cire hular sojojin, tasoma shafa lallausar sumarsa , tana Dan bubbuga kan a hankali, wnaan shine abinda take Masa lokuta da dama Idan tashiga damuwa ko Yana kuka tun Yana yaro, kuka yayi Mai isarsa har Saida Tace mace " ya Isa hakanan SARAKI , ya Isa Dana, ya Isa gudan jinina, ya Isa babana, ya Isa, sarkin gobe"

" Ya Isa Dan HARITHA baban sarki, ya Isa Dan ummansa"

Hanunata ya k'ank'ame sosai, Yana Dan maida ajiyar zuciya. Yace " umma kimin adua"

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now