SADAUKARWA

492 66 1
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi na saba'in da hudu*

My sweet wattpadians, wanan shafinku ne wallah, kuyi yadda kukaso dashi.

**********************

Wai wasa farin girki, rahma bata raina kanta ba saida taga an jefasu su a wani shegen cell , yunwa kishirwasun addabeta matuka , yaran ma haka duk sun jigata, meeting akashiga akanta na musamman, tana lallaba yaran ne lokacin sallah yayi babu zancen tace zatayi alwala , nan ta bubbugi gini Tayi tayyamum( taimama), Tayi sallah dukkan yaran sai sukayi yadda Tayi, sukayi sallah, jeruwa duk akayi ana kallonsu, wani daga cikin su ne yake cewa cikin harshen turancin broken " dis woman get strong head, even for here she dey pray?

Daga gefe wani yace " wonders shall neva end woo"

Fitowan babbansu ne ya sanya su yin shiru, ya dubi inda take da yara, duk saiyaji tausayinta cikin ikon Allah, shi ba musulmi bane bai kuma son musulunci amma yana gani wanan matar she is innocent, ya umarci abata ruwa da abinci kafin sugama ya ke hukunci akanta har yanzu ana dudduba kayyyakintame ko zaa samu wani exhibit.

Sai gabbanin magriba, yasa aka fito da ita da yaran sunata kuka su ta mayarsu gun babansu game din ya isa haka bazasuyi ba dn tace musu game ne sukeyi na adventure,

A tsanake ya soma tambayarta meya fito da ita, a tsanake ta larabta masa ko ita wacece, yasha mamaki, kwanyarsa cike taf da tambayoyin ya akayi diyar father take musulunci?? Kai wanan Abu da alajabi, kuma ya lura zancenta ba kanzon kurege cikinsa, hasalima seda ya dubeta sosai yasan cewa tana matukar kama da mahaifinta, abin ya matukar bashi mamaki.

A take ya buga yace yanason ganin wani.

Bayan yan mintuna mutumin ya iso , a ofishin ya samesu, ya Dan dubeta a fissge ya zauna, ita kam tunda ya shigo ta ganeshi kasan cewarta marar mantuwa, kafin ma ya fara masa bayani ta katsesu

" uncle Ben!

Ben ya juyo yana dubanta sosai Kamar yasan yarinyar nan a wani guri,

Ta Dada narkewa cikin kwallah tace " ita me raham"

Yayi sororo kafin yace " rahma"

Tayi saurin cewa " Mary ann"

Ya mike kamar zararre yana cewa " Ann ! Mary ann! Is that you?

Ta gyada kai " yes uncle its me"

Komawa yayi ya zauna jagwaf ya dafe kansa, wanan Yar wansa ne wai, wai Mary ann tasu dasuka so, sukayi kewarta, Mary ann de da kullum rikici akeyi akan zuwa kwatota, an hada an shirya duk wani makirci na karbota jiran lokaci akeyi se gashi ta kawokanta, shi yanzu murna zaiyi ko bakin ciki, father bazai taba Aminta da ita ba dn yayi disowining dinta, ko hura wutan kwatota dinma shi da yan uwansa ne acewarsu  " hanunka bazai rubeba ka yanke ka Yar"

Ai tasuce jininsu CE ko sunki ko sunso kumadolene su dauki mataki, duban abokin nasa yayi yace masa " can I go home with her asp?

Ya Dan tattaro hankalinsa ya kalli  Ben din kafin yace masa " yes that's why I called you, cause she is nt safe here, please do take care of her and her kids, they are all tired ,they need rest"

Mikewa yayi yana masa godiya, ya sanya ta agaba suka fice , folisawan NATA leke da zunde suna so su San wace CE ita har kanin sanata yazo daukarta, lallai akwai wani babban al'amari tare da wanan mata me shigar masquerade din sunan dasuka lakaba mata, da sun zaci isqkancin arewacin najeriyar ne ya iso su na abinda musulmai sukeyi na tada  bambamai da kunar bakin wake, da kashe kashe, basajin zasu dauki wanan renin hankalin, tsirarun musulmai da zama ya kawosu nan su suke ganin musiba sunajin gwara ma su koma arewa dn samun sukuni, anan sede kayi sallah a boye, zancen sa hijabi kuwa an ajiyeshi gefe banda wulakanci da barazana ba abinda suke fuskanta anan din, kila datasan da haka ma bazata zo ba.

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now