SADAUKARWA

432 61 3
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi na sittin da uku*

Wanan shafinku ne , Yan sadaukarwa group na watsapp

Kuyi yadda kukaso.

Muskutowa mamma Tayi tana mata rada cikin kunne kamar wata saarta tace " dama zan baki ki malleke min shi daganan semu juyashi son ranmu"

Wani garangatsau  taji abin, mallaka! Mallaka   mama? Ni kam ina tsoron zuwa gun boka , idan ma'a taji kasheni zatayi ai adai canza wani"

Mamma ta galla mata harara ganin yadda duk ta birkice " ke shasha dallah tsaya kiji waye miki zancen boka anan, aikin banza inason taimakonki kina butsarewa toh shikenan jeki ki yi tsimi da dabararki tunda kina ganin zaki iya, kinsan dai ni Yar uwar mahaifinki ne ko? Zan cutar dake ne? 

Ta dan mike a fusace, zata bar mata Gurin ,da dan saurinta ta rukota tace " ah ah haba mama kiyi hakuri dn Allah, kece kai na ya dawa fa, kinga ko maa bata bayana, dn Allah kiyi hakuri kawai de Inajin tsoro ne"

Ta dan dakata tayi nazarinta azara wawuyace gabuwar ire iren yan Fari, seta dan sassauto ta zauna ta dan tabe fuska tace " ah tohh ana ga sa kina bakiga kaho ba Yar nema, kin fini son danane aka fada miki?  Inasonsa sonda nake masa ne ma ya shafeki, Kuma tsanar wanan tubabbar ajinina take, inaso ta barmun da na Taje can ta karata mitsiyaciya, shine ke Kuma zaki bata abin"

" kideyi hakuri mama am, kanadi go ne inji mutan borno"

Ta dan murmusa " yawwa ko kefa Yar gari, yanzu in tambayeki wai a meduguri din baku da wasu magungunane na mata haka masu dauke hankalin namiji, tunda Naga mahaifiyarsu Yar can ce, takuma fi son Kuna bin al'adarta?

Kunya ta rufe  azara yau tanaganin surikar zamani, ya ilahi!

Cikin kunya tace " akwai mama amma maa ta hanani"

Ta dan dafata tace " bari dakaina zan nemo miki su daga nan se musan abinyi"

Godiya ta soma yi mata,

" Kuma duk abin da na   baki ki tabbata kinyi amfani, zankuma rika yi miki wani kokari a gefe daban , kede duk abinda kika gani ki kame bakinki"

Ta gyada kai kamar wata kadangaruwa " toh mama nagode Allah barmin ke".

Shewarsu Daya dan jiyo ne ta bashi mamaki, mamma da azara sun baro rahma tanata fama su suna nan su na shewa jikinsa ya bashi anya Alheri suke shiryawa kuwa.  Anan yayi jigum  tasomoshi taci ado da wata silk rigan bacci, fadowa kansa Tayi, ta jone fuskarsu guri guda tana masa wani irin Sumba na matan da suka jiku da boko, sosai yakejin abinda take masa kafin wani lokaci ya shagala ya tsimu, suka fada wata duniyar, bayan komi ya lafa ne yace mata " najiyoku kunata shewa keda mamma nace me kuka samu ne haka"

Dan murmushi tayi tace " Umm ba dole ba, toh ka mance dani kayi sabon da ai dole ne na kama masu sona"

Dariya ya danyi " azarah problem azarah!"

Tace " haka dama zakace ai nasani kulum nice problem"

Rukota yayi jikinsa sosai, yace " azara dn Allah kinaso na shiga wuta ne? Saunawa zan bayyana miki zuciyata game da rahma wai, dn bana sonta bashi bane zaisa na ki diyana , ko na shiga hakkinta, I think she deserves some respect ko?

Ta danyi Jim wani Abu na tsakurarta , amma tasan tada rigima ba NATA bane

Ya katseta

" Kuma I expect idan kina sona zakiso abinda na Haifa, abinda jinina ke yawo a jikinsa, abin alfaharina, amma ina ganin yadda kike shashshare yaran nan banajin dadi ko kadan sekace wasu kashi Dana naki ne ai inda so"

Dan tureshi Tayi daga jikinta tace " a'a wallahi diyan da zan Haifa de sune namu, NATA da akaci amanata aka haifesu NATA ne Kuma".....

Ya daga mata hannu " OK ya isa please!

Ya juya ya mike ya shiga wanka ya fito ya kwanta yaja bargo tanata fitinarta ita kadai har bacci ya kwasheshi.

Ita kam bataga ta bacci ba kulafucin furucinsa takeyi gareta tsabar wayo ta kasa gano kan zaidu din ko kadan, kishi ya rufe mata idanu bata iya ganin komi bata iya gane gaskiya da karya zuciyarta CE kawai take juyata haka ta kwana dn masifa idanu biyu.

Da safe ya tashi da abincin dada ya karya lafiyayyan dumamen tuwon gero da miyar kubewa danya, taji kifin mutan hadejia, ya kuma sha kunun kanwar mejego yanata Santi, dada Tayi amfani da wanan damar tamasa nasiha sosai ,abindayake bukata daga Gurin mamma kenan dn cinye kaddarorinsa, amma ina! Yayi godiya anan take CE masa " nanda sati zata juya"

Ya zaro idanu Yana cewa " a'a dada wanan wasa kikeyi, har yaushe kika gama wankan dannaki, gaskiya ki tsaya ki wankemin abokina tas a gasa min shi ehe!"

Ta dan harareahi cikin sigar wasa tace " dan kaniyarku ni banda mijine? Bazanje na kula dashi ba sena kare a gidinku"

Dariya sukayi daukkansu kafin rahma tace " ayya inna uncle zayyan dina fa"

Ta langabar dakai alamar  ban baki da shagwaba, sanyinta da rashin rigimarta suna birgeshi yanason mace me sanyi da rashin tsiwa sede kash yakasa jinta ne Sam a ransa!. Abin har tsoro yake bashi wallahi zuciyarsa wata irin banzar zuciya ce, Mai shegen kafiya.

Da kyar ya iya dauke idanunsa daga gareta dai sukayi sallama ya fita.

Daga fitansa dada ta dubeta tace " wato duk Abu na Allah shine dai dai, ki ga yanda zamanku ya mika haka, naje dadi da idanuwana suka ganemin haka, ki kara kama aurenki da daraja, ki bawa mijinki kulawa ta musamman, kuma ki kiyayi kishiyarkin nan da mahaifiyarsa dn naga sun hade kai, kuma adua itace takobin ko wace mace tagari kinji ko?

Ta gyada kanta itama tanajin lallai ta Dan samu gurbi de agun mijinta dn yana iya kokarinsa.

Kwanaki sun shude, zamansu da mamma na doya da manja ne lefinta ma ya shafi dada wacce batama shiga shirginsu, tana ganin yanda suke kanainaye yareeman duk Dan su rabashi dasu amma Sam baya iya ko rimtsawa idan baiga yaran nan nasa ba guda biyu ba sun zamo wani bqngare na rayuwarsa ma gaba Daya, haka har lokacin tafiyar dada tazo, maimartaba kuwa yace duk da mamma zasu taho haka ta tattara ta tafi.

Bayan kwanaki kadan mamma ta soma aikinta tana aikowa azara! Wanan shine mafarin hargitsewar zaman nasu.......

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now