SADAUKARWA

684 88 22
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na ishirin da biyar*

Innallaha lah yuhibbul mubazzarin


Cikin Kwana biyu ya shirya ya taho gida a kagauce, sede bayan ya iso kuma hankalinsa ya tashi, dn Bai ma San ta inda maimartaba zai saurareshi ba shekarunsa nawa rabonsa da gida?

Da wane Ido zai kallesu?

Gabansa ya Fadi lokacin daya tuna haj, rabuwarsu ta karshe, da abinda taga ya aikata, Koda zuwansa ya samu Babu kowa ma a gidan sai mamma wacce itama dawowarta kenan dn anyi Babu dadi da ita acan kano din kowa yayi Allah wadai da ita sai jahilai kalilan dasu daure zancenta a bakin katarar su, ko ba Komi ta ci riba da hakan dn ta san tabarwautane dayawa wanan Abu data kirkiro ta kakkabawa annah tayi alkawarin saita dai daita rayuwarta, tayi alkawarin sai musulunci ya gagari annah, tayi alkawarin seda nuna Mata baa Shiga gonarta a zauna lafiya yawan tsanar mutum aranta yawan tarin fitinar data tanadar Masa.

Shigowarsa ne ta katseta, dubansa tayi zuciyarta cike da murna Amma fuskarta kaman hadarin daya taso daga gabar yakeson zubda ruwa bayan anyi bakar guguwa, yasha jinin jikinsa tun kafin su gaisa ta mike zatayi ciki, da azmaa ya zube a kasa ya Kama kafafunta " maman je suis de'sole'e"

Ya rike kafarta Gam

Haushinsa takeji Amma ba yanda ta iya, tanaso saraki ya Bata hadin kai su mulki wanan daula Mai alkhairai dayawa Amma fir! Yaki yadda ya Kama wani shirmen banza! Tureshi tayi tasake azamar barin gurin ya Dada rarumota Yana cewa " Dan Allah mamma Dan Allah"

Shiru tayi kafin daga bisani ta dubeshi, sosai ya taba Mata zuciya balle da ma 'dan so! Ai dol ta huce ma Amma kuma Tana bukatar ja Masa kunne matuka, da dorashi bisa hanya wacce zata bille musu, saboda tasha wahala Akan sa, ita tasan gwagwarmayar datayi kafin tasamu cikinsa, har kuwa ta Yi gwagwarmayar maidashi SARAKI sarautar da sai mai jiran gadon ne ake damka Masa ita kuma sai ya Bata Mata lamura, akwai wani sirrrin da daga ita sai Allah suka sanshi saiko Wanda abin ya shafa sirrin da Idan duniya tasani ta kade, kuma Abu ne daya shafe shi shi SARAKI batasan iya tabka sab'on Allah manya manya datayi ba a dai kan rayuwarsa ta inganta, soyayyar mulki ya makantar da ita! Mamma irin matan Nan ne dake matukar son mulki Tana alfahari da mulki Tana kuma kaunarsa, ko Don cikinsa ta tashi ne?

Ko kuma de dama  haka nan jinin sarautar kan kaunaci mulki fiye da aljannarsu? Ko kuwa Daman haka suke tsoron rasa mulkin fiye da yadda suke tsoron Allah?
Kaiconmu Yan Adam da muke bautawa duniyarmu ba lahirar mu ba.

Guri ta nema suka zauna can kuryar daki, ta dubeshi a dake Tace " Zan yafe maka bisa sharadi guda!"

Ya dagota a kaugace yace " menene mamma ki fada min ko meye zanyi?

Ta danyi murmushi Tace " aure nakeso kayi"

Wani murmushine ya cika Masa fuskarsa

" Mamma Nima maganar danazo da ita kenan"

Nan ya Bata labarin Komi, takuma ji Dadi duk da de taso ya auri Yar gida Amma ko ba hakan ba gaba zata sanyashi ya auri Yar gidan tunda mulki zaiyi.

" Maimartaba fa?

Ya tambayeta se a lokacin Tace " Yana can kasar kano, anyi rasuwa"

Cikin damuwa yace " waye ya rasu?

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now