SADAUKARWA

462 81 5
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi na arbain da uku*

Wani irin ihu beebah take tsalawa saboda rikon dayayi mata kam kamar ze karya diyan yatsunta, baffan ne yashigo yaga halinda suke ciki, yayi iya kokarinsa ya banbare hanunsu Abu ya gagara, a hankali bakinsa ya fara motsi ya kuma fara kokarin motsawa da Kalmar shahada ya farka, se lokacin ya fara sakin hanunta a hankali, Tayi tsale ta koma bayan babanta ta tsaya tana haki kamar Wanda tasha gudun ceton rai!

Dushu dushu yake gani bai kuma iya tuna komi bare ya gane kowa, wani mashahurin ciwon kai yakeji, da kafarsa datayi tsami, se wash wash yake cewa, a hankali buba ya rankwafo yace " kayi a hankali jikinka akwai rauni me yawa, tayashi tasowa yayi yana ciza lebe na karbin hali, wasu irin zogi yakeji amma zogin da zuciyarsa takeyi yafi komi, a hankali ya furta " inaso nayi alwala zanyi sallah"

Ruwan ta kawo a kwarya ta ajiye masa, yasa hannu da kyar yqna shafa ruwan, suka zuba masa idanu, Rabon dasuyi wani Abu wai shi sallah sun mance hasali ma basu daukanta da muhimmanci kai banajin ma duk garin ansamu Wanda ya iya sallar bare karatun ta balle sanin hukunce hukuncenta, shi kansa baisan iya sallolin Daya sauke ba dn bai San iya adadin kwanankin dayayi a kwance ba, seda ya idar Dan kansa sanan yace musu " zansha ruwa"

Jikinta har rawa yakeyi ta dauka masa ruwa me sanyi a tulu,ya kafa kai ya shanye tas, aiko nan ya murdeshi dn cikinsa ba komi, kakarin amai ya soma kuma yaki Fita  dn komi a cikinsa , da sauri baffan ya dauko damammiyar fura dataji Zuma ya miko mmar nan yakama sha kamar mayunwacin zaki ya sami nama a dokar daji, yasha cikinsa yayi nak! Sanan ya jinjina jikin garun bukkar, yana maida numfashi, baffa ya zauna kusa dashi ya dafashi " kwana 14 da sunka wuce nassameka yashe bisa. Kasa an maka mummunan halbi, Daya ga kanka dayan ga kafafunka, na kawo gidana na kula da kai"

Ya dubeshi yana tuno meya faru dashi a karshe, bai iya hasko hoton komi, se Harbin da akayi mishi da Kalmar karshe dayayi.

Baffa yaci gaba " inane kasarka? Da garinku"?

Gabansa ya bada dam! Ya soma tambayar kansa " wanene ni? Daga INA nake meya kawoni ? Suwaye suka harbeni? Tambayoyine da baida amsoshinsu ko Daya, toh fa!

Wallahi ya kasa tuna komi nasa, lallai Dan Adam ba komi bane muna bata lokutanmu abanza muna fankama muna kababa muna jin mu wasu ne, rana Daya idan Allah yayi maka kqmun kazar kuku wallahi seka zamo abin tausayi.

Ganin ya kasa cewa komi Baffa ya CE " toh meye sunanka?

Nan ma de Jim yayi kafin yaji karfin guiwar CE musu " bansani ba wallahi na manta koni wanene?

Baffa ya dubi beeba suka maida idanunsu gareshi, Baffa ko tantama baiyiba kan sa ya tabu, dama tsiyar harbi a ka kenan se ya tabar da kwakwalwa.

A hankali ya fara warewa, beebah tafi kowa kula da lamarinsa safe da rana tana masa hidima, sun Sama masa suna "BAKO"

Shima dole ya karbi sabon sunansa, zuwa yanzu ya gane kowa na gidan musamman beebah, se Baffa da inna wuro. Jikinma a hankali ya soma warkewa Baffa yasashi gaba yana tattakawa, dn kafar ta ware.

Yau ma kamar kulum, Baffa ya samoshi a daki yana zaune jugum tunanine da tambayoyi birjik acikin kwakwalwarsa data hanashi amsarsu.

Baffa ya katseshi " kadi bako yau kam fita zamuyi kiyyo da kai, ka motsa kafafunka"

Ya mike ya jawo sandarsa yana cewa " toh Baffa muje"

Murmushi baffan yayi yana jinjina wa kokari irin nasa.

Tunda ya fito take kallonsa, harseda suka fice, ba shiri ta dauko sandarta, ta dauko mayafi tayi damara tamau,  da harshen fillanci inna wuro tace mace " hoi beebah kema zakijene?

Gyada kai kawi Tayi ta ruga da gudu ta bisu a baya tana ccewa " Baffa Ku jirani"

Tana haki ta cin masu, sukaci gaba da tafiya, suna tafiya Tana satar kallonsa, hira suke jefi jefi saboda banbancin hausarsu da kyar Bako yake ganewa, kiwo sukayi sosai, shikuma ya ga baiwarr ubangijinsa ta NATURE ko INA abin shaawa, kiyo sukayi sosai yakuma ji dadin fitar nan yayi alkawarin fita kiwo kulum Dan debe kewa.

Beebah Tana bashi mamakin yadda takeyin abubuwa tamkar na miji, su hawa bishiya kamar wata biranya,🤣🤣 da tsalle tsallen nan , bata dena bashi dariya da kuma mamaki mace ta maida kanta namiji.

Haka rayuwar tasa Tayi ta gudana, mutanen gari suka fara saninsa, sunan BAKO ya bishi, kiwo kuma ya fara zamowa wani bangare na rayuwarsa.........................

Mafi yawancin lokuta ka kan tsinci kanka cikin wata rayuwar da Allah ya zqba maka Baka da mafita illah kaima ka rumgumeta haka nan har Allah yayi yinsa....

Vote! Comment! Dn insan kuna jin dadin abin, nasan na kawo confusion amma zamu warware. Thinking thinking wasu na over thinking,😆😅, Niko Ina lafing, Zan kawo end of discussion...

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now