SADAUKARWA

647 95 22
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

              * Babin na saba'in da shida*

********************************************

Tsawar Daya doka musu tasanyasu tsayuwa, jikin ta yana bari , komawa ciki yayi , ya fito yana  sassarfa me zasu gani?

Wata katuwar hunters gun ne, bindiga dirkekekiya, ya saita Rahman da Ita yana cewa " I will shoot you if u dare step into my house" , bawasa kuma yake ba yadda ya saito ta din ya kuka  bindigar zai ja kunamar Harbin, da gudu maman ta tare Rahman tana cewa " sede ka kshemu tare" cikin harshen Igbo, aikuwa ya saki harsashin nan hqnunsa na rawa ya sake sakar wani, cikin tashin hankali  Ben ya hau sama da gudu suka kama kokawa, ya kwace bindigar, duk sun sadakar ya harbesu ita da mamarta, amma ihun yaran da su precious da Michael ne ya sanya suka San abin baa Kansu ya auku ba, 

Harith ne kwance cikin jini male male yanata jijjiga, Michael yayi kansa ya Ciro rigarsa ya danne inda jini ke zuba, Dede cikinsa, ihun kukansu ya ruda ko INA, rahma da gudu ta fada kan harith din tana ihu " innalillahi wa inna ilaihirajiun, harith karka mutu ka barni dn Allah, "!

Kuka take haikan, daga saman unclen Ben ya sauko da gudu da sassarfa, a mota suka sanya yaron suka dunguma asibiti, da kyar aka karbeshi saboda police case ne, bayan awanni aka samu nasarar fitarda harsashin sede kuma fa harith yashiga coma..

Zirga zirga kawai yakeyi a harabar gidan , yakanji tashin hankali idan ya hangi jinin yaron male male akan inter locks din, ya kai gauro ya kai mari, yanata gumi, duk wani  zafi  Daya dauko ya sauka amma bayajin zai iya yafe mata! Tausayin yaron ya kamashi baya raba dayan biyu wanan yaron jikansa ne, wato harta haihu? Jikinsa ya kuma sanyi. Ji yake Kamar ya bisu asibitin yaga halin da suke ciki.

Fitowar likitan ya sanya su mikewa baki Daya, sukayi Kansu

" calm down, he is fine bt still in a coma, we will watch his condition for 24hrs"

Jikkunansu a sanyaye suka bukaci ganinsa,  yana kwance akan gadon an jona masa na'urorin taimakawa numfashi, ga bandeji daure da kugunsa wanada jinin yake ratsowa ta jiki, kuka  takeyi sosai, tana tuno lokacin dayake cemata su tafi bayason zama, Ashe Gurin ajalinsa ta kawoshi bata Sani ba, idan har harithd ya rasu ta dalilin mahaifinta bataji zata iya yafewa kanta duniya da lahira, wanan kuma shine zai zamo Abu mafi muni Daya faru da Ita a rayuwa, sonda takema harith ba kadan bane baya ma kwatantuwa da sauran diyanta, tafi shakuwa dashi, gabanta ya fadi data tuno yadda kowa zaiji idan yasamo labarin harith ya rasu musamman babansa, tasan Allah ne kadai zai rabata dashi, bayan haka mamma kam cewa ma zatayi Taje Tayi tsafi dashi ne, Allah ka rufamin asiri ka tashi kafadun yarona Allah ka dubeni, I CNT bare dis, sauran yaran sun yanyameta suna kuka haikan suma, so suke ta maidasu gun abbansu kawai su huta su sun hakura da game din hakanan.

Da kyar madam jeniffer ta rarrasheta abinka da uwa da da, nan da nan ta soma sanyaya mata zuciya, tare da yayarta da kaninta, haka suka wuni cikin zulumi, kafin yaron ya farka da dare, aiko de ya farka cikin firgici, da buge buge, har saida likitoci  suka hau kansa aka masa allurar bacci, maddam jeniffer ta koma gida dn debo musu abubuwan bukata tunda abin bana kare bane, duk da dare ya tsala amma garin abuja ba Susan da wanan ba, hasali ma mafi yawancin mazauna garin wanan talatainin Daren shine lokacin shagulgulansu.

Jin motsinsu ya sanya shi mikewa cikin sauri ya fice dn ya tarar dasu adua yake Allah sa yaron yana Raye, dukkansu babu Wanda ya kulashi, suka rabe ta gefensa ko kallonsa basuyi ba, haka ya sanya jikinsa ya Dada sanyi, a daki yasamota tana tattara abinda zasu bukata, ya tsaya yana dubanta, ita ko kallonsa bata son yi, ba tun yau ba take fama da halinsa na rikau da taurin kai, tana hakuri amma wanan Karon yakaita makura batajin zata saurara masa akan wanan abin dayayi kuma dole seta nuna masa kuskurensa, wanan karon bazata sake rasa diyarta ba zatayi duk mai yiwuwa  dn ta ga ta kwato diyarta!

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now