SADAUKARWA

716 99 2
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na ishirin*

Wandonsa da rigarsa duk ya zare, ya afka kanta Yana cewa " yau saina haramtaki ga mahaifina, Idan nasanki a Diya mace ai shikenan ko, duk da tsabar tsanar danayi Miki da kyamarki danakeyi, gwara na kusanceki dn kawai ki haramta ga mahaifina"

Ganin da gaske so yakeyi ya afka Mata ta Soma zuba aduoi iya kqrfinta cikin ikon Allah wani karfi ne ya zo Mata ta hankadeshi, seda ya bugu da gini, tamike da kyar dn ceton kanta , Amma wani jiri ya hanata kwasa a guje, tuni ya cin mata ya shatale kafarta. Takuwa Fadi ruf da ciki gigitacciyar karar data saka ne, ta jayo hankalin haj data biyo bayanta ganin magriba tayi kuma Bata yarda da shirun ba  , tasan munafircin gidan sarauta tasan kaidin gidan sarauta, komi na iya faruwa Bata yarda da kowa ba Akan RAHMATULLAH!

Sashensa ta nufa har Tana tuntube gurin shiru DN bayi duk sun tafi sallah,

Yaune haj tayi mummunan gani , ga jikanta da tafi so tsirara haihuwar uwarsa Yana neman haikewa Yar tqhalikan Nan, da dukkan karfinta ta angajeshi , ta Soma ijjiga rahma wacce ko yatsarta Bata motsawa ga wani jini dayake zuba male male, dago idanunta tayi ta dubeshi fuskarsa Nan kwabe, ta mike taje gabansa ta Soma tafka Masa Mari Tana tambayarsa " me kayi Mata saraki, saraki me kake Shirin aikatawa baiwar Allah Nan, saraki Ashe Kai azzalumine?

Azuciye yace " sonake na haramtawa mahaifina ita tunda ance aurenta zaiyi"

Wata hajijiya ce taji ta saukar Mata, idanunta har baya gani, da rarrafe ta koma gun rahma Amma shiru, ba shiri ta fita neman agaji zuciyarta cike da fargaba da tashin hankalin da Bata taba fuskanta ba aduk tsawon rayuwarta na gidan mulki inda ake kowace irin gwagwarmaya dn kowa ya tsira da mukami da izza, fagen da zaa iya kisa ko lahanta bil adama dn wani cikar buri, yau ta sallama duniya tazo karshe lokacin kawai ake jira.

Dogarawa biyu ta samu amintattu, taja kunensu kan maganar bataso ace a sashen yareema aka ganta, sashenta aka kaita sanan ta kintsata a gurguje sukayi asibiti.

Likitoci sun amsheta, sede sunce aiki zaayi Mata kuma sai an saka hannu, wanan yasa tayi Kiran waziri da Dada suka , zo sede duk tambayar da zasuyi Mata ta kasa cewa Komi  se kuka kawai takeyi, waziri yasa hannu, aka Shiga da ita, suka zauna Nan jungum jungum.

Kimanin awanni hudu aka Diba ana mata aikin daga bisani aka fito da ita

Da sauri duk suka taso, " likita Yaya take? Ina abinda ta Haifa"

Dubansu yayi yace " toh mun Ciro abinda ta Haifa Amma har yanzu baiyi kuka ba, Bai motsa ba Amma kuma da numfashi a tare dashi, tasamu da namiji, ita kuma  zuwa wayewar gari zata farka"

Ya maida numfashi lokacin da duk suka rude da salallami

" Yaron ba karamin buguwa yayi ba acikinta Dan har bangaren hanunsa na dama ya Dan Tara jini, muna kyautata zaton faduwar datayi ne ya janyo haka Amma zamuyi iya kokarinmu muga min ceta rayuwarsa"

Wazirine yace" zamu iya ganinta?

" Sure Mai zai Hana baba"

Ya Mike wani korido suka bishi abaya har cikin dakin, ya fice ya barsu jikinsu a sanyaye.

Dada kam kuka takeyi haikan Tana cewa " um um rahma Kinga rayuwa rahma kina kan gani rayuwa Allah ya saukaka Miki, ya Sanya imaninki marar rauni ne"

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now