SADAUKARWA

476 84 4
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *Sadaukarwa*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi Na sittin da saba'in*

Gumine ya rika keto mata, daddy ya bata yan kwanaki Tayi making decision ko de ta zabi Daya ko kuma ta kawo wani wanan karon babu dole acikin abin.

Hankalinta ya soma tashi dn shirun yayi yawa gashi lokacin da daddy ya bata Yana Neman kurewa yaya zatayi, kwallah suka zubo mata data tuna da Hajj tananan komi zai warware mata da sauki, ba shiri ta kama azumi, da aduoi, kowa de ya zuba mata na mujiya ba Wanda ya ce zabinmu wane ne an bata yanci.

Se me?

Ranar da waadinta ya cika, waziri ya kirata falonsa Yana sanar da Ita Tayi bako daga Gurin maimartaba, a falo ta samoshi ya hakimce, yasha wani kwamemen tabarau, da wani uban kwabdeden agogo a hanunsa, se wani shan kamshi yakeyi, ta dubeshi sosai wazata gani kamar yaron nan imarana!😳😳😳😳😳, ya washe baki kafin yace mata " surprise surprise"

Ta kalleshi shekeke tana zama tace " uhum imarana kenan Kaine yau a gidanmu, Ashe zaka iya barin kwallo kazo ka dubamu"

Yadda take maganar kamar wata Yar shekaru 60 tana wani tattabe baki ita wai ala dole seta nuna masa ruwa ba saan kwando bane tafishi shi karamin yaro ne.

Dan murmushi yayi Yana hasaso me take ayyanawa game da shi din, yau zai bata mamaki zatasan yara ma Suna suka Tara ai,
" maman harith mun sameku lafya? Ya kowa da kowa ya yaran nawa"?

" lafiya lau, ya school?

Yana tube gilashin yace " school angama ai har service ma ni yanzu bigger boy ne"

Ta danyi murmushi " uhhhmm gaskiya fa, yanzu da seka jona masters dinka at young age zakaji dadinta"

Dariya yayi kafin yace " aure zanyi ai bawani masters, tunda INA kasuwanci nakuma Samu aikina, meya rage kuma? Sai mata ai kawai"

Tayi galala kawai tana dubansa, yaron nan yanason kureta

Ya katseta " dama maganar auren ne ta kawoni gunki"

Ta dan zaro idanu " ni kuma toh me zan maka?

" ke ce kikeda abin yimin kuwa, komi ma Yana hanunki"

Ta dan yi dariyar yake gabanta na dan faduwa tace " hannuna kaman yaya fa?

Tasowa yayi daga inda yake, yazo daf da Ita yayi zaman dirshan.  Ya mata wani irin shuumin kallo Daya rikitata nace yau taga aikin yara🤣🤣🤣🤣

Da wata iriyar murya yayi amfani yace " maman harith inasonki kuma inaso na aureki dn Allah ki amincemin, zakiga soyayya Marar iyaka me dorewa, bazakiyi nadama ba"

Ya salam!!! Abin har ya zamo haka da Zaid Yana Raye kila seya kusa kasheshi dn wanan reni, ohh zawarci me kwashe kwashe wai imrana ke sonta da wani tsareta da magan ganun soyayya ta shigesunta wanan abin kunya da me yayi kama.

Ganin duk ta daburce yasa ya mike ya dauki wayarta yayi dailing numbarsa, yaga numbanta ya ajiye mata, ya dan kafa mata idanu kafin yace " zan baki lokaci dn naga kinshiga shock , amma duk abin da na fada miki babu karya ciki, nima bansan lokacin Dana tsunduma sonki ba wallahi maman harith"

Ya dan ja da baya Yana ficewa yace " zuwa gobe nabaki kiyi nazari, dn banason adauki lokaci auren kawai zaa daura mu koma damaturu da zama inda na bude sabon kasuwa, ki kulamin da kanki babyna"

SADAUKARWAOnde histórias criam vida. Descubra agora