SADAUKARWA

425 62 1
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na arba'in da shida*

Kallo suka bishi dashi alamun mamaki karara a fuskokinsu, girgiza kai beebah takeyi kawai dn tasan ba Abu bane mai yiwuwa Bakonta ya doke juma, mutuminda har kisa yakeyi a shadi in yaso yin mugunta, haka kawai in ka bashi haushi ma seya hada shadi yace a zo a fidda raini.

Tsakiyarsu yashiga ya zauna, ya dubesu dukkansu ya fara basu kwarin guiwa " ko babu so tsakanina da beebah Baffa bazan taba bari ta auri azzalumi,jahili irin juma ba, ko ban saka muku da komi ba Ku barni na saka muku da wanan dn girman Allah shine iiya abinda zan iya yi muku na rama muku halarcin da kukayi mini, Baku San koni wanene ba kuka bani dukkan rayuwa, ni dinma kaina bansan ni wanene ba, mugu ne ni, barowoneni, Dan fashine, me yankan Kaine duk ban Sani ba, duk da haka kuka aminta dani, a sanadinku nake kyakkyawar rayuwar da banjin rayuwata ta baya haka take, banjin nakai haka hakuri kirki da karamci a boyayyar rayuwata, zamana daku ya maidani mutumin kwarai, nikuwa maizanmuku namuku sakayya Daya wuce wanan abin?

Jimmm sukayi kafin daga bisani Baffa yace cikin jimami " ayya bako am ba ki munkayi bafa, tsoron abinda kaje kazo muke gudu, juma mugune Kuma mayene ga shadi, inde har zakuyi fa sede muma muyi namu shirin na shiryaka"

Dago kqnsa yayi ya dubeshi yace " haba Baffa INA tauhidin yake? Ai babu wani rintsi dazai sanya mu shirka da sabawa Allah, mu nema gurinsa shi zai bqmu kude kutayani da adua"

Karfafa musu guiwa yayi Tayi har sukaji sun aminta Allah ne zai basu SAA.

Beebah kam duk wani tsoro ya fice mata arai, 

Da Daren ranan sunacin abinci, hasken fitilar aci balbal ta harka gurin fuskar beebah Tayi fayau da Ita se sheki takeyi, zuba mata idanu yayi yana yaba kyawunta acikin zuciyarsa, harta farga, hada idanu sukayi Tayi murmushi ta sadda kai kasa, daga kasan makoshinsa ya kirayi sunanta da wata irin siga " beeeebah"

Wani yarrrrr taji tsikar jikinta ta zuba, saboda wata magana disu data tsinkaya a muryar tasa.

" kinsan kinada kyau kuwa beebah?

Ta sake sadda kai  kasa

" kafini kyau fa"

Ta fada masa cikin kunyarta datake Dada burgeshi, matsowa yayi kadan bayan ya tsame hannuwansa daga akushin abincin,

" um um beebah, kin fini kyau nesa ba kusa ba, har fata nakeyi mu samu yarinya kamar ke dinan Kuma zan yi miki takwara na maida mata sunanki tsaban  sonda nake miki"

Tayi shiiru kunya ta lullubeta amma Kuma se wani Abu ya taba mata zuciya yana iya gano hakan, tambayarta yayi " menene Kuma kika gimtse fuska?

Ya iya ganota ta ko INA komi Tayi yasan fassararsaa,

Dan shiru Tayi kafin ta CE " tsoro nake ji karkaje ka tuna bayanka ka yada dani, kila kanada matarka wacce tafini kyau da komi wayayya Yar boko bani ba diyar hilanin daji dqmusan komi bq Allah Daya hallicemu ma kai ka doramu bisa turbarsa"

Ta kare maganar cikin Alhini, aransa yake sakawa ko yanada mqta ma toh shi dai bqyajin yataba sonta kamar beebah, shin yqma tabayin son gaskiya kuwa banda akanta? Bazai iya tunawa,

" INA adua ko zan tuna baya Allah ya barni da wanan son danake miki, sonda nakejinsa na gaskiya , son da banjin na taba yiwa wata mace bayanki"

Sanyi taji cikin zuciyarta ko baa komi Allah ya azurtata da managarcin namiji Kuma haziki!.



Su juma kam anacan ana tsumuwa, ba shi ba har bulalar dazaiyi amfani dashi seda aka tsaface ta, yasha bauri da tauri da tsumi har ya gaji, har tausayin bako yakeji Dan bugu guda zaiyi masa ya mutu mut! Abar ma zancensa beeebah tazama tasa har abada, lokaci lokaci yake tsuma yana kwafa shi kadai yqna wani kqrkarwa ji yakeyi tamkar ranar ma bazata zo ba.

Duk wani me kaunar Bako da beebah adua yakeyi musu ta da cewa, shikuwa bako ya tanadi ILAJISIHIR dinsa Wanda ya tofa tareda gqnyen magarya yanata wanka dashi dn Neman tsari banda aduoi dayake ta faman yi.

Garin na RUGAR ARDO ya Tara taron da baa taba irinsa ba duk dn wanan alamari, kowa kunshe da tararradi a ransa.

A Filin shadin juma ne yake ta tsuma yana kwarmatato tamkar zararre yan gindinsa suna kara zugashi yana tsuma , jikin kowa seda ya fara sanyi dn yadda yakeyi din.

.mintuna kadan bako ya bayyana a Filin, cikin natsuwarsa, ya tube rigarsa nan kowa ya fara mamakin ganin kwanjinsa Ashe shima bijimin namiji ne har yanaso ya girmewa juman, nan aka dauki sowa da tafi raf! RAF! RAF!

Hakan ya sake tunzura juma baran ma yanda yqga beebah tana tsalle tana tafi seya harzuka.

A tsarin shi zai fara shadin, nan bako ya mike ya daga hqnnayensa ya turje kafafunsa cikin kasa, yana kwaroro aduoi,  juma ya takarkare ya lafya masa Daya Dede karfinsa, zafin ya shigeshi amma ba yadda ake zato ba, nan juma yashiga lafta masa bulalar duk inda ya bugga sai fatar ta tashi, yakai mintuna ashirin yana bugunsa har bulalun suka karye inka dauke jikinsa dake da ahatin bugun bawata. Alama da zata nuna yanajin bugun.

Har Juma ya gaji dankansa nan fili ya kacame da murna. Beebah kamar zataje ta rungumo mutumin nata.

Guri ya natsa bako ya amshi bulalar shadin nan ya dadai ci marar juma da basmala a bakinsa ya zuba masa, nan yaji abin ya shigeshi, ya Dan motsa, ai bugu biyar juma ya soma rawar Dari, tuni ya fadi agurin.

Ehhhhhhhhhhhhh!

Mutane suka Debi sowa, dagudu beebah Taje ta rungumoshi tama mance halin da suke ciki!!!!!!

#vote
#comment
# share
#like

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now