SADAUKARWA

688 104 26
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na Ishirin da tara*

Rabbana atmim Lana nurana wa kaffir sayyi'ati a'amalina watawaffana ma'al abrar.

SARK'AK'I YA

ZAREN TSAKIYAR LABARIN

Tana gaban ZALZALU hankalinta a tashe , yau fuskarta Babu annuri shima, saboda yanayin da ake ciki din,

Fuska a turbune yace " na fada Miki aikin Nan baida wani makari, a lokacin bakice bakya so ba sai yanzu da abin ya dawo kanki, mu Babu abinda zamu iya, Inde har kuwa Bai auri wanan yarinyar ba, kuma Dole yaci gaba da amfani da wnaan maganin, in ba hakan ba kuyi kuka da kanku"

Itama a fusace Tace " wallahi bazai yiwu ba"

Cikin wata murya Mai tsawa yace " fulani kokinsan a tafukan hannuna kike? "

Shiru tayi kafin ta bar gurin a fusace.

Abin duniya ya Mata yawa ta Ina zata fara ceto gudan jininta? Mai yasa Komi take kwabe Mata ne wai? Me yasa Komi baya tafiya dai dai?

Ta runtse idanunta Tana hango gawar dannata kwalli guda daya, farat ta bude idanuwanta ta tashi ta zauna, Tana cewa " Kai Ina bazaiyiwu ba billahil azeemu Dole ya Kara Armen Nan"!

********************************************

TSAFI GASKIYAR MAI SHI

Cikin ikon Allah MONIFA ta kudira aiki da wanan maganin, wata ranar asabar kuwa ta gayyaceshi can inda suke shaye shayensu,

Jikinsa a salube ya dubeta zai Bata hakuri, ta dakatar dashi cikin washe Baki Tace " karka damu na hakura, zamu koma kamar da can"

Ta Dora hanunta bisa nashi ta langabe ki irin yanda Wanda sukaji bariki suke kwace Mana mazajenmu dashi, Tace " DNT worry muyi adua kawai, cause all of me loves all u love ur curves and all ur edges , all ur perfect infection give ur all to me , I give my all u, ur my end and my beginning, even when I lose I am winning"

Ta karashe zancen nata da wata wakar datasan yafi kyauna fiye da kowacce ta babban jarumin mawakan soyayya na alif dubu biyu 2000 wato John legend da taken wakarsa all of you.

Wani lumshe idanu yayai tare dajin kamar an sanyashi a cikin aljannar firdausi, ya kwakumota jikinsa son da yake mata din ya koma na gaskiya tanada wasu abubuwa dayake matukar so a tare da ita, wayewa, iya bi da namiji, da sauran wasu boyayyun alamura dayake kishin kowane namiji yasansu a tare da ita.

Rananr dai ta aiwatar da nufinta  a kansa, Mai aukuwa ta auku, Nan wani mummunan kulli ya kullu a  tarihin rayuwarsa! Wanda zai sashi Dana sani Babu adadi.


********************************************

Yayi kwaankin Nan cikin azaba da wahalar soyayyar Monifa wani sabon lamarine yake aukuwa gareshi, bayajin Komi baya ganin Komi face ita, jarabarta kuwa dayakeyibata kwatantuwa, kuma wani abin tsoro Monifa ta fara janye Masa dn Tace se de suyi aure ya Rika kusantarta ko kuma a hakura ta Yi aurenta Wanda duk wanan wasu strategies ne na daga Masa hankali da kamashi a hanunta,

Yau kam ta kaishi makura yasha ya bugu dn Babu yadda ya iya ya dawo gida Yana tangadi da tambele

TSAUTSAYI!!!!

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now