SADAUKARWA

724 148 21
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na goma Sha biyu*

Hakuri shine maganin zaman duniya, mafiya yawancinmu Yana bamu wahala, Amma ga aduar da zata taimaka Miki ki makanwajen koyon hakuri da tausasar zuciya👉🏿👉🏿👉🏿 Rabbana afrig alaina sabran watawwafana muslimin, wanan aduar Tana daga cikin rabbanoni guda arbain nacikin qurani.


Cikin kaduwa ta zuba Masa ruwa Tana Mika Masa " ungo uncle Sha ruwa , sharuwa"

Ta Debi ruwan a hannu ta zuba Masa Akan kafarsa hakanan nna yake Yi musu Idan sun kwaru in sunacin abinci.

Da kyar ya dawo saiti, duk sai yaji ma ya koshi , ga wani abincin ya fice Masa a Rai, zuciyarsa ta Rika wani irin Abu da bai Taba jin irinsa ba, mikewa yayi har Yana tangadi ya bar gurin dakinsa ya nufa , Yana zuwa ya zube a kasa, Yana wani irin zufa! Me hakan yake nufi kenan??

Wata zuciyar tace kishi kakeyi ZAYYAN kana kishin ann, kana kuma sonta son da baka taba yiwa kowane mahaluki ba.

Juye juye yayi tayi, Idan zaiyiwa kansa adalci yasan zuciyarsa ta kamu da kaunar Ann tun Tana kankanuwarta, tun Bata mallaki hankalin kanta ba, Amma wautar dayayi shine tun lokacin daya hakkake a zuciyarsa cewa SO ne yake Mata ba zancen Yan uwantaka ko tausayawa, SO ne marar algus, so ne irin Wanda duniya ta daukeshi Karya ta daukeshi babu shi se a finafinai, so ne fillah!

Sai yayi zaton ai zata soshi haka kuma zai bayyana  matane bayan ta Kara hankali Ashe wani ya bigeshi, wani kafa gwamnatinsa a zuciyarta?.

Daga Nan dataji shiru daki ta shige itama tanata wasi wasin me ya ke fatuwa? Ko agurin magana tayi laifi ne?


Har washe gari bai kuma haduwa da ita ba duk saita damu, Dada ce ta sameshi har daki ta zauna Tana dubansa baimasan ta shigo ba Saida tace SADAUKI!

Ya danyi firgigit ya dawoda tunaninsa,

" Meyake damunka ?

Ta jefo Masa tambaya

Jiki a sanyaye Yana yake ya Dan tashi ya zauna Yana cewa " Dada lafiya ta kalau fa kawai de.......

Ta katseshi " kana sonta ko?

Da gaggawa ya dubi idanunta da suke kafe kansa, seyaji kwallah suna Shirin zubo Masa ...

" Dada ba hak.......

" Kana sonta fiye da komi, ban taba ganin abinda kakeso ba a duniya irinn annah, wanan shine gaskiyar magana"

Kukan dayake kokarin boyewa ya kubce Masa, da sauri Takoma kusa dashi ta rungumeshi Tana lallashi

" Matar mutun kabarinsa SADAUKI, ka kwantar da hankalinka kayi adua, Idan haka ya tabbata zanfi kowa murna, Amma kuma bazamu so kanmu ba mu bar Annah ta zabi abinda takeso, dn Allah, inhar kana sonta da gaskiya kaso abinda takeso ka karfafa Mata guiwa tunda kasan komai game da ita"

.rarrashinsa sosai tayi, inda ya saduda ya danne zuciyarsa ba don yaso ba saidon yanason annarsa fiye da kansa.

Tana girkin Amma jikinta duk yai sanyi, jin mutum.tayi a bayanta Yana cewa " kar dai ayi Mana danyen tuwo"

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now