SADAUKARWA

452 75 4
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi na saba'in da biyu*

Wanan shafinki ne  kawata aseeya66 me littafin Hargitsi masomin rayuwa! Thank for ur kind gesture  the Somali friends are exceptional😘🤪😁

Dada CE ta doka salati tana kuka, ta dagota kenan su zayyan suka shigo, jikinsa na rawa ya tallafo abarsa zance ko abarsu shida   zaid, jijjigata ya somayi yana kiran sunanta, yaran ma suka rufu akanta suna koke koke, da azama yayi mota da Ita, zaid ya fito shima, kawai ya fada motar, shima basu kula juna ba se lokaci lokaci Zaid ke CE masa " zayyan kayi Sauri dn Allah kada mu rasata"

Wayaga karfin hali!

A asibiti abokin  zayyan ya amsheta ya soma dubata, Zaid ya lafe agefe yana kuka yana cewa " Allah na tuba Allah dan Allah na tuba, na tuba, kada horeni da kashe rahma kamar yadda beeba ta tafi, Allah ka yafemin, ka bar rahm koda bazata zamo tawa ba, Allah ka yafemin, bazan karaba, na zalunci kaina na zamo bawa shaidani nayi izgili ga Wanda tafini rikonka,Allah bazan sake ba wallahi bazan sake ba, Allah dan Allah"
Wato akwai lokuta da dan Adam ke samun kansa cikin wata iriyar nadama, da tsoron mahalicci dn yasan wanan ba kamun kowa bane sena mahaliccinsa wani Abu yakeji a kirjinsa mai nauyi mai ciwo! Ciwon da baki bazai taba iya fadarsa ba, ciwonda yafi kunar wuta zafi, se yau yake kara nadama kan nadamar abinda yayi a rayuwarsa da yadda ya rike rahma meyasa tun farko bai sawwake mata ba yayi amfani da biyayya ga iyaye ya cutar da ita, ai ya cancanci kowane irin hukunci daga gareta, bazai taba jin haushinta ba hasali ma kunyarta yakeji.

Kukansa da maganganunsa suna suya a ran zayyanu, wani irin mugun tausayi ya kamashi, ai besan lokacin dayaje ya dan dafoshi ba, Dama kamar mai jira sai kuwa ya fada jikinsa ya rika kuka kamar Allah ne ya aikoshi, " zayyan ka rokarmun Allah da bakinka me tsarki ya sassautamin ya yafemin ya rufamin Asiri dn Allah"

Kuka yayi sosai har seda yaji kaman babu hawaye a idanunsa. Fitowar likitan ne ya sanya shi bazama gurinsa yana jefo masa tambayoyi ratata

" likita bata mutu ba,? Ya jikin nata"

Yaya............

Likitan ya katseshi " she is alright now, dama tashin hankaline da tsoro kuma I am sory to say Tayi barin diya biyu na wata uku, an mata wankin ciki, kasancewarta me maihaifa me saurin buduwa ko yaya taji tsoro ko tashin hankali zata iya bari, dn Allah a kula"

Dafe Kansu sukayi dukkansu kowa yana jin ciwon rai!

Sun samu ganinta tana kwance kamar ba numfashi, dada ma kuka takeyi,  sukuma sun sanyata agaba kaman a shirin wasan kwaikwayo, zayyan jarumi baya kuka se hadiyar zuciya, mazaje kuwa tuntuni sun dawo mata dn kuka yake risga abinsa ko kunya baiji.

Itakam bata farfado ba sai wajen tsakan dare, motsinta ya tada zaid, da sauri ya tashi ya matso kusa da ita ana haka zayyan shima ya motsa, da zayyan ta fara tozali setasa kuka tana cewa " hibbini kaman naga jini kafin narasa inda kai na take ko? Nayi bari ne!?

Ta soma shafa cikinta  ciwon datajine da kuma jinin dake dan zuba yasanyata Sanin lallai Tayi bari wata dunkulalliyar tsanar zaid ta taso mata shikenan. Yayi sanadin barinta a karo na biyu! Ita kuwa me zataci da yareemA kallonsa batasonyi bare jin sunansa.

Rarrashi ya somayi, tana daga idanu ta ganshi a tsaye a gefenta ya kafa mata idanu!

Wani ihuu ta kurma Wanda yakusan tada kowa a asibitin, Wasu su zaci ma mutuwa akayi,
Da karfinta take magana

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now