SADAUKARWA

752 71 13
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na goma Sha  shida*

Kirjinsa ya Dan dafe Yana wani irin zubda zufa, innnalillahi kawai yake karantowa, Bata lura da halin dayake ciki ba dn kanta a sunkuye yake tanajin kunyarsa sosai wanan Karon,.

Da gaggawa ya bar gurin, Dada ta mike tabi bayansa , bandaki ya shiga ya zuzzuba ruwa ajikinsa da kansa dayakejin ya dauki caji, wani kuka ne yazo Masa ya kuwa fashe dashi Dede karfinsa ( nace Ashe sojoji suna kuka😨😨).

Dada ce ta fada bandakin ta rukoshi da kyar tanfito dashi Tana lallashinsa bayan ta rungumeshi

" Haba SADAUKI na Haba babana, haba Dan Dada Katuna fa Kai Mai hakuri ne da kawaici, kanada tawakkali kuma dn kanada addini, matar mutum kabarinsa, Idan annah rabonka ce seka aureta ZAYYAN wani Bata auren matar wani"

Wadanan kalaman na Dada suna sashi yaji sanyi sosai, saide kuma baiga ta inda zasu faru ba Yana sanyawa kansa yarda Dole da hakan kodon ya samu sauki a ruhinsa,

" Dadah inason annah dayawa dayawa ki taba kirjina kiji yadda zuciyta take bugawa dn Allah dn Allah taba kiji"

Hanunta ya Sanya daidai kan kirjinsa dayake bugawa Bal! Bal! Bal!

Yau Babu kunyar Nan ta Dan fari , itama jajircewa tayi kada ta daga Masa hankali dn kwallah taji Tana Shirin zubo Mata, sosai ta Soma jijjiga shi Tana cewa " nasani SADAUKI nasani adua itace kawai maganin wanan abin kaji, ka jajirce kayi adua sosai"

Ya amsa da "toh dadah kema ki tayani dn Allah"

Sun dauki lokaci Mai tsawo, kafin ta samu ya koma dai dai sede Bai fito ba kwanciya yayi, kafin magrib kuwa zazzabi da ciwon Kai sun rufar Masa , shigan waziri dakinsa ne ya tarar dashi a haka hankali a tashe kuwa ya shiga cikin gidan,

" Annah, bakisan Dan uwanki baida lafiya ba halan"

Mikewa tayi a rikice Tana cewa " baba Yana Ina? Meya sameshi ? "

" Yana dakinsa Nima yanzu na shigana sameshi magashiyan akwance"

Bata jira Komi ba ta fita ta fada dakin su dadah suka biyota abaya,

" Uncle meya sameka dn Allah"

Ganin Baya cikin hayyacinsa ya Sanya ta sa kuka Tana cewa " baba akaishi asibiti dn Allah baba"

Asibiti aka nufa dashi, likitoci suka Soma aikinsu na nema Masa lafiya.

Anan asibitin suka kwana, sai washe gari masu dubiya suka Soma tuttulowa , yareema ZAID kam anan ya ke wuni har kwana, suna tare, ganin yadda kowa ya tashi hankalinsa musamman dadah da annah ga uwa uba amininsa da ko bacci bayayi sai yayi kokarin danne duk wani Abu dayake zuciyarsa ya maida komi ba Komi ba, ya Soma tsananta adua.




********************************************

Hutunsu ya Kare Dole suka tatttara suka koma hakan ya Kara Masa kwanciyar hankali sosai, dn Bata ganinta duk da Tana manne a zuciyarsa, yareema ya koma harkokinsa duk da shima AZARA Tana zuciyarsa sede yanajin shi jarumi ne zai iya mance duk wata mace da zata zame Masa matsala, kafin wnaan lokacin kuwa barasa tabi jininsa, Mata ma haka, ya jefa kansa acikin wnaan boyayyan lamarin da bawanda yasani daga shi sai Allah sai amininsa, Wanda yanzu boye Masa yakeyi. Se muce Allah ka shiryar damu.


SADAUKARWAWhere stories live. Discover now