SADAUKARWA

488 61 4
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi Na sittin da tara*

Abu kamar wasa gaba ta kullu tsakaninta da mamma, ya rabbi mamma wace irin mutum CE? Amma fa kusani duniya tana cike taf! Da ire iren su mamma har wadanda suka fita, sufa Kansu kawai suka fiyeso, basu damuwa da kowa bukatarsu tasu ce, haka nan idan suka sama Kansu Abu toh babu mai iya canza musu shi! Kuma mafi yawancinsu basu barin wanan halayyar har sai mutuwa ta riskesu bagatatan! Allah ka kiyashemu.

Tun raham tana damuwa har ta daina ta gane wanan shine kaddararta kuma bata isa ta canza ba, takabarta ta kare, seta maida hankalinta kan Neman ilimi ta kowane fanni ta kama masters dinta a nan state university, babu nisa da motarta take zuwa, yara ta sasu a makaranta, ta cigaba da shaaninta, zuwa yanzu ta zamo malamar kanta, Wasu ma tana kararsu da dumbin ilimi da fasaharta, da yawa yawan mutane suna shaaawar rayuwarta a rufe ruf zaka ganta, kumasaye da niqabinta rudin duniya ba NATA bane, akwai burirrika data tanada wa converts marasa galihu irinta bakuma zata cinma haka ba har sai ta Gina kanta ta dogara da kanta tukunna bataso ta jinginu da kowa face kanta, gorin mutanen duniya ya isheta, tanaso taji tanada yancin kanta da kanta ba ta dogara da wani ba, shiyasa da akazo batun gado tace Sam bazama ta amsa ba, adai bawa diyansa da matarsa da mahaifansa ita kam ta gode, waziri ne ma ya mata kaca kaca tasha kukanta yace ai hakkintane, kuma in bata amsa ba bata yafewa zaid ba kenan?

Tace ita duk wani Abu Daya daganceshine bataso mamma tana Dada sanya mata tsanar mamacin da komi nasa.

A haka ta amsa, gidan Kano ya zamo NATA da diyanta da motocinsa, da sauran su duniyar Daya Tara baa maganarta, ganin mamma nason ta handame komi yasa taji tausayin mamacin, tace a tona rijiya ayi masallaci kuma sadaqatujjariya ga zaid din.....

Daga bakin hanya ta hango motarsa zuciyarta Tayi fes! Uncle zayyan ya zo kenan yau akwai kwanan zaune ana hira, Tayi parking akofar gida, tundaga zauire take cewa " oyoyo oyoyo uncle dina"

Murmushi yasomayi tun kafin ma ya ganta, ta iso falon dada Wanda yanzu yasha gyara da Wasu kujeru masu kyawun gaske , ta ajiye Jakarta ta cire niqab dinta, ta Dan yaye hijabin NATA ta dn tasha iskar fanka da ac dake falon, dubanta yayi yace

" wai annah haka kike bi tagaban sojojin nan duk jiki a rufe Basa bata miki lokaci ko kuyi rikici"?

Tayi Yar dariyarta me kara mata kyaun fuska tace " tun muna rikici dasu har mun dena sun ma Sanni yanzu kam, sau Daya ne ma fa wani zai rainani har kaman zai taba min niqab nayi Sauri na daga, shine wai yace meyasa nake boye kyau na haka, namasa kaca kaca"

Fuskarsa ya gintse dn wani Abu da yaji ya taho mar makoshi kishi kenan!

Fada ya soma mata " ke Kuma ki ka soma musu shashar dariyar nan taki ko?

Shiru Tayi tana kallonsa kafin daga bisani tace " wallahi ko kadan uncle , nafada maka fada mukayi fa sosai, nace masa an bawa kowa daman zabin yin addininsa dn ana taaddanci bazai hanani yin yadda nakeso ba ai sunce zuciyata a wanke take"

Se a lokacin ya Dan sassauto, ya dubeta yace " ya karatun "

Ta Dan tabe fuska tace " wallahi har ya isheni kodon muna gab da karisawane"

" um um ki dage de nasanki da kokari toh ki kara pls kanwata, kuma kar ki rika kula kowa"

Yar dariya Tayi " Umm uncle kenan nida ko fuskata bawanda ya taba gani har yau wama zai kulani, kowa dai yayi shaanin gabansa, kuma pls you should trust me akan maganan maza banda time din kowane mahaluki, in fact bani ba aure har mutuwa"

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now