SADAUKARWA

691 88 9
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na talatin da Daya*

Rabbana lah tuzig qulubana bada iz hadaitana wahablana minladunka rahmatan innaka antal wahabb.



ZAREN FARKON LABARIN

Sadik hamada d'a ne  ga wan Alh Bakura bukar Mai suna Hamada bukar, uwarsu Daya ubansu Daya, shi alh bukar yanada Diya biyar ba'ana, yadawo, sai yakura da Mustafa, baa goni, Dan auta, dankasuwane Dan Boko kuma Dan siyasa, sabanin shi hamada bukar dayake dankasuwa kawai shima diyansa biyar sadik shine babba sai bukar, sai bakura, ka mairam, da lawan Dan auta,  wanan ahali suna da wata alaqa babba a tsakaninsu da kuma zumunci Mai karfi, kaunar dasuke wa junane ma tasa hamada ya jawo bakura da iyalansa suka taho kano Dan habaka kasuwancinsu tunda Nan yake zaune.

Sadik yarone Dan gata gaba da baya Wanda iyayen sa suke sonsa sede hakan baida sun lalatashi ba dn ya tashi da tarbiya ta gari, yayi karatun injinjya a jami'ar bayaro har matakin digiri na biyu, inda yaso abarshi yaketara can kasashen ketare dn Karo karatun digirin digirgir na PhD, Amma kakarsu wacce take da aji a fada ga dukkan ahalin Tace fir!  Jikanta bazaije kasar arna ba, Dole aka hakuri bawai dn ba wadatar daza'a kaishi ba, hakan ya hakura ya koma jami'ar, bayero din dn ajja mairam itace kankat, duk abinda Tace iyayensa ma Basu Isa suja da ita ba, irin tsaffin Nan ne masu kwarjinin gaske, ga masifa kowa tsoronta yakeji.

Ganin da yayiwa annah yasa ya sauya tunani da dama na rayuwarsa da wasu kaidojinsa dayake ta riko dasu Akan irin matar da zai aura da sauransu, annah ta sauya Masa tunani Yana tuno yadda yakura ta fada Masa wata magana Mai nauyi game da annah " ya SH annah abar tausayi ce, Tana bukatar taimako, kamar Bata shigo addininmu ba a sa'a jarabawowinta masu zafine, wanan ko mu da aka haifemu cikin musulunci bazamu iya jurarsu ba, aure biyu tayi mazajen na rasuwa ta haihu agida na farko, na biyun a hanyar kaita yayi hatsari ya rasu, rayuwarta ta Shiga kaduwa, ni mamaki take ban  kani rin jarumtarta, ta maida Komi ba Komi ba take rayuwarta, Anna tanada hankali badon kawata bace bt she is every man's dream"

Wanan zancen ya tsaya Masa arai sai yaji Yana Kara kaunarta fiye da yadda yakeji jiya, kwanaki na Kara tabbatar Masa ya mugun kamu da son annah son da zallar tausayi yafi yawa da kuma gaurayen kauna.

Sanye yake cikin wani yadi Mai laushi fari fat dinkin Yan Niger Delta, bakin fatarsa ya sake wuluk! Har Yana kyalli, sede fararen idanunsa manya , da Dan bakinsa suna sawa ma ka mance da wnaan bakar fatar tasa, yakura Tana ce Masa dashi fari ne balarabe zaayi,  siraran zanensa na bare Bari sun Kara Masa kyau matuka, a taikace dai SH kyakkyawa ne dai dai shi, motarsa ya Shiga yanata fara'a yau zai Ida nufinsa akanta, yanata tsara kalaman da zai sace zuciyarta dasu Yana tukuin mota, har ya Isa cikin makarantar, 

Text ne ya shigo wayarsa " na hango ka ka taho bayan ajinmu zaka ganmu"

Murmushi yayai Yana jinjina irin yadda yakura take kokari wajen ganin ya cika burinsa, wanan itace kawa tagari.

Suna mahawara kan wani Abu dayashafi halayyar da Adam ta zage tanata zance da kwasar dariya sai kawia taga mutum a kansu, ba shiri ta Soma gyara zama , kunya ta kamata

" Ya SH Ina wuni"

Ta gaidashi cike da kunya, guri ya nema ya zauna Yana furzar da iska da taimakon labbansa , ya dubesu yace lafiya, Ann ya karatu?

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now