SADAUKARWA

416 53 1
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

💖 *SADAUKARWA*💖

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

*Babi na arbain da tara*

Sun tusa keyarsa sansaniinsu. Inda a sansanin sojojin kuma suka kasance cikin tashin hankali. Wani daki suka wurgashi suka barshi.

Mukoma Garin Ardo

Dai dai iya nan ya iya tunawa a nan kuma yaga wani irin duhu ya mamayeshi seji. Yayi idanunsa sun rufe ruf! Bai ma San me ya kuma faruwa dashi ba.

Hayaniyar mutane da kuma ruwan sanyin da ake kuza masa ne ya farkar dashi daga nannauyan bacci ko suma zance, mutanene kewaye dasu Wanda baima sansu ba tukunna, Wasu halittu na daban da bai taba ganinsu ba kyawawane tamkar  larabawa bakake da fararensu, ga dogayen gashi mazajensu da matansu, lallai tsarki ya tabbata ga Allah dayayi wadanan hallita,  ya rasa dalilinsa na zuwa cikinsu, kuma gashi ma kamar har an daddaureshi, idanunsa ne ya fara yawo Kansu, ko zai gane Gurin , tunani yakeyi toh yaushe sansanin yan boko haram din ya juye haka? Ya akayi suka sauya kama?

Daga karshe de ya bada gari akan kawai gamo yayi, nan take ya rintse idanu yana karanto aduoi na Neman tsari.

Amma Ina hayaniyarsu ma taki ta barshi, daga can gefe yaga wani Dan matsagaicin mutumi ya ratso tsakiyar dairar , hanunsa rungume da wata Yar budurwa, kamar tana barci a gabansa ya shimfideta, wani irin kyawune da ita na ban mamaki, annuri ne da haske cike da fuskarta  kamar me murmushi idanunta rufe tsam.

Yasan fuskarnan amma ya mance a ina yanaji yasan wani Abu game da wanan kyakkyawar yarinyar amma a INA??

Shi Kansa baida wanan amsar.

Hango wani suka na wuka yayi a  daidai cikinta Wanda bayan busashen jini akwai kuma sabon jinin dake zuba har yanzu ta cikin hudar.

Gabansa ya fadi kadde ta mutu?

Shikam Kansa ya gama daurewa da wadanan mutane da suke ta koke koke.

Mutumin yagani yana kuka Haikan kafin ya dubeshi  yace " Bako beeba ma mainama"

Tabbas da yaren fulatanci mutumin yake magana sede kasancewar bawani jin filllanci yake ba duk da mahaifiyarsa usul CE ta fulanin nijar da zabarmawa amma duk nacinta yaren Hausa ya kwace mata su sukanji kadan kuma basu mayarwa, amma Kalmar mutuwa da beebah kadai yaji yakuma gane yarinyar dake kwance gabance male male cikin jini ta mutu kenan? Gabansa ya fadi yaana aduar Allah yasa baida hannu cikin mutuwarta dn baisan ya mutanen nan zasuyi dashi ba!

Zazzare idanu ya farayi yanaso ayi masa bayani dallah dallah.

Wani ne ya bazamo cikin filin yana nunashi da yatsa yace " Baffa Bako ne fa ya kasheta"

Razana yayi bakinsa yana rawa yace " ya ya kake nunani, ni sunana ZAIDU! Ba Bako ba ni ban sansan komi ba banma San yarinyar ba wallahi"

Gurin ya kaure da salallami,

Baffa ya dubeshi " Bako baka gane matarka ba beebah?

A razane yace " mata kuma? Ni ...ni ..ni.. Na auri wa?

Dada dumulmula masa kwakwalwarsa sukeyi da wadanan tuhume tuhumen Nasu, toh shi har yaushe yayi wani aure kuma a dokar daji shi yaushema yazo nan wai? Yau ya shiga ukunsa.

Duk dakiyarsa wanan karon babu ita bashi kuma da mafita.

Tabashi mutumin yayi " bako baka ganeni ni Baffa ba baban beebah"

SADAUKARWAWhere stories live. Discover now