SADAUKARWA

436 56 1
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*

   *Babi na hamsin da daya*

  Bacci yayi mai dadi Wanda ya Debi lokaci mai tsawo baiyi irinsa ba cikin natsuwa amma baccin fa cike yake da mafarkai marasa kan gado yawanci na rahma ne da beeba,  sai gabanin magriba ya tashi yayi alwala dn jin kiraye kirayen sallah, Dede korido suka hadu yana Dan dingisa kafa murmushi hamadou ya sakar masa suka jera suka nufi. Masallaci, basu dawo ba har ishai.

Nan tasake shirya musu abinciccika harda na Nigeria kasancewarta ruwa biyu hadizatou kenan matar Dr hamadou, mahaifiyarta Yar katsinace mahaifinta Dan jahar maradi, mace CE wayayya mai riko da addini da sauke duk wani nauyi na mijinta, baida bakin gode mata sede yayi mata adua kawai, suna zaman su lafiya amma basu taba haihuwa shekaru wajen uku da aurensu kenan, Dr hamadou mutumin kirki ne duk da kasancewarsa banijare yana kaunar yan najeriya, saboda mahaifiyar matarsa, kyakkyawane farin bamarade.

Sunci sun sha nan suka fara taba Yar hira, amma duk yadda hamadou yasoo ya binkici zaiduu shi din yaki bada fuska, hakan yasa hamadou din ya rabu dashi kawai yasa masa idon yasan ba cutarsa zaiyi ba, toh dole wataran Allah ya matsi bakinsa ya fada mashi ko shi Waye ne?.

Haka lokaci yayi ta tafiya zaidu nasamun lafiya sosai, har kafarsa ta ware, shakuwarsu tana kara karuwa , anan ya fahimci hamadou mutum ne Wanda yake kusa da Allah duk kyaunsa da kudinsa baisa ya bar hanya ba, mutum ne me addini da kyankyanin zunubi ko Yaya yake, jikinsa ya kara sanyi, tare da kara mika lamuransa ga Allah sosai, seyaji ya koma wani zaidu na daban mai tawadee'u da tsoron Allah yayi masa caaaa!

Yana jin tashin hankali inya tuna abubuwan Daya aikata, irin barasar dayasha, matan Daya nema, sunada dama bai iya kayyadesu, ya duba yaga hamadou ko kallon mata bayayi bare wani ya nemesu matarsa ta sunna ta wadatar dashi duniya da lahira nan jikinsa ya kara lakwas!

Wata ranan asabar zaidun yayi niyyar sanar da hamadou ko shi wanene kuma tayaya zai taimakeshi ya koma kasarsa.

Kasancewar ranar Hutu CE, ya samoshi gindin dalbejiya suna zauna da hadezatou data wadatashi da shayin na'na, da Su kayan marmari, hirarsu sukeyi gwanin sh'awa, sanye take cikin zumbudeden hijabi tunda yazo gidan bata taba bayyana jikinta ba,  rahamarsa ya tuna ya Dan ciza lebe alamar takaici.

Da sallama ya isa ya jawo kujera ya zauna, sun gaisa ta mike tana cewa " bari nashiga sekun shigo zan daura girki"

Hamadou ne ya batada amsa " I will miss u badly dear" murmushi Tayi ta wuce cikin kunya dn bakonsu yana nan bazata iya cewa dashi komi ba.

Saida yagama shaukinta ya juyo kan zaidu, yqna murmushi shi kuwa ya Lula ga wani tunanin, har saida ya zunguroshi ya farga,

" halan kana tuna gida ne danuwana?

Zaidya Dan murmusa yace " hmmmmm kaman ka shiga zuciyata Dr"

Shiru yayi kafin Dr ya katse shirun da cewa" wato na jima banga mutuni mai zurhin ciki ba irin ka ba zaidou, Sam kaki hwadi mini gaskiyar lamarinka, shin ta kaka zan taimaka maka ni da bansa ainifin matsalarka ba"

Gaskiya yake fada kam sekasan ciwon mutun zaka bashi maganinsa

Wasu kwallah ne suka taru suka zubowa zaid yau mazajen suna kuka! Lqllai Abu ya girmama

Murya gwanin tausayi yace " hamadou idan na fada maka koni wanene zaka gujeni domin muna nan halayyata, kasani bazan kara wata kima ko daraja ba a idanunka, kasani bazaka kara so ka mnuaamalanceni ba, ni fasikine, mazinaci ne, mugune, Wanda ya tsana duk wani Arne Wanda koya musulunta bana uzuri, ni azzulumine ga matatata sunna, mafi muni shine ni na kasance cikin mutane masu fuska biyu ne, basusan yawan tarin laifukana ba, basusan ni mutumin banza bane musamman iyayena, na cutar da iyayena nakuma yaudaresu banajin zasu taba yafemin musamman mata ta, Aminina kuwa ya sha wahala da tattauran halina , muguwar dabiata da duk wata hallayyata maras kyau, shin banzama abin kyama ba, shin yanzu bam zama kaskantacce ba kaicona kaicona!

Ya Kare maganar yana kuka na ban tausayi , hamadou ne ya dafashi yana karfafashi " Allah is merciful, zai yafemaka, zaidou, babu wata zunufi da Allah bai yaheshi"

Dagowa yayi gaje gaje cikin hawaye yace dn bqka San LABARINA bane shiyasa kace haka"

" toh zaidou bani labarin naka mana INA bidar najishi ko zan dauki darasi nakuma taimakeka"..............

Bari mu dauko zaren da muka datse a baya ya zamo labarin zaidu ga hamadou..

******************************************************************

Gumi ne ya soma tsatstsafo mata bayan bugun da goshinta yayi, shin kuka zatayi kome? Anya kuwa batayi kuskuren kin bin iyayenta ba kuwa? Anya anya? Wanan zzancen take ta nanatawa, saukin zogin da kirjinta yake yi take nema INA ,zata tsoma rayywarta, meyasa kaddara take mata haka? Meyasa rayuwarta take haka?

Vatada amsoshin tambayoyin, da kyar ta mike ta nufi sashen haj, ta shige tayo alwala  ta kama sallolin dabatasan dalilin yinsu ba, tana Neman mafita gun ubangijinta.... Wanan shine mafarin rayuwarsu me cike da hargitsi!

Abu kamar wasa zaidu ya zamo wani daban kulum yana daki iyakarsa gaisuwada kowa, Allah Allah yakeyi hutunsa ya kare, Hutu na karewa kuwa yayi shirinsa ya kama hanya bai sanar da kowa ba , nan ya tafi ya barta da igiyar aure a kanta.

Sai bayan kwanaki itama taji tagaji da zaman zata koma makaranta kawai, se lokacin ta samu daddy ta fada masa zata koma makaranta kawai, maimartaba yasha mamakin jin zaid koma gun aiki , wato fushi yayi kenan har yanzu be amshi kaddarar Allah ba bisa kansa.

Baibi takansa ba shima saiya shirya mata komi ta koma makaranta. Zuciyarsa cike da tsoron kada dannasa ya kunyata shi.

Kwantar da hankalinta tayi tasa karatunta a gaba , su Maryam na matukar tausaya mata, jin iyayenta sunzo ankuma aura mata ya zaidu ta hakura da duk wani farinci na rayuwa. Takan CE mata " maryam ta yiwu anhalice ni ne dn na kyautatawa wasu mutanen rayuwarsu"

Sihikam tunda  ya koma kansa ya kulle, tunanin yada zai yakice annah daga rayuwarsa yakeyi kawai.

SADAUKARWATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang