SADAUKARWA

1.3K 164 4
                                    

✍✍✍MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*SADAUKARWA*

          

Via wattpad: @maryamtalba

  *Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

*Bismillahir rahamanir rahim*
                
Babi na biyu*

A can wani bigire na nahiyar suke rayuwarsu, tun zuwan  mishinari na farko a shekara ta alif dubu daya da dari Tara da shida, daga kan Oswald waller bafaran se ne, Ernest Belin, da Joseph mouren, Wanda su suka kawo akidar mishinaramci kasar najeriya, awanan bigeran suka rayu har suka hayayyafa inda suka Tara babbar zuria, bayan rarrabuwarsu dn yada addinansu sun shiga lunguna, da sakuna na kasar najeriya inda suka rinjayi da dama nadaka maguzuwa, da kuma kalilan daga cikin Hausa Fulani da sauran yarurruka, wasunsu dayawa basu dawo ba, Wasu sun mutu, Wasu kuma sun bazu har kasashen ketare na kasar kamar su chad,Sudan,nijar, da sauran su.

St Francis Xavier, ya kafa tsatsonsa a wani bigire na kasar inda ya Samar da yaduwar zuriarsa, father William na daya daga cikin reshen da yasamu yaduwar jinin kabilar Igbo ta asali, Wanda mafi yawancinsu sun dauko surar turawa da faransawa kai harda duchawa " dutch"

Shiyasa suka mallaki wani kyau na ban mamaki, matansu da mazansu fararene tas tas! Ga tsaho, ga gashi baki dogo, idanunsu farare, kai sun mallaki komi na kyawu. Kabilun sun hadu sun kuma yawaita a dukkanin fadin nijeria in har zakayi irgen kabilun kasar dole kabilar Igbo tazo ana uku ko ta biyu, sunada hadin kai, da kuma Neman na kai, sun iya juya Sisi ya koma taro, akwia zafin nema mazansu da matansu, da kuma bautawa aure da rike alada tamkar addini, addinin kuma shima an rike kam.

Tun daga cikin cocin take tsanyara kuka ta hana kowa sakata, uwar ta goyota tafito da Ita cikin takaici, tana jin kamar ta mammaketa,ganin Tayi tsit a baya hardda dariya ganin sun fito daga cikin Gurin, gefe ta nema ta zauna ta zubawa kyakyyawar diyar tata idanu, tanajin sonta a ranta, amma kuma cikin tana danjin haushin yanda take so karfi da yaji ta hanata zuwa Gurin bautarta, kullum haka yake faruwa idan sukazo, abin har ya fara damunta, Yar dariya Tayi irin ta yara Tayi ta fada jikin uwar tana jin dadi , sabata Tayi abaya takama hanyar gida. Ranta cike da haushin ta hanata yin bauta, agidan suna zuwa ta bingire ta kama barci. MARY ANN kenan diyar babban pastor na wanan nahiyar me suna JOSEPH WILLIAMS , Ana Ganin girmansa kan duk wani Abu daya shafi addininsu, mutum ne me tsayayyen raayin rikau, da akida mummuna, sede Kuma mutum ne me tausayin na kasa dashi da adalci , Amma fa akan addininsa Baya daga Kafa ma kowa.

Diyansu biyu Rak! A duniya MARY ANN da Kuma SARAH wacce itace babba.

SADAUKARWADonde viven las historias. Descúbrelo ahora