“Oh ni na dauka ko kashe wayar ki kai, domin nata kira ban samu ba”

“Wallahi faduwa tai ta fashe screen din ma ya watse gaba daya”

“Subhanallahi garin ya?”

“Ba zan iya fada ba, ni dai kawai tana hannuna ta subuce ta fadi kasa, ka zo ne?”

“Na zo, sai dai ban karaso kofar gida ba saboda bana son kowa ya san da zuwana, dan ki kawai na zo”

“Ka tafi ko kana nan?”

“Na tafi amman na fi karfin one hour a gurin kamin na tafi”

“Ayyah ban jidadi ba”

“Karki damu zan shigo gobe In-Sha-Allah”

“To Allah ya kai mu”

“Amin mu kwana lafiya”

Ba bari na sake cewa komai ba ya katse kiran, ni kuma na sauke wayar ina ta tunanin abunda zai kawo shi gurina ni kadai, wata kila kum zai yi min jajen abunda ya faru ne ko kuma ya bani wata shawarar, ban raba dayan biyu ba Hafiza ta shigo dakin na mika mata wayarta bayan n goge call din domin Bana son ta san da wanda nai wayar. Sai kuma na nufi inda jakata take na bude na dauko dubu biyu saboda ina son siyo man goge baki da Vaseline din mu daya kare. Hijabina na saka ina Kwalawa Namra kira ta zo ta raka domin ta fi sauran natsuwa da abun hankali, sai dai duk yadda nai ta noke noken na fita ni kadai ban samu sa'a ba har sai da Amal ta gan ni ta biyo da gudu tana kuka, a dole na tsaya na rika hannunta sannan na nufi dakin Mama na shaida mata cewar zan je shagon titi na siyo man shafawa da kuma na wanke baki.

“Ba zaki aika kanenki si siyo miki ba?”

“Ina son fitar ne Mama”

“To Allah ya tsare”

Na amsa da amin sannan na kama hanya ina rike da hannu Amal Namra kuma na gefena na hagu dukansu suna sanye da riga da wando ne yan kanti. Cikin tsananin kunya na ratsa kofar gidanmu na wuce saboda taron da maza yan zaman majalis sukai yi. Wanda na san a nan ma ba zan rasa wanda zai yi gulma ta ba, koma na ce gulmarmu yan gidan gaba daya domin mun tara yan mata Masha-Allah, wanenda aka dade ana zancen wai mai kudi suke jira wasu kuma tuni suka fara yi kanena zargin masu nemansu duk na neman auren suke zuwa ba iskanci ne kawai ke kawo su, ni kuma na dade da yin zurfi wajen sanin cewar aure da haihuwa da mutuwa da rayuwa duka na Ubangijin Annabi Adamuna, wato Allah S W T wanda ke rubutowa bawa abunda zai same shi tun gaban bawa ya zo duniya.
Lokuta da dama kan jarabi bawa da abu ba dan Allah baya son bawan ba sai dan gwada karfin imaninsa da kuma aikinsa. Idan na tuna mahaifina da mahaifiyata ina samun kaina a cikin wani kogo mai cike da tausayinsu musamman ubana wanda na san shi mutane za su zaga, kuma shi zai fi kowa shiga damuwa, domin bayan yan dakin Mama akwai na dakin Inna waenda sukansu yan mata ne da suka kasance a karkashin inuwarsa. Gashi lafiyar kafafuwa ma bata wadace shi ba.

“Momy a nan za mu yi ta zama? Daddyn ba zai zo ba?”

Maganar da Namra tai ka katse min zancen zuci da na dade da yin zurfi a cikinsa, gabana ya fadi ba faduwa ta tsoro ko fargaba ba, ba faduwa ta irin amsar da zan bata ba, ko kuma abunda zan mata ta fahimta ba, faduwa dai irin ta ko wace uwa mai yayana yana daya daga cikin dalilin daya hana ni fitowa a gidan Aminu gudun irin rayuwar da yayana za su yi idan bana gidan, sai dai kuma yanzu da suke hanuna kuma ya rufe idonsa daga kallonsu balle waiwayarsu ya rayuwarsu zata kasance?  Mama tana yawan fada min ba ko wane namiji ne zai auri da yayana ba, idan ma ya aure ni ba zai yarda na zauna da su ba, anya idan na bar su a gida za su samu kulawar da nake musu fatan samu? Ya makomarsu zata kasance lallai juma'ar da za tai kyau tun daga laraba ake gane ta, indai har yau ba tai musu kyau ba ya gobensu kenan?

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now