Kamar wacce aka saka da mashi haka magana Mama ta ratsa kirjina ta shiga har cikin kaina, tsakanin maganar fyaden da sakin da Aminu yai min da kuma maganar Mama sai na rasa wane yafi yi min zafi a kirji.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”

Na fada ina jin kirjina kamar zai fashe zuciyata ta fito waje, muna haka Baba ya shigo dakin yana turo wheelchair dinsa Inna na bayansa tana hawaye shu kuma fuskarsa na nuna tsantsar damuwar da ke tattare da shi. Ina kallonsu sai ya tuna min da wacan lokacin na baya lokacin da aka dura aurena da Aminu, lokacin da ko wace fuska take dauke da murmushi da annashuwa da jindadi.

“Halimatu ya akai hakan ta faru?”

Ban boye masa komai ba ciki har da ikirarin da Hajiya tai na kaiwa Sadi Namra ya rika.

“Wannan maganar banza ce! Taya zai sake ki ba tare da sauraren gaskiya ba kuma be yi bincike ba sannan ya ce zai dauki yaya ya kai wa kanensa? Babu wanda ya isa ya rabaki da yayanki a nan za su zauna tare da ke idan kuma yayi musu kotu zata rabu mu da shi, domin yanzu babu sauran mutunci a tsakaninmu da shi, duk abunda yake takama da shi sai na gani!”

Baba ya fada cikin fushi da daga murya kana kallonsa kasan ransa ya bace sosai, wanda ban yi zaton haka ba domin yana da wahala ka ji bakinsa maganar zamana da Aminu bayan ki yi hakuri aure sai da hakuri, na ji sanyi sosai kuma ina jin na samu kwarin guiwar rike yayana da kyau domin na samu mai goya min baya.
  Sun dade suna da maganar aurena da Aminu tun daga kan haihuwa ta ta fari har zuwa yau abubuwan da sukai ta faru da kuma abubuwan da suke gani ko ji, ni dai ban ce uffan ba domin har lokacin da kennana suka shigo suka saka baki ana yi da su ban ji ina furta ko da sunan Aminu ba a zance balle kuma har nai wata firar abunda ya shafeshi, sannan suna yi an saboda su nuna min kar na damu akan abunda ya faru.

Sai kuma sha biyu sannan kowa ya nemi gurin kwanciya, a lokacin Amal ta dade da bachi a kirjina, sai da na kwantar da ita a kasa saboda fitsarin da take sannan na fito falon Mama neman su Adnan.

“Ai tun dazun Abdallah ya tafi ta su gidansa, yace can za su kwana”

Mama ta fada.

“Har da Namra?”

“Eh har da ita”

“Akan me zai tafi da ita bana son tana rabar kowa a yanzu bari na kira shi...”

Ina juyawa Hafiza ta kirani.

“Anty Halima dan Allah karki kira shi yanzu, kin san dai indan kowa zai lalata miki yara ban da Yaya Abdallah, kuma saboda yana tausayin yaran yai so karki bashi kunya a yanzu”

“Bana iya yarda da kowa akan yarana yanzu, indai har kannen mahaifinsu zai iya yin wani abu na lalata da Namra, to kowa ma zai iya lalata da ita, rayuwar ya mace a yanzu tafi ko yaushe bukatar tattali, idan na nesa be lalata maka ita ba, na kusa zai iya samu damar hakan, idon kowa ya rufe a yanzu Hafiza, ba zaki taba gane abunda nake nufi ba har sai kin yi aure kin haihu sannan za ki gane tarbiya da tsare yaya abu ne mai wahala, ban son na sake aikata kuskuren da na aikata na barin Sadi da yarana har ya samu damar yi min tabon da ba zai gogu ba har na koma ga mahallincina, da na san cewar zuwa na gurin aiki zai haifar da haka da ban yi aikin ba, da na zauna da yayana a ko wane irin hali, a ko da yaushe ina aina yadda Namra zata ji idan ta girma ta samu irin wannan labarin, ida na kuma na sake bari wani ya sake faruwa? Laifin akan wa zan dora shi?daman tun farko be kamata na yarda da kowa akan yayana ba”

Na karasa tare da saka hannuna na share hawayen idona, sannan na kai dubana gurin mahaifiyata wacce ke kallona fuskarta da murmushi.

“Kinji kwatankwacin abunda nake ji a lokacin da kike budurwa ke da yan'uwanki da kuma yadda nake ji a yanzu da nake tare da kanenki, a kullum ina cikin fargaba da tsoron kar wani abun ya same su kar wani ya lalata musu rayuwa, ko daga nan zuwa gidanki suka fita hankalina a tashe yake har sai sun dawo sannan na ke samun natsuwa, shiyasa a kullum bana da burin da ya wuce ko wacce na ganta a dakinta, Halimatu kina jin abunda na ke ji a matsayina na uwa, ke ma uwa ce”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now