PART 37

1.9K 136 20
                                    

Dedicated to all my lovely readers
Lots of love😍😍😍😍😍.

___IDENTICAL_TWINS BY BASMA_BASHIR

                  👇👇ENJOY 👇👇

Karku matso kusa Dani" Ya kwato bindiga daga hannun sojan. Nan ne duk suka maida makaman yakinsu. Ammi ta'kama baki tana salati "Abarsa yatafi' ihun data rapka kenan, ta'kara wata ihu tanacewa' Abude musu kofa sutafi, kuma kasani Zaid daga yau bani ba kai har abada mun rabu kenan, Daga yau ka kaddara bakada wata uwa a Duniya, Ni kai na daga rana itayau nacire nauyin kowa akaina nakoma tsohuwar Turai wacce bata ta6ayin aureba bare tasamu y'aya. Kasani daga yau ni Hajiya Turai Mafiya banida kowa aduniya sai dukiyata sun fiyemun daraja sau dubu.

Ya zuba mata ido cikeda mamakin maganganunta har tsaida takammala bayanan ta tas!, Shiko bai kara wata kalmarba haka ya rike hannun 'kanwarsa suka fice daga jirgin. Duk karfin zuciyarsa sanda yazub da kwalla awannan lokacin yana takaicin rayuwar duniya, atunaninsa ya'fi duk duniya rashin sa'a, shikuma jarabawarda Allah yai masa kenan.
Munah itama shiru tai suna tafiya jugum!!! tamkar tafiyar hawainiya.

       ***************************
Wani ne fiskarsa a duhu yake kwance gindin wata babbar bishiya ruwa na rapkawa shiko ya la6e anan jikinsa na karkaruwa sany'i ta'shigeshi sosai, gashi ko kayan kirki baisakaba sai dai mutane suta wucewa suna zoleshi ana masa dariya. Shi ba mahaukaci ba amma ana masa kallon mahaukaci.

Hakan yasa wannan mutumin yai shirin chanza gurin zama, yayinda yazo Haye hanya ce sausayi ta riskeshi mota ta bigeshi,jikinsa duk jina jina.

Miemah ce tafito daga wannan motan tana salati a tsorace, mutane sun cike wajen nan ta'ke, anata nanata mutuwa yayi, Allah yajikansa daman wannan mutumin anan wajen ya'saba kwana bashida kowa. Wannan irin maganganun da mutane suke akansa yasa Miemah ta'karaso domin taga'ne koshi waye, tana zuwa kuwa fiskar Zaid tagani.  "ZAID? Ta kwala ihu meyesa ake duk wannan maganganun akanka, kuma meyakawoka nan wajen?

Wata tsohuwa ce tabata amsa cewa" Baiwar Allah wannan saurayin sunansa Zayyad anan yake kwana anan yake tashi, Kuma naji ajikina kece Zaki taimaka masa,yana matukar bukatar taimakonki awannan lokaci.
            ✨✨✨✨✨✨✨✨

**** Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun wannan wani irin mafarkine Miemah tafarka ba shiri, sai had'a gumi take jikinta na karkaruwa tanakuma nanata salati aranta. Tun ranarda tahad'u da wannan bawan Allah Zayyad, batasan koshi wayeba Amma yanzu ba dama Tai barci ko yaushe sai tayi mahafarkinsa yana bukatar taimako daga gareta. Wannan mafarkin datai ayau yasa ta gaskanta sauran mafarke mafarkenda takeyi ako yaushe, Babu Shakka akwai wata 6oyeyyen sirri gamida Zayyad kuma ko a ina yake yana bu'katar taimakonta na gaggawa.

*****
Mutanen gida sun wuni cikin tsananin damuwa, y'an Sanda sai zirga zirga suketayi ko ina an kafa tsaro ana neman Zaid da Munah. Ma'inah ta kasa ci bare Sha ayanzu burinta kawai shine taganta tareda Zaid, rashinsa zai iya janyomata babbar matsala arayuwarta sabida babu wani namijinda take gani amasayin na miji face Masoyinta Kuma abar kaunarta Zaid. Su Mommy sai rarrashinta ake ayanzu sumanta biyu kenan, Nunfashi dakyar takeyi karshentama asibiti aka wuce da ita.

****
Cikin wannan tunanin Miemah talalu6o tatashi, damuwa da rud'ani ne sukayi Mata yawa awannan lokacin ga tunanin 6atan Zaid da Maimunatuh, gakuma tunanin halinda Ma'inanta ke ciki, uwa uba Kuma tunanin wannan bawan Allah Zayyad. Kasancewar tana barci alokacin da Ma'inah ta sume suka kaita asibiti babu kowa agidan, ita kad'ei akabari, tafito falo cikin tunani duk dacewa babu wanda tagani a gidan bata damu da tambayan ko ina sukajeba, samun waje tai tazauna a kujera tacigaba da sana'arta ta tunani.

"Ina bukatar taimakonki Baiwar Allah ke kad'ei ce zaki dawormin da Farin ciki a rayuwata, Banida kowa a duniya. 
Wannan maganar data doso kunnuwarta ne  yasa ta tashi bit!!! A tsorace tanacewa "Kai waye?

Zaid yayi matukar mamakin ganinta ahaka, ya rasa meke tsoratata daga tambayan Ina Mainah shikenan "Miemah lafiya dei? Abinda ya'kara fad'i kenan. Ita kuwa Miemah jitayi yace "Baiwar Allah ke kad'ei ce zaki dedeita tsakani na da zuri'ata, ki taimakamin. Cikin hawaye ta rufoshi da runguma, tana shafa fiskarsa "Bawan Allah ban sankaba Kuma ban ta6a saninkaba amma yazama dole nashare maka hawaye.

Ta6e Baki Zaid yayi "I think this girl is crazy" abunda yafad'a aransa kenan, a bayyane yace "Are you Alright? Yafad'a cikin  sassanyan murya inda ya'kara dacewa Ni nefa Zaid Muhammad Zabir yanzu muka ku6uce daga hannun Ammi, Miemah Baki gane nibane? Ya'kara tambayarta.

Kwarai da gaske na ganeka man, wallahi naganeka, Kuma bazan ta6a mance wannan kekkyawar fuskar ta'ka ba, alkawari nayo maka Insha Allah zaka dawo cikin y'an uwanka Zayyad Muhammad Zabir. 
   Jin wannan sunan daga ba'kin ta yasa Zaid saurin bankadota kasa, awannan lokacin fiskarsa cike takeda rud'ani bila adadin. Amma babu abunda yafad'a barin wajen yai nan ta'ke.

       **************************
Azaune take gindin bishiya tun zuwansu tana rusa kuka babu ci bare Sha. Shi dei Saminu ya Saba da wahala babu abinda ya'kara fad'amata ahaka tacigaba da kuka har saida akayi sallan Isha, Sanda tajira garin yai duhu sosai sannan tamike domin ta aikata abinda tai niya.
Daman ta shirya duk plans d'inta, da daddare zata kone gidan nasu da Saminu duka zata had'a takonesu kowa yahuta, ta gaji da rayuwa da mutumi matsiyaci babu arziki sai tsiyar banza.

Da saman rufin d'akin Saminu tafara konawa a Sannu asannu d'akin ta'kama da wuta bal_bal, gobara cikin gida abun tashin hankali,  ita kanta dakyar ta tsere, gidan ta kama da wuta sosai sai ci take tamkar gara Maisha koh tuni tashige daji aguje tana neman hany'a domin kada wani yaganta azargeta dawani laifi.

Labewa kusada wata katuwar bishiyan mangoro tai tana lekowa ko zataga anfito da gawan Saminu, saiko taji an ta6ota ta baya. Ihu tasaka awannan lokacin jikinta na karkaruwa dakyar ta bud'e idanunta tamkar a mafarki Saminu ne tseye agabanta da wuka ahannunsa.

    ****************************
Yana tuki cikin hawaye, ahaka yacigaba da share hawayensa har saida yakai ofishin mahaifinsa sannan ne yai ajiyar zuciya yakaraso ciki. La6ewa yai aba'kin kofa, har saida ya tabbar dacewa Baba nanan cikin ofishin Nan ne yasauke wata ajiyar zuciya a tsorace yai ciki. Yana shiga Baba yami'ke tseye cikeda farin cikin ganinsa "My Son, Zaid a Ina ka shiga? ka barmu cikin damuwa tun tuni nemanka muke.

Zayyad ya bud'e bakinsa a tsorace zai Masa bayani kenan Baba yarufoshi da runguma "Son I love you Soo much karka 'kara barinmu ahaka kaji D'ana.  Awannan lokacin Zayyad yarasa mezai Fadi jikinsa na karkaruwa yayinda ya gyad'a kai "Toh Baba Insha Allahu"

Yana kokarin barin wajen cikin dabara Amma babu hali, babban abinda ke tayar masa da hankali kuwa shine kada Zaid ya bayyana anan wajen aga'neshi.

"Ma'inah tana asibiti a dalilin 6atanka, kaga ya'kamata mutafi domin kaje kadubata Koh" cewar Baba. Ta6e baki Zayyad yai, ya zaro idanuwa a tsorace tareda had'iye myau "ko wacece Ma'inah? Yafad'a aransa, inda  ya'kara gyad'a kai a fisace yace" Toh Baba"

    ##########################

IYA ABUNDA YA SAWWAKA A YAU KENAN 🤗 KEEP ON FOLLOWING ❤️❤️❤️

ABUBUWA DA DAMA ZASU AWKU A SHAFI NA GABA, SO NO SPOILERS FOR YOU GUYS 😊😉😉 SHIYASA NA DAKATAR DA WANNAN SHAFIN AHAKA. SAURA KIRIS! MU KAMMALA TAGWAYE INA BUKATAR SHAWARWARIN KU. DA FATAN DEI KUNAJIN DAD'IN LITTAFIN.

NOTE
NO COMMENTS
NO UPDATE

ALLAH YAI MUKU ALBARKA😍 SAI MUN HAD'U A SHAFI NA TALATIN DA TAKWAS.

😍😍😍
🤩🤩🤩
😍😍😍
🤩🤩🤩

Tagwaye (Identical twins) On viuen les histories. Descobreix ara