PART 32

2.1K 132 13
                                    


   IDENTICAL TWINS BY BASMA BASHIR

                   👇👇ENJOY 👇👇

Karfe shida da rabi, adedei lokacin Sallar Maghriba jirginsu tai landing a babbar international airport ta Abuja wato Nnamdi Azikwe Airport. Daddy ne yafara fitowa sannan Saminu da Matarsa suka biye a baya, fiskokinsu duk ba kyaun gani musamman ma fiskar Saminu kwata kwata baiji dad'in bayyanar wannan sirrin ba, abinda ke kara tsotsa masa zuciya kuma shine tonuwar sirrin Maisha, ayanzu Yan sandan Maiduguri suna nan suna nemanta ruwa a jallo, shiko Saminu yasha alwashin cewa dazaran yana Raye babu abinda zai faru da y'arsa zaibi ko tawace hanya domin ya ceci yarsa ta ciki Maisha Saminu Maidugu.

Bismillah, Bismillah , Hi✋ Saminu lafiya meye kake tunani haka?  Sai yanzu yadawo cikin hayacinsa inda yaga ashe tun tuni anbude masa kofar mota, Daddy da Matarsa duk sunrigada sunzauna shi kad'ei ake jira. Dasauri yasa kafa yashige, shiru suke cikin Wannan motan babu wanda yai magana har Sanda suka kai gida saukesu Daddy yai shiko Kai tseye yanufi asibiti gun Matarsa daman ya matsu yadawo gunta sabida yana kewarta sosai ya kuma san duk yedda akayi ayanzu tana cikin kad'uwa da matukar ciwon zuciya domin wannan sirrin zata iya tsanadiyar rasa rayuwarta gaba d'aya sabida ta dad'e tana bautawa Y'ar da ba jininta ba, wacce Kuma tai tsanadiyar nisantarta da yayan cikinta "Innalillahi wa Inna ileihi rajiun'.

      ***************************
Dayake sunada d'aki a gidan Sambo, Kai tseye Saminu ya janyo Matarsa suka shige tamkar fad'a ya fisgo jakarda ke hannunta ya wullota kan gado da jajayen ido ya tsawatarmata" Aisha, Maisha yarki ce Kuma jininki amma meyesa kikebin bayan Dan uwana kuna zaginta, how dare you? Aisha wallahi idan kin kuskura nagano kinabin ba'yan Sambo da matarsa Aisha zan gujeki kuma karshen igiyar auren mu kenan sabida babu 6ata lokaci zan datse ta....

Toh sai me? Ta katseshi babu fargaba tace' Saminu ka sakeni mana wallahi ta ma'fi nono fari, sannan tun da wuri kasani bazan ta6a bin Bayan Mara Gaskiya ba, Maisha ta'yo halinka Saminu batada Hankali bare imani fad'amin me Zanyi da y'a irinta Allah wadaran halinku dakai da d'iyar taka ba'ki d'aya, Nidei har gobe banida wata y'a datawuce Miemah, Itace jinina, bazan ta6a kar6an Maisha amasayin Y'ata ba Allah sauwake yariny'ar datai niyar kashemu iyayeta kawai sabida tasamu damar cigaba dazama agidan Ya Sambo bayan bayyanar gaskiya...   Bata karasa wannan Furucin dake bakintaba yayinda Saminu yakai hannu fiskarta, alokaci d'aya yakai mata mari har guda Uku "Toh kisani wallahi zamana da ke ya'kusan karewa shasha kawai wacce batasan ciwon kanta ba.

Toh Sannu Wanda yasan ciwon kansa, nidei kamar yedda nafad'a ban fa'sa ba, Miemah itace Y'ata har abada, kaje kadauki d'iyar ta'ka kuje bangon duniya bata shafeniba wallahi.  Girgiza kansa yai yanabinta da kallo, ganinta yake tamkar mara hankali, Babu abinda ya'kara fad'i bud'e kofar d'akin yai Zuuuu!!! Yafitce a guje kamar wanda aka koro.

      ****************************
Innalillahi wa Inna ileihi rajiun' Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun'. Kalmar dake fitowa abakin Daddy kenan bayan jin abubuwan da Maisha ta aikatawa Matarsa a asibiti dakuma kudirinda tai niyar d'auka wato kudirin kisan y'ayansa Miemah da Maisha.

Tasowa yai cikin sananin damuwa ya rungume Hajiya Safeenah "A Gaskiya nima yanzu hakuri na ya'kare, Maisha ta turani bango she must pay for all her crimes Insha Allah, I'm sorry Safeenah ki yafemun tun tuni na'san Maisha tasan cewa mu ba asalin iyayenta bane sedei ita kanta batasan cewa na'san da hakanba, Nikuma don gudun 6acin ranki yasa nabarki cikin duhu ban sanarmiki da komai ba na'san kuma na aikata babban laifi don Allah ki gafartamin.    Dasauri momy ta'rike hannayensa "Mijina na yafemaka har abada sedei inason kafad'amin yaushe Maisha tasan da wannan maganar?

Tun lokacinda muke America tanada shekaru bakwai alokacinda muke shirin dawowa 'kasa Nigeria, kinsan Maisha da shiririta cikin jaka'ta tagano wannan takardar yarjejeniya damukayi tsakanina da D'an uwana dakuma Likita.......

Tagwaye (Identical twins) Where stories live. Discover now